Hotunan yadda masu zanga-zanga suka ƙwace iko da mamaye gidan shugaban ƙasa

Rashmi Kavindhya ta ce ba ta taɓa mafarkin za ta taka ƙafarta a cikin fadar shugaban ƙasar Sri Lanka da ke birnin Colombo ba.

Kwana ɗaya bayan da masu zanga-zanga suka kutsa cikin gini mafi tsaro a ƙasar, dubban mutane irin su Ms Kavindhya sun yi ta rububin ganin haɗaɗɗen gidan shugaban ƙasar.

Gida ne mai tsarin ginin Turawan mulkin mallaka da ke da baranda da yawa, da ɗakunan taro da kuma farfajiya, sannan akwai wujen ninƙaya da filin shaƙatawa.

Lamarin da ya faru ranar Asabar ya tursasa Shugaba Gotabaya Rajapaksa tserewa.

"Kalli haɗuwa da kyawun wajen nan," a cewar Ms Kavindhya wacce ta je wajen da ƴaƴanta huɗu.

"A ƙauye muke rayuwa kuma gidanmu ƙarami ne. Wannan fadar da al'umma ce kuma da kuɗin al'umma aka gina ta."

Dubban maza da mata da yara ne suka yi ta ƙoƙarin dannawa cikin gidan shugaban ƙasar, yayin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suke daidaita rububin.

Su kuwa ƴan sanda da dakarun tsaro na musamman sun yi cirko-cirko a wata ƴar kwana suna kallon ikon Allahn da ke faruwa.

A yayin da mutane ke ta zagaye daga wannan ɗaki zuwa wancan, kowannensu na ƙoƙarin ɗaukar hoto a gaban kayan ƙawa da zane-zanen da aka yi wa ɗakunan ado da su.

Ana iya ganin yadda aka yi watsi da fasassun gilasai da tukwanen furanni a cikin gidan, wanda hakan ke nuni ya irin yamutsin da aka samu lokacin da dubban mutane suka kutsa cikin harabar.

"Mafarkina ne ya tabbata na ganin fada irin wannan," a cewar AL Premawardene wanda ke aiki a wani wajen wasan yara a garin Ganeamulla.

"Ko yaushe muna layin sayen kananzir da gas da abinci, amma shugaban ƙasa da iyalansa na nan suna jin daɗinsu."

Masu jagorantar zanga-zangar sun ce ba za su bar fadar Shugaba Rajapaksa da Firaminista Ranil Wickremesinghe ba har sai sun sauka daga muƙamansu.

Duk da barazanar samun turereniya saboda irin yawan mutane da ke tururuwar shiga gidan, dakaru da sojoji masu ɗauke da makamai sun tsaya ne kawai suna kallonsu.

Sai wasu daga cikin masu zanga-zangar ne ke ƙoƙrin shawo kan maziyartan.

Wajen ninƙaya na zamanin shi ne abin da ya fi jan hankalin mutanen.

Iyalai sun tsattsaya a gabansa suna sha'awar ruwan ciki.

Mutane sun kaure da tafi da sowa a lokacin da wani matashi ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwan ninƙayar, inda aka naɗi bidiyon yadda mutane suka dinga shagalinsu a cikin a ranar Asabar.

"Na ji takaici," in ji Nirosha Sudarshini Hutchinson, wacce ta ziyarci fadar shugaban ƙsar tare da ƴaƴanta ƴan mata biyu.

"Kalli yadda mutumin da aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa ya ƙare cikin abin kunya. Yanzu mun yi da-na-sanin zaɓarsa. Mutane na son ya dawo d akuɗin ƙasar da ya sata."

An ga wani hoto da wasu matasa suka kwanta a kan gadon a cikin gidan shugaban ƙsar.

A cikin bidiyon da suka yaɗu kuma ana iya jiyo mutane na magana da harsunan ƙasar irin su Sinhala da Tamil, har da ma Turanci. Ana iya ganin farin ciki a tattare da su.

A wajen ginin kuwa, ɗaruruwan mutane ne ƴan addinin Buddha da Hindu da kuma Kiristoci ne suke ta karakaina a babban lambun da ke wajen, inda a baya kaɗan ba su isa ƙafarsu ta taka wajen ba.

Ƴan Sri Lankan na ganin zanga-zangar da suka shafe watanni suna yi ta yi nasarar hamɓarar da shugabannin ƙasar, waɗanda suka zarga da janyo taɓarɓarewar tattalin arzikinsu.

Sannan yanayin da suka ga shugabannin na rayuwa a ciki a fadarsu ya ƙara ƙona musu rayuka.