Matsalar tsaro ta zama ruwan dare a Najeriya - Makarfi

Babbar jam’iyyar hammaya ta PDP ta bayyana manyan matsalolin da ke janyo wa Nijeriya cikas ta fuskar ci gaban ƙasa, da bunƙasar tattalin arziki da inganta tsaro.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Ahmed Muhammad Makarfi ya ce idan aka sake bai wa jam’iyyarsa ta PDP dama a zaɓen 2023, za su kyautata al’amura.

Makarfi ya shaida wa BBC cewa da wuya rayuwar al'umma ta inganta idan kusan komai da take amfani da shi daga kasashen waje ake shigowa dasu

 “Ka ga dai duk wata kasa da za ta dogara a kan cewa kusan komai za ta shigo ne da shi tana cikin wahala, kuma kusan yadda muke kenan a Najeriya.

Ya kamata a ce gwamnati ta shimfida abubuwa a kasa da za su habaka tare da sarrafa abubuwa daban daban da na ci, da na amfani da su, har ma a rinka fitar da wasu.”

“Haka ne zai sa darajar kudin kasar watau naira ta yi karfi, idan kuma ta yi karfi to ka ga wannan ba karamin al'amari ba ne, saboda zai kawo ci gaba a tattalin arziki kasa,” in ji shi.

Noma da harkar kasuwanci da zumunci sun gagara

A cewar tsohon gwamnan, lamuran sun kara yin muni ne saboda matsalar tsaro.

Ya ce a lokacin da jam'iyyarsu ke mulki a 2015 matsalar ta fi kamari ne a yankin Arewa maso Gabashin kasar, amma ya yi ikirarin cewa sun fara daukar matakin shawo kan matsalar saboda har an gudanar da zabe a yankin.

Amma ya nuna shaku a kan ko hakan zai yiwu a wasu yankunan kasar a zaben 2023.

 “Kalli yanzu yadda yankin Arewa maso Yammaci ya koma, haka al'amarin yake a yankin Arewa ta Tsakiya, haka idan ka je kudu. A Najeriya noma ma yana gagara, kasuwanci yana gagara, zumunci yana gagara kusan abubuwa da dama suna gagara,” in ji Ahmed Makarfi.

Jam'iyyar PDP dai ta ce idan 'yan Najeriya suka sake ba ta dama za ta gudanar da shugabanci mai karfi wanda a cewarta shi ne zai shawo kan matsalar.

Sai dai wasu na ganin cewa jam'iyya mai mulki a yanzu ta gaji matsalar ne daga babbar abokiyar hammayata.

"Abin da aka gada shi ne rikicin Boko Harama a yankin Arewa maso Gabashi ko shi kafin gwamnatin PDP ta ba da mulki an fara shawo kan shi, shi ya sa ma aka yi zabe a ko'ina a yankin Arewa maso Gabashin.

"Ba a ce an kasa zabe saboda rashin tsaro ba, amma yanzu har a kaduna ma ana ikirari a wani wajen cewa ka da zo a yi kamfe na siyasa, balantana maganar zabe wanda wani abu ne da bai taba faruwa a baya ba.

''In an gaji abin da yake North East, za ka gaji abu ne don ka yi maganinsa, amma maimakon maganin sai matsalar ta koma ruwan dare,'' in ji tsohon gwamnan na Kaduna. 

Mafita

A cewar Makarfi shugabanci na gari ne zai sa a iya shawo kan matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban kasar.

“Wannan ya ta'allaka ne kan shugabanci saboda ana bada kudade don wannan yanayi, ya ake ba da kudaden kuma in ka ba mutum mukami idan ya yi aikinsa yadda ya kamata sai ka saka masa da alheri, in ya kasa to kai ne shugaba, ka san abinda ya kamata ka yi cikin gaggawa,” a cewarsa.