Sauyin Yanayi : 'Duniya na cikin bala'i' -MDD

An bude taron kolin sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Masar tare da gargadin cewa duniyarmu tana "aikewa da sakon damuwa".
Sakatare Janar Antonio Guterres na mayar da martani ne ga rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a ranar Lahadi yana mai cewa shekaru takwas da suka gabata sun kasance mafi zafi a tarihi.
Shugabannin kasashen duniya fiye da 120 ne za su isa wurin taron da aka fi sani da COP27, a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh a tekun Bahar Maliya.
Za a fara tattaunawa ta tsawon makonni biyu ne a tsakanin kasashen kan batun sauyin yanayi.
Shugaban taron kolin na COP27, Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry, ya yi kira ga shugabannin da kada su bari rikicin abinci da makamashi da ke da alaka da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ya kawo cikas ga daukar matakan shawo kan kan sauyin yanayi.
"Ya zama wajibi a kanmu baki daya a birnin Sharm el-Sheikh, mu nuna amincewa da irin girman kalubalen da muke fuskanta da kuma tsayin dakanmu na shawo kan lamarin."
An bayyana bukatar daukar matakin ne a sabon rahoton da hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.
Mista Guterres ya aike da sakon bidiyo ga taron inda ya kira rahoton da aka fitar a kan yanayi na duniya na shekarar 2022 a matsayin " halin da duniya ta cike ta fuskar sauyin yanayi".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin rahoton, masana kimiyya sun kiyasta cewa a halin yanzu yanayin zafi a duniya ya karu da 1.15C tun kafin kafuwar masana'antu kuma sun ce shekaru takwas na baya-bayan nan suna kan hanyar da za ta kasance mafi zafi a tarihi.
Rahoton ya kuma yi gargadi game da sauran tasirin sauyin yanayi, da suka hada da karuwar yawan ruwan teku a cikin sauri, da karuwa a yawan yawan kankara da ke narkewa da kuma matsanancin zafin da ba a taba ganin irinsa ba.
Mista Guterres ya ce bisa la’akari da wadannan binciken, dole ne taron kolin na COP27 ya zama wurin daukar matakan gaggawa kuma sahihanci.
A ranar Litinin din nan ne za a fara taron kolin COP27 gadan- gadan tare da babban taron shugabannin kasashen duniya, inda shugabannin kasashe da na gwamnatoci za su gabatar da jawabai na mintuna biyar don bayyana abin da suke so daga taron.
Ana sa ran Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak zai bukaci shugabannin duniya da su yi kara " hanzari" wajen soma amfani da makamashin da baya gurabata muhali.
Zai kuma fadawa wa shugabannin da kada su "ja baya" kan alkawuran da aka yi a taron COP26 na bara a Glasgow.
Shugabannin kasashen duniya za su yi magana a ranakun Litinin da Talata, kuma da zarar sun tafi, wakilan kasashen duniya za su ci gaba da tattaunawa don cimm matsaya . An samu kasashen duniya da suka yi alkaura a taron kolin bara.
Kasashe masu tasowa - wadanda su ne matsalar sauyin yanayi ta fi yiwa illa - suna bukatar a kiyaye alkawuran da aka yi a baya na samar da kudade.
Shin ko kasashe na kan hanyar cimma muradun sauyin yanayi na Glasgow?
Su wanene shugabanni da kuma wadanda ke kawo cikas ga shirin?
Amma kuma suna son a tattaunawa kan "asara da barna " da kuma kudi - don taimaka musu jimre da asarar da suka samu sanadin sauyin yanayi maimakon kawai a taimaka mu su akan yadda za su tunkari matsakar nan gaba.

Kazalika bayan tattaunawar da za a yi akwai kuma daruruwan taruka da za su gudana a cikin makonni biyu da suka hada da na baje koli da na tarurrukan bita da wasanin al'adu daga matasa da sauransu.
Zanga-zangar nuna adawa da matsalar sauyin yanayi da aka aba gani a kowani taron koli wataƙila ba za a yi shi ba a wannan karon.
Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2014, a karkashin jagorancinsa ne aka rika murkushe masu adawa da gwamnatimsa.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi kiyasin cewa kasar na da fursunonin siyasa kusan 60,000, kuma da dama daga ciki ana tsare da su ba tare da shari’a ba.
Mista Shoukry ya ce za a kebe fili a birnin Sharm el-Sheikh domin gudanar da zanga-zangar.
Sai dai masu fafutuka na Masar sun shaida wa BBC cewa kungiyoyin cikin gida da dama sun kasa yin rajistar halartar taron.











