Yadda mutane suka shiryawa tunkarar yanayin hunturu da ke tafe

Hazo

Asalin hoton, OTHER

A daidai lokacin da yanayi ke ci gaba da sauyawa zuwa sanyi da ƙaruwar bugawar iska, mazauna arewacin Najeriya da kudancin Nijar na ci gaba da shiryawa tunkarar yanayin.

Tuni wasu mazauna birnin Kano da ke arewacin Najeriya suka shaida wa BBC irin tanadin da suka yi wa sanyin.

Wasu sun ce sun tanadi kayan sanyi su da iyalansu, yayin da wasu kuma suka ce sun tanadi man shafawa wanda bai zai rinka sanya fatar jikinsu na bushewa ba.

Sauyin yanayi irin wannan kan zo da wasu larurorin lafiya ko ta da waɗanda suke kwance, abin da ya sa masana ke shawartar jama’a su yi hattara.

Dakta Mukhtar Ahmad Gadanya, na sashen kula da lafiyar al’umma a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce ana bukatar mutane su kiyaye a irin lokaci na sanyi da jin rauni, sannan kuma a guji ajiye ruwan zafi a inda zai cutar da yara ko ma manya.

Ya ce ” Ga masu lalurar asthma, to su tabbatar a koda-yaushe suna tare da magungunan da suke amfani da su, sannan kuma a rinka tabbatar da ana shan ruwa sosai, da kuma shan abu mai dumi da ma cin abubuwan da zasu kara lafiya.”

Dakta Gadanya, ya ce a lokacin sanyi yakamata a rinka ba wa yara da tsofaffi kulawa ta musamman, saboda sanyi yafi illa garesu.

Hukumar kula da yanayin sararin samaniya a Najeriya dai ta yi hasashen samun ƙarin hazo, yayin da ƙura ke tasowa daga gabas.

Kazalika an shawarci mutane da su kiyaye da kai wuta daki saboda suji dumi, haka suma direbobin motoci an shawarce su da su rinka kula da iskar tayar motocinsu saboda za a rinka samun zafi wani lokaci kuma sanyi.