Hunturu: Abin da ya sa taɓin hankali yake tashi a kokacin Sanyi

Wani mai fama da larurar taɓin hankali

Asalin hoton, Getty Images

Lalurar taɓin hankali cuta ce da mutane da dama suka santa, walau dai kana da wani ɗan uwa, ko wani da ka sani da ke fama da ita.

A wasu lokutan ana iya killace waɗanda ke fama da larurar a gida ko cibiyoyin kula da masu taɓin hankali na gwamnati, yayin da wasu lokutan kuma masu irin wannan cuta ke bazama su yi gararamba a gari ba tare da an san yan uwansu, ko daga ina suke ba.

Wani abu da mutane da dama suka sani shi ne cutar na ƙara ƙamari a lokacin sanyi, sannan yawan masu taɓin hankali da ake gani a kasuwanni da tashoshi musamman a Najeriya na ƙaruwa a wannan lokaci. Shin kun san abin da ke kawo hakan?

Dalilin kenan da ya sa muka tuntuɓi Dakta Auwal Fatuhu Abubakar, na asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano.

Mecece alaƙar dake tsakanin sanyi da lafiyar ƙwaƙalwa?

"Babu wata cikakkiyar alaƙa da za a ce ga ta musamman, kawai dai wasu abubuwa ne aka kula a wasu a cikin nau'ukan ƙwaƙwalwa suka fi tashi ba kowanne ba," in ji shi.

Ya ƙara da cewa abin da ya sa aka fi ganin haka shi ne yawancin waɗannan nau'ukan na ciwon ƙwaƙwalwa na da yawa a cikin al'umma to shi ya sa tun da suna da yawa a cikin al'umma sai aga kamar ƙaruwa ya yi, sai mutane su kula cewa ana samun ƙaruwar mutanen da ke samun wannan matsala.

Dakta Auwal Fatuhu Abubakar ya ce: "Idan baya zuwa asibiti, to ya kamata ya ziyarci likita, idan kuma aka ga alamun ciwon zai tashi sai a yi sauri a mayar da shi asibiti domin a mayar da shi kan magungunan da yake sha."

Alamun da za a iya gane ciwon mai taɓin hankali na neman tashi.

  • Rashin samun bacci ko baccin zai ragu
  • Karuwar kasala da rashin jin kwarin jikin mutum zai karu
  • Damuwa da ɓacin rai za su ƙaru
  • Yawan fushi na ƙaruwa
  • Za a ga mutum yana janye kansa daga cikin jama'a sannu a hankali
  • Zai riƙa tunani iri-iri, ciki har da na son kashe kai
  • Zai riƙa jiye-jiye da gane-ganen abubuwan da ba kowa ne ke ganinsu ba.

Wani taimako za a iya yiwa mutum kafin kai shi asibiti?

A cewar Dakta Auwal Fatuhu Abubakar idan aka kula canji ya soma faruwa ga halayyar mutum to idan yana da magunguna ya kamata ya fara amfani da su.

Sannan ya kamata ya kiyaye, ko ƴan uwansa su kiyaye masa ka'idojin da likita ya gindaya masa.

"Ya danganta da tsananin ciwon, wani za ka ga na dan lokaci kankani ne, wasu kuwa sai an dan kwana biyu ana shan magani sai ka ga ya warke," in ji Dakta.