Dan fim Mohamed Al-Siyari a Tunisia na shan caccaka kan neman sauya lokacin azumi zuwa hunturu

محمد السياري، ممثل تونسي

Asalin hoton, SHEMS FM

Lokacin karatu: Minti 3

Wani fitaccen dan fim a Tunisia Mohamed Al-Siyari ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a Gabas Ta Tsakiya bayan ya yi kiran a dawo da yin azumi lokain hunturu duk shekara.

Ya yi wannan tsokacin ne a wata tashar rediyo ta Shams FM a Tunisia a ranar Juma'a.

A tattaunawar, ya ce ya kamata "Ramadan a mayar da shi watan Disamba duk shekara, saboda azumi lokacin bazara akwai wahala," yana kuma mai cewa "mayar da yin azumi lokacin hunturu zai ƙarfafa wa mutane yin azumi. "

Ya jaddada ra'ayinsa da cewa "addini mai sauƙi ne ba wahala ba" tare da yin tambayar cewa: "Me ya sa wai muke azumi cikin tsananin zafi?"

Ramadan wata ne na tara a kalandar Islama, kuma wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Amma al-Siyari ya ce ya kamata malaman addini su haɗu su sauya lokacin azumi ya zama kamar lokaci guda da ake Kirsimeti a ƙarshen shekara.

Kauce wa YouTube, 1
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 1

Kalamansa sun haifar da caccaka da zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta musamman a Tunisia da sauran ƙasashen Gabas Ta Tsakiya.

Ya kuma sake fitowa a wata tashar Rediyo ta "Mosaic FM" yana kare kalamansa cewa yana da ƴancin ya bayyana ra'ayinsa tare da ƙin amincewa ya fito ya janye kalamansa da kuma neman afuwar Musulmi kan abin da ya faɗa.

Kauce wa YouTube, 2
Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a YouTube, 2

Yawancin waɗanda suka yi tsokaci a kafafen sada zumunta sun caccaki kalaman Al-Sayyari ne, wasunsu sun ce rashin ilimin addini ne ya sa har ɗan fim din ya furta kalaman.

@fbati91 cewa ya yi "ɗan fim na Tunisia Mohamed Al-Siyari kamar ya mayar da addini abin wasa. Jahilci bala'i ne "

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Haka ma @saberlarbi ya caccaki Muhammad Al-Siyari kan kiran da ya yi na a dawo yin azumi zuwa watan Disamba.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wasu daga cikin masu caccakarsa sun ce ya yi kalaman ne kawai "don ya ja hankali don farfaɗo da sunansa saboda rashin aikin yi, kamar yadda Samir Elwafi ya bayyana.

منشور لسامر الوافي على فيسبوك

Asalin hoton, Facebook

A tsokacinsa Ali Guesmi ya ce "Mohamed al-Siyariya ya fahimci addini amma abin da ya kasa fahimta shi ne yanayi.

منشور لعلي غويسمي على فيسبوك

Asalin hoton, Facebook

A ɗaya ɓangaren kuma wasu sun bayyana rashin jin daɗi kan yadda "ake suka da caccakar Al Siyari kan kalamansa, da kuma rashin tattaunawa ta fahimta da mutuntawa a tattaunawar.

Akram Al Zribi a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook ya nuna cewa ya kamata a yi bincike game da batun ta hanyar hujjoji daga ayoyin Qur'ani, ba wai suka ba da jifar kalamai na zagi da nuna wani ya yi ɓatanci ba.

منشور لأكرم الزريبي على فيسبوك

Asalin hoton, Facebook

Al-Siyari ɗan wasan fim ne wanda ya sha fitowa a fina-finan Larabawa musamman masu dogon zango.