Birnin da babu sana'ar da aka fi samun kudi kamar sayar da akwatun gawa

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yi wa sojoji jana'izar ban girma - ba kamar sauran mutane ba

A baya birnin Bamenda na kasar Kamaru ya shahara wajen harkokin kasuwanci amma a yanzu rikicin da aka kwashe shekara biyar ana yi tsakanin bangaren da ke magana da turancin Ingilishi da ke son ballewa daga kasar da kuma bangaren da ke magana da turancin Faransa ya jefa birnin cikin mawuyacin hali.

Birnin Bamenda ya mutu. Sana'ar sayar da akwatun gawa ce kawai take garawa a birnin. Ana zubar da gawarwaki a-kai-a-kai a fadin birnin - a mutuware da kan tituna da cikin koguna.

Ma'aikatan da ke kula da birnin ne suke kwashe gawarwakin sannan su binne su.

"Abin alfahari ne a binne mutum idan ya mutu, musamman ma idan iyalai da 'yan uwansa ne suka yi masa suttura," a cewar wani mutum da ke aiki a makabarta a yayin da ya je karbar akwatunan gawa 10 masu saukin kudi daga wurin sayar da su.

An rage bukatar sayen akwatunan gawa na-gani-na-fada - wadanda ake sassakawa a yi musu siffar littafin baibil, ko mota ko kuma kwalabar giya, domin nuna salon rayuwar mutumin da ya mutu.

"Yanzu ba kowa ne yake iya sayen akwatun gawa na CFA miliyan daya ba [kusan $1,500 ]. Akasarin mutane ba sa iya sayen akwatun gawar da ya wuce CFA 50,000," a cewar wani da ya je wurin sayar da akwatun gawa.

Ana yawaita yin jana'izar matasa da kananan yara abin da ke tunawa mutane irin rikicin da ke faruwa a yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yammacin kasar Kamaru da ke magana da turancin Ingilishi.

A cikin shekaru biyar, rikicin ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane, yayin da ya tilasta wa fiye da mutum miliyan daya tserewa zuwa yankina da ake magana da turancin Faransa, kana kusan mutum 80,000 suke gudun hijira zuwa Najeriya.

Wannan matar ta ce 'yan sanda sun kashe danta

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Wannan matar ta ce 'yan sanda sun kashe danta

Yakin ya samo asali ne daga rashin jituwar da aka rika samu tun bayan kawo karshen mulkin mallaka, yayin da aka hade yankin da Birtaniya ta yi wa mulki da yankin da Faransa ta mulka aka kirkiro kasar da a yanzu ake kira Kamaru.

Tun daga wancan lokaci mutanen da ke yankunan da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka suke zargin cewa an tauye hakkinsu kuma suna bijire wa abin da suka kira yunkurin gwamnati - wadda masu magana da Faransa suka mamaye - na tilasta musu barin tsarin rayuwarsu, ciki har da daina amfani da harshensu da tarihinsu da tsarin ilimi da na shari'arsu.

A shekarar 2016 ne aka soma tayar da jijiyoyin wuya a Bamenda da sauran yankuna da ke magana da turancin Ingilishi yayin da wasu mutane suka bijire wa yin amfani da Faransanci a makarantu da kotunansu, da kuma gazawar gwamnati wajen wallafa takardu da turancin Ingilishi, duk da yake shi ne harshen da hukumomi suka amince a rika aiki da shi.

Kasancewar gwamnati ta umarci hukumomin tsaro su murƙushe masu zanga-zanga a maimakon zama da su domin warware matsalolinsu, sai matasa maza suka ɗauki makamai domin neman a bai wa yankin Ambazonia ƴanci, kamar yadda suke kiran yankunan biyu masu amfani da turancin Ingilishi.

A yanzu, motocin sojoji suna rangadi a-kai-a-kai a yankin Bamenda. Mazauna yankin sun ce sojoji na samame a gidaje tare da kama wasu da cinnawa kasuwanni wuta sannan suna kuma suna yasar da gawarwakin mutane har da kwamandojin mayaƙa domin gargaɗin mutane kan shiga irin ƙungiyoyin.

Dakarun gwamnati sun tafka asara sakamakon yaƙin inda duk ranar Alhamis da Juma'a ake kwaso gawarwakin sojoji daga ɗakin ajiyar gawa da ke Yaounde, babban birnin ƙasar. Matan da mazajensu suka mutu na koke-koke gaban jerin akwatunan gawar da aka yi wa kwalliya da tutocin ƙasar Kamaru kafin a binne sojojin.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farar hula sun fi jin jiki a lokacin yaƙi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan aware sun yi ƙaurin suna a ta'asar da suke tafkawa kan farar hula har da fille kai da azabtar da mata da suka ayyana a matsayin waɗanda suka yaudaresu kan fafutukarsu,".

Suna yaɗa bidiyon ɓarnar da suka tafka domin gargaɗin mutane kan irin hukuncin da za su fuskanta idan aka zarge su da haɗa baki da sojoji.

A ranakun Litinin, Birnin Bamenda na zama kufai - tituna fayau kuma kasuwanni a rufe. A ƴan kwanakin nan, ƴan garin da suka take dokar hana fita na fuskantar harbi ko ma a cinnawa shagunansu wuta.

Sojoji da ƴan sanda sun ƙaurace don gujewa hari daga mayaƙan da ke da ƙarfi a birnin. Mayaƙan sun kuma ba da umarnn a rufe dukkanin makarantu shekara huɗu da suka gabata a wani ɓangare na boren da suke.

Wasu makarantun sun kasance a buɗe amma ko kusa ɗaliban ba sa kayan makaranta. Sojoji sun ƙaƙaba dokar hana fita cikin dare a birnin abin da ya sa kasuwa a galibin wuraren cin abinci da wuraren shaƙatawa da gidajen rawa ta mutu, babu wadatacciyar wutar lantarki."

Yawan harbe-harbe ya sa mutane sun ƙaurace," a cewar wata mai jiran kanti. Ta kuma ce hakan ya hana mutanen da ke zaune a ƙasar waje komawa gida. Wadanda ke zaune a ƙasashen waje ne zuciyar tattalin arzikin Bamenda , suna tura kuɗi domin zuba jari a harkar gine-gine sannan su koma gida lokacin kirsimeti su amfana da guminsu.

Amma hukumomi na zarginsu da ɗaukar nauyin ƴan awaren. Wasu da suka koma gida sun tsinci kansu a hannun hukumomi, wasu kuma na gidan gyaran hali na Younde da Douala - yayin da wasu kuma suka yi ɓatan dabo.

Kuɗaɗen da ƴan ƙasar da ke ƙasashen waje ke turowa ya yi ƙasa, a yanzu kuma sun daina zuwa. Wani daɗɗen mazaunin Peter Shang ya ce a yanzu mutane suna ɗaukan kwana ɗai-ɗai ne: "Rayuwa ba ta da tabbas. Akwai abubuwa da dama da ke tuna maka da mutuwa. Za ka hadu da mutum yau amma zuwa gobe rai ya yi halinsa."

Ga Marie Clair Bisu, a yanzu tana samun damar ganin mijinta saosai saboda yana komawa gida kafin dokar hana fita ta fara aiki." Ya gano ƴaƴansa. Ya kasance mutumin da ba ya komawa gida da wuri, wani zubin ya dawo a make da giya, ya kuma je kai tsaye ya kwanta. A yanzu zai iya wasa da yaransa ya kuma duba litattafansu. Rikicin ya sake haɗa kawunansu," a cewarta. Matsalar da muke fuskanta ita ce harbe-harben bindiga na hana mu bacci."

.
Bayanan hoto, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma ne yankunan Kamaru da ke Turanci

Kuma bayan shafe dare ana luguden wuta, sai mazauna sun yi ta kiraye-kiraye sannan su tabbatar da yanayin kafin su fita waje.

Duk da haka, harbin bindiga ya zama ruwan dare a Bamenda ta yadda mutane sun daina firgitar neman tsira idan suka ji harbin.

"Me za mu ci idan muka ci gaba da tserewa? Dole na ciyar da ƴaƴana," in ji wata mai sayar da kayan lambu. "Kawai muna neman mafaka ne sannan mu koma harkokinmu na kasuwanci idan aka tsagaita harbe-harben.

"Wata matar ta ce ƴarta ta saba da jin ƙarar har ma ta san suwa ke harbin. "Shekarar yarinyata 7 kuma tana iya faɗin irin bindigar da aka yi amfani da ita wajen harbin - ko ta sojoji ko kuma ta mayaƙan," kamar yadda ta faɗa.

Wasu mata masu sadaukar da kansu ga addini da na haɗu da su kan titi sun ce suna jiran tasi ne domin zuwa gidan marayu na Abangoh. Yaƙin ya ƙara yawan ƴan mata masu juna biyu ganin yadda ƴan matan da suke ƙauracewa gidajensu ke fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata daga duka ɓangarorin biyu. Ɗaya daga cikinsu cikin fushi ta ce "yin amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi abin ƙyama ne."

Akwai shaidun da ke nuna cewa birnin da a baya yake ƙyalli a yanzu ya shiga ruɗu sakamakon yaƙin da mutane da dama ke ganin bai zama dole ba.

.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Turawan mulkin mallaka ne suka tsara iyakokin ƙasashen Afirka
  • Jamus ta yi wa yankin mulkin mallaka a 1884
  • Sojojin Burtaniya da Faransa sun tilasta wa dakarun Jamus ficewa a 1916
  • Shekara uku bayan nan aka raba Kamaru - kashi 80 cikin 100 ga Faransa, kashi 20 kuma ga Burtaniya
  • Yankin da ke amfani da Faransanci na Kamaru ya samu ƴancin kai a 1960
  • Bayan zaɓen raba gardama ne ƴan Kudancin Kamaru suka ɗinke da Kamaru yayin da ƴan arewacin Kamaru kuma suka ɗinke da Najeriya.