Dalilin da ya sa 'yansiyasar Ghana suka kasa kawo ƙarshen matsalar Galamsey

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Haruna Shehu Tangaza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kumasi Ghana
- Lokacin karatu: Minti 4
Karuwar ayukkan haƙar zinare ba bisa ka'Ida ba zai kasance babban ƙalubale ga duk wanda zai zama shugaban ƙasar Ghana na gaba, yayin da masu kaɗa ƙuri'a ke shirin fita rumfunan zaɓe ranar Asabar.
Tun gabanin zaɓen, lamarin ya zama wani batu mai santsi da kowane ɗantakara ke kaffa-kaffa da shi wajen yakin neman zaɓe, duk da cewa yakan jawo gurɓata ruwan koguna da lalata gonaki - musamman na Cocoa - da kuma yin illa ga lafiyar mutane.
Galibin talakawan ƙasar dai na son a kawo ƙarshen wannan fasa-ƙwauri da ake kira "galamsey", amma 'yan siyasa sun sha yin alkawarin hakan ba tare da cikawa.
Wannan ta sa ake zargin manyan masu samar wa jam'iyyun siyasa kudade na amfana da harkar.
Harkar ta Galamsey ba baƙuwa ba ce a nan Ghana, amma ta yi ƙaruwar da ba a saba gani ba saboda tashin farashin ma'adanin zinare a duniya.
Sai dai yawancin zinarin da ake haƙowa, ana fita da shi ne ta ɓarauniyar hanya, abin da ya sa kasar ba ta cin moriyar fitar da wannan dutsen mai daraja a hukumance.
'Dalilin da ya sa na shiga galamsey'

A gefe guda kuma, harkar na samar da ayyukan yi masu tsoka ga ɗimbin mutane, da samar da maƙudan kuɗaɗe ga manyan mutane.
Abdulhamid Yahaya na ɗaya daga cikin mutanen da suka amfana da harkar ta galamsey, kodayake ya ce yanzu ya daina bayan shekara uku a cikinta.
"Ba aikin yi ne," in ji shi. "Dalilin da ya sa kenan na shiga aikin saboda mu rufa wa kai asiri. Ana ɗan samun kuɗi."
Ko me ya sa Abdulhamid ya daina haƙar ma'adanan?
"Daga baya wani rikici aka yi a wurin har ma aka kashe mutane, shi ya sa na bar aikin kuma na koma gida. Yanzu na daina aikin," kamar yadda ya shaida min.
Sinadarai masu haɗari
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu wannan sana'ar kan yi amfani da wasu sinadarai masu haɗari ga rayuwar ɗan'adam wajen raba zinaren daga ƙasa, sannan su zubar da dagwalon cikin gulabe da koguna.
Wannan hanyar ta wanke ma'adani kan gurɓata ruwa da haddasa cutuka, in ji Hizbullah Mohammad Salisu - wani wanda ya san yadda ake gudanar da harkar.
"Lahanin yana da yawa sosai, saboda sinadarin da suke amfani da shi ba shi da kyau. Yakan sa a haifi yara ba hannu ko ƙafa ko ma babu ido," a cewarsa.
"Wani lokacin idan ka buɗe famfo sai ka ga ruwan ya zama ja, ko ka ga ƙwari sun mutu a ciki. Kowace gwamnati ta zo sai ta yi alƙawarin cewa za a daina."
Wata matsalar kuma ita ce yadda masu haƙar zinaren ta ɓarauniyar hanya ke kutsa kai cikin gonaki musamman na cocoa suna haka ramukan hakar zinaren.
Hizbullah ya ce hakan ya bayar da gudunmuwa wajen raguwar ma'adanin cocoa da ƙasar ke fitarwa matuƙa da kuma tashin farashin kayan abinci.
"A da Ghana ce ta ɗaya wajen fitar da cocoa ƙasashen waje amma yanzu ba mu ciki saboda masu galamsey sun yayyanke cocoan."
A watan Agusta kamfanin samar da ruwa na Ghana ya yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙarancin ruwan sha a wasu sassan kasar saboda aikace-aikacen yan galamsey.
Gargaɗin ya zaburar da wasu masu fafutika, inda suka shiga zanga-zangar neman a kawo karshen fasa-ƙwaurin kuma suka sa ya zama babban batu a yaƙin neman zaɓen da za a yi ranar Asabar.
Manyan 'yan takarar shugabancin kasar biyu wato Mahmudu Bawumia na jam'iyya mai mulki ta NPP da kuma na babbar jam'iyyar adawa ta NDC John Dramani Mahama duk sun sha alwashin kawo karshen safarar ta Galamsey.
Amma yawancin'yan Ghana na ganin yana da wuya yanzu a samu shugaban kasar da zai yi kasadar kawo ƙarshen galamsey saboda yadda ake zargin masu ido da kwalli na kasar - ciki har da manyan 'yansiyasa da sarakuna - na da hannu dumu-dumu a cikinta.
Masu sharhi kan al'amura dai na ganin mafita kawai ga sabuwar gwamnatin ita ce jawo masu wannan harkar a jiki domin nuna musu yadda za su yi aikin bisa ƙa'ida, da bin matakan kariya ga rayukan mutane da muhallansu, da saka ta cikin tsarin samun kuɗaɗen shiga na hukuma.











