Ambaliya ta kashe mutum 195 a Najeriya - NEMA

FLOODS

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 195 a jihohi 15 na ƙasar a shekarar 2024.

Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta raba ƙarin wasu fiye da mutum 208,000 da muhallansu a cikin jihohi 28.

A cikin rahoton da ta fitar kan ƙididdigar ɓarnar da ambaliya ta yi a Najeriya a cikin 2024, NEMA ta ce fiye da kadada 107,000 da gidaje 80,000 ne ambaliyar ta lalata a bana.

Babbar daraktar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta shaida wa BBC cewa: ‘‘Hasashen yanayi da muka samu daga cibiyar aikin gaggawa da muka kafa a cikin watan Yuli, ya nuna cewa ƙananan hukumomi 140 wannan ambaliya ta shafa, a cikin jihohi 28’’

‘‘Sannan mutum 548,494 ne ambaliyar ta shafa, kuma a cikinsu aƙalla mutum 2,000 ne suka ji rauni sakamakon ambaliyar’’

Hajiya Zubaida Umar ta ƙara da cewa jihohin da ambaliyar ta fi shafa sun haɗa da Bauchi da Zamfara da Sokoto da kuma Jigawa.

‘‘Jihar Bauchi ce ta ɗaya, amma a Jigawa aka fi samun asarar rayuka, amma a Bauchi da Zamfara ne aka fi tafka asarar da ta shafi sauran abubuwa’’

Ko waɗanne matakai hukumomi ke ɗauka a kai?

NEMA ta ce dama tun kafin faruwar ambaliyar, ta buƙaci jihohi su ware wasu wurare da za a iya tsugunar da mutane idan an samu ambaliyar, kamar yadda aka yi hasashe tun da farko.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

‘‘To jihohi da yawa sun yi wannan, wasu sun yi amfani da makarantu, wasu kuma har a cikin sansanin ƴan gudun hijira. Mu kuma namu (NEMA) mun je muna ƙoƙarin samo masu kula da lafiya da masu gyara ruwan da ya gurɓace da dai sauransu, yadda za mu san ta yaya za mu kai masu tallafi’’ inji Hajiya Zubaida Umar.

Hukumar bayar da agajin gaggawan ta Najeriya ta ce ambaliyar ta bana ta zarce wadda aka saba gani a baya saboda yawan ruwan saman da ake samu a bana, ga kuma gine-gine da ake yi a kan hanyoyin ruwa, ga shara da ba a kwashewa

Hukumomin a Najeriya sun ce tun daga lokacin da suka samu hasashe daga ƙwararru cewa za a samu ambaliyar suka fara aikin wayar da kan jama’a a kai, tare kuma da faɗakar da hukumomin da lamarin ya shafa, musamman a matakin jihohi domin ganin sun ɗauki matakan da suka dace.

Amma duk da irin wannan mataki na gargadi da wayar da kan jama’a, da dama ba su aiwatar da tsare-tsaren da suka dace ba har sai da ambaliyar ta faru.