Wane ne Pavel Dúrov mai dandalin Telegram?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Tun dai lokacin da ƙasar Faransa ta kama tare da tuhumar Pavel Dúrov, wanda attajirin ɗan kasuwa ne ɗan kasar Rasha, kuma mamallakin dandalin Telegram sunansa ya ci gaba da amo musamman a kafofin sadarwa, inda jama'a ke son sanin ko shi wane ne.

Faransa na zarginsa ne da rashin yin ƙoƙari wajen dakatar da ayyukan laifuffuka a dandalin nasa na Telegram, zargin da lauyoyinsa suka musanta.

Tuni kotu a Faransa ta bayar da belinsa a kan Fan miliyan biyar, sannan ba zai bar Faransa ba, inda zai rinƙa kai kansa wajen ƴansanda sau biyu a kowane mako.

To shin ko wane ne wannan attajirin matashin mai shekara 39?

Wane ne Pavel Durov?

An haifa Pavel Durov ne a Saint Petersburg, inda ya karanci falsafa wato Philosophy.

Ya fara kasuwanci ne da buɗe shafukan intanet, amma abin da ya fara ɗaga darajarsa shi ne assasa dandalin sada zumunta na Vkontake a shekarar 2006.

Cikin ƙanƙanin lokaci VKontake ya zama dandalin sada zumunta mafi karɓuwa a Rasha.

Mista Durov ya ce a shekarar 2014 ya sayar da Vkontake ɗin ya bar Rasha saboda hukumomin tsaron ƙasar sun buƙaci ya bayyana bayanan masu amfani da dandalin, waɗanda suke goyon bayan zanga-zangar Euromaidan ta Ukraine.

Kafin nan, a shekarar 2013, ya riga ya assasa kafar Telegram, inda yake shugabancin kamfanin daga Dubai, inda yake zaune.

Yana da shaidar zama ɗan ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Faransa, amma Rasha ta ce har yanzu tana masa kallon ɗan ƙasarta.

Mene ne dandalin Telegram?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dandalin Telegram na cikin manyan dandalin sada zumunta a duniya irin Facebook da WhatsApp da Instagram da TikTok da WeChat.

Dandalin ya samu karɓuwa matuƙa tun daga assasa shi a shekarar 2013, inda a watan Yuli Mista Durov ya yi iƙirarin cewa masu amfani dandalin sun kusa kai biliyan ɗaya.

Abin da ke bambanta Telegram da sauran kafofin sadarwa shi ne misali, yadda za ka iya ba na’ura damar bayar da saƙo a madadinka.

Sannan za a iya yin hira a sirrance domin ɓoye bayanan masu yi, kuma za a iya buɗe zaure da zai ɗauki har zuwa mutum dubu 200.

An yi amfani da dandalin a lokacin zanga-zangar da aka yi a Belarus da Hong Kong, sannan ya samu karɓuwa matuƙa a Rasha da Ukraine.

Harwayau, dandalin Telegram a baya-bayan nan ya zamo manhajar da masu "mining" suka fi amfani da ita a harkokin kuɗaɗen intanet kirifto.

Mai dandalin na Telegram ya fito ya bayyana cewa ba zai bayyana bayanan masu amfani da dandalin ga gwamnati ba a baya. A 2016, ya ƙi amincewa da buƙatar masu bincike na gwamnatin Amurka, sannan a 2017 ya ƙi ba Rasha wasu bayanai da sashen bincike na Rasha wasu bayanai.

Amma damar ɓoye bayanai da Telegram da yake da shi ya sa ana gudanar da wasu harkokin da ba su dace ba, wanda shi ne ya sa aka kama Pavel Durov.

Bayan kama Mista Durov, Telegram ya ce tsare-tsarensu, “na daidai da tsare-tsaren ɓangaren kuma kullum suna ta ƙoƙarin inganta shi.”