Waiwaye: Gyara matatar Fatakwal da kama Yahaya Bello
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Asalin hoton, Getty Images
A cikin makon da ke ƙarewa ne matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Rivers ta dawo aiki, inda ta fara tace man fetur, kamar yadda babban jami'in hulɗa da jama'a a kamfanin NNPCL, Femi Soneye ya bayyana.
A cewarsa, "yau an samu wata gagarumar nasara domin matatar man fetur ta Fatakwal ta fara tace man fetur. Wannan wani sabon babi ne a ɓangaren makamashi a Najeriya, da yunƙurin inganta tattalin arzikin ƙasar," kamar yadda ya bayyana a ranar Talata.
Ya ce za a fara lodin man fetur ɗin daga yau Talata, sannan ya ƙara da cewa kamfanin na NNPCL na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ita ma matatar Warri ta fara aiki.
Wannan ya kawo ƙarshen gazawar cika alƙawurra na lokacin kammala gyaran matatar da gwamnati ta sha yi a baya.
Mun kama Yahaya Bello - EFCC

Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook
A ranar Tsalatar makon ne kuma Hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta sanar da kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Kafin hukumar ta tabbatar da kama shi rahotanni da dama na ambato cewa, tsohon gwamnan wanda ke fuskantar tuhumar almundahana, ya kai kansa ne ofishin hukumar da ke Abuja tare da rakiyar wasu lauyoyinsa.
A wani hoton bidiyo na tashar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumar tana tsare da tsohon gwamnan na Kogi.
Taƙaddama ta kasance tsakanin EFCC da tsohon gwamnan, bayan da hukumar ta ayyana nemansa a watan Afirilu, bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta sha aika masa tare da nuna tirjiya kan duk wani yunƙuri na kama shi, wanda hakan ya sa ya shiga kulli-kurciya da hukumar.
Tinubu zai tafi Faransa ziyarar aiki

Asalin hoton, state house
A ranar Laraba ne kuma shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tafi ƙasar Faransa domin wata ziyarar aiki.
A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ne ya gayyaci shugaban na Najeriya.
Onanuga ya ce ziyarar ta kwana uku ce, kuma za ta mayar da hankali ne, "kan inganta alaƙar tattalin arziki da dimokuraɗiyya da noma da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da samar da aikin yi ga matasa da sauran abubuwa muhimmai."
Sanarwa ta ƙara da cewa Tinubu zai yi tafiyar ce tare da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, inda shugaban na Faransa ta matarsa za su tarbe su.
Haka kuma Oluremi Tinubu da uwargidan shugaban ƙasar ta Faransa, Brigitte Macron za su gana game da shirin uwargidan shugaban Najeriya na Renewed Hope Initiative na inganta rayuwar matasa.
Gwamnatin Anambra ta yafe wa masu ƙananan sana'o'i haraji

Asalin hoton, Gwamnatin Anambra
A ranar Talata ne gwamnatin jihar Anambra ta cire masu ƙananan sana'o'i da jarinsu yake ƙasa da Naira N100,000 daga biyan haraji.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Law Mefor, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce gwamnatin ta zartar da hakan ne a ƙarshen taron majalisar zartarwar jihar karo na 37, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Mefor ya jaddada cewa har yanzu dokar yaƙi da zaman-banza da kashe wando da yawon tasha ta jihar har yanzu tana nan da ƙarfinta, a don haka ya shawarci matasa su shiga shirin koyar da sana'o'i da bayar da jari na gwamnatin jihar domin cin guminsu ta halaliya.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga masu zuba jari da su karɓi kamfanonin gwamnati na jihar, inda yake cewa bayar da su haya ko jinginar da su ga 'yan kasuwa ya fi a ce gwamnati na tafiyar da su.
Kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 200 ya kife a Neja

Asalin hoton, Other
A safiyar Juma'a ce aka wayi gari da kifewar wani kwale-kwale a sashen Dambo-Ebuchi na tekun Neja, wanda ya yi sanadiyar wasu mutane.
Waɗanda lamarin ya auku a gaban su sun shaida wa tashar Channels cewa, kwale-kwalen, wanda na wani mai suna Musa Dangana ne, yana tafe ne da fasinjoji sama da 200, ciki har da mata ƴankasuwa da masu aikin gona waɗanda za su tafi kasuwar mako-mako ta Katcha.
A watan Oktoba ne aka samu kwatankwacin hatsarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da ƙaramar hukumar Mokwa na jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.
NYSC ta sake buɗe sansanin horaswa na Zamfara bayan wata 16

Asalin hoton, X/NYSC
A cikin makon ne kuma hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya (NYSC) ta sake bude sansanin horaswa na jihar Zamfara, bayan rufe shi na wata 16 saboda dalilai na tsaro.
Yayin taron budewar da ya gudana a sansanin na wucin gadi da ke Gusau, an kuma rantsar da sabbin 'yan hidimar ƙasa na rukunin Batch C Stream 1.
Yanzu haka gwamnatin jihar na aikin sake gina sansanin horarwar na dindindin da ke karamar hukumar Tsafe.
Kulle sansanin da aka yi a shekarar 2023 ya janyo tsaiko ga matasan masu hidimar kasa da aka tura jihar, wadanda daga baya aka tura wasu jihohi kamar Kebbi mai maƙwabtaka.
Rashin kai matasan Zamfara na da nasaba da hare-haren da 'yanfashin daji ke kaiwa kusan a kullum, inda suke garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.










