Yadda matasan da aka haifa a Faransa ke komawa rayuwa a Afirka

- Marubuci, Nour Abida, Nathalie Jimenez, da Courtney Bembridge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
- Lokacin karatu: Minti 6
An haifi Menka Gomis a Faransa amma yana ganin zai fi samun damar rayuwar da yake so a Senegal, inda aka haifi iyayensa.
Menka mai shekara 39 yana daga cikin tarin 'yan Faransa asalin Afirka da ake ta samu suna barin Faransa, saboda ƙaruwar matsaloli na wariyar launin fata da nuna bambanci da asalin ƙasa.
Sashen BBC mai binciken ƙwaƙwaf (BBC Africa Eye) ya gudanar da bincike kan wannan batu - domin gano abin da ya sa matasa irin su Gomis suka dawo daga rakiyar rayuwa a Faransa
Gomis ya kafa wani kamfani na shirya tafiye-tafiye da ke bayar da garaɓasa, yawanci da ’yan Afirka musamman waɗanda suke son komawa ƙasashensu na asali, inda yanzu ya buɗe ofis a Senegal.
An haife ni a Faransa. Na taso a Faransa, kuma na san wasu abubuwa. Akwai wariyar launin fata sosai. Tun ina ɗan shekara shida a makaranta ake nuna min wariyar launin fata, kusan kullum, kamar yadda Mista Gomis, wanda ya yi makaranta a birnin Marseille ya sheda wa BBC.
Ya ce, ''Zan iya kasancewa Bafaranshe to amma kuma daga wani wuri na zo.''
Mahaifiyar Mista Gomis wadda aka kai Faransa tun tana jaririya, ta kasa gane dalilin da ya sa ɗan nata yake son barin dangi da abokansa ya koma Senegal.
Mista Gomis ya ce, ya ƙuduri wannan aniya ne saboda abu biyu, burin taimaka wa asalin inda iyayensa suka fito da kuma amfana da damar da ke tattare da nahiyar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Afirka kamar yankin nahiyar Amurka ta Arewa ne da Amurka ta Kudu a lokacin arziƙin zinare. Ina ganin nahiya ce da za ta bunƙasa nan gaba. Waje ne da zai rayu nan gaba,'' in ji shi.
Alaƙar da ke tsakanin Faransa da Senegal - ƙasar da yawancin mutanenta Musulmi ne, wadda Faransa ta yi mata mulkin mallaka, wadda kuma ta kasance wata cibiya mai muhimmanci a lokacin cinikin bayi zuwa Turai da Amurka - alaƙa ce mai tsawo da kuma sarƙaƙiya.
A wani bincike da BBC (BBC Afirka Eye) ta yi kwanan nan ta haɗu da wasu 'yan Senegal, waɗanda suka ƙuduri aniyar yin tafiyar nan mai haɗarin gaske ta teku zuwa Turai.
Da yawa daga cikin irin waɗannan 'yan cirani suna zuwa Faransa ne inda, hukumar kare 'yan gudun hijira da mutanen da ba su da ƙasa, ta ce an samu yawan mutanen da ba a taɓa samu ba da ke neman mafaka a ƙasar a shekarar da ta wuce.
Jumulla kusan mutum 142,500 ne suka nemi mafakar kuma an amince da buƙatar kusan kashi ɗaya bisa uku.
Sai dai ba a san mutum nawa ne kuma ke son barin Faransa su koma Afirka ba kuma saboda dokar Faransa ta haramta tattara bayanai a kan launin fata da addini da kuma ƙabila
To amma bincike ya nuna ƙwararrun 'yan Faransa waɗanda iyayensu Musulmi ne, yawanci 'ya'yan baƙi, suna sulalewa suna kowa.
Waɗanda BBC ta tattauna da su suna alaƙanta hakan da matsaloli na wariyar launin fata da kuma dokoki da ake ƙara tsanantawa kan baƙi inda masu ra'ayin riƙau ke ƙara samun iko a mulkin Faransa.

Asalin hoton, AFP
Fanta Guirassy na zaune duk tsawon rayuwarta a Faransa, kuma tana gudanar da aikinta na jinya a garin Villemomble - a wajen Paris - to amma ita ma a yanzu tana shirin komawa Senegal, inda aka haifi mahaifiysarta.
"Abin takaici ne a 'yan shekarun nan muna rayuwa cikin yanayi na farba da ɗar-ɗar a Faransa. Abin takaici ne mutum ya faɗi haka to amma gaskiyar lamari kenan,'' in ji Fanta mai shekara 34 a tattaunawarta da BBC.
Ta ce wasu abubuwan da kake gani suna faruwa a talabijin yau sai ga shi sun faru da kai ko wani naka, ''wannan abin tashin hankali ne.''
A watan Yuni na bara tarzoma ta ɓarke a faɗin Faransa bayan da 'yansanda suka harbe wani matashi mai shekara 17, ɗan Faransa, asalin Moroko da Algeria, Nahel Merzouk.
Wannan tarzoma ta tayar da hankali a Faransa - inda take nuni da irin damuwar da tsiraru suke ciki tsawon shekaru a ƙasar.

Wani bincike da aka yi kwanannan a Faransa a kan baƙaƙen fata ya nuna cewa kashi 91 cikin ɗari an taɓa nuna musu wariyar launin fata.
Sakamakon wannan tarzoma da aka yi a Faransa hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga Faransa ta magance matsalolin na nuna wariya a cikin jami'an tsaronta.
To amma ma'aikatar harkokin wajen faransa ta yi watsi da kiran, inad ta musanta zargin nuna wariyar launin fata da wasu bambance-bambance.
Sai dai kuma alƙaluman ma'aikatar cikin gida ta Faransa sun nuna cewa an samu ƙaruwar miyagun laifuka da ke da alaƙa da bambancin launin fata ko addini ko asali da kashi ɗaya bisa uku.
I want to go to work without having to remove my veil"
A Faransa sanya kallabi ko ɗankwali ko hijabi abu ne mai janyo taƙaddama sosai, inda shekara 20 da ta wuce aka haramta sanya su a dukkanin makarantun gwamnati.
Wannan dalilin ne ya sa Audrey Monzema, malamar makaranta, 'yar Faransa asalin Kongo, take son barin Faransar ta koma Senegal inda take ganin za ta iya gudanar da addininta na Musulunci da kuma al'adunta ba tare da wata tsangwama ko takura ba.
Wani bincike na kwanan nan ya nuna cewa sama da Musulmi 1,000 'yan Faransa, waɗanda suka bar ƙasar suka koma wata ƙasar waje suma kusan irin wannan dalilin ne ya sa su ƙaura.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta maƙala a kan yadda ake ƙaura daga Faransa (France, You Love It But You Leave It), Olivier Esteves ya sheada wa BBC cewa, wannan ƙaura tana raba ƙasar da ƙawararru ne, domin yawanci masu ilimi ne Musulmi 'yan Faransa suke tafiya.

Fatoumata Sylla, mai shekara 34, ƙwararriyar mai yin manhajar kwamfuta a kan yawon buɗe idanu, ta ce,'' lokacin da mahaifinmu ya bar Afirka ya zo nan Faransa domin samar wa iyalinsa rayuwa mai kyau a Afirka, har kullum yana gaya mana kada ku manta da inda kuka fito.
Fatoumata wadda take shirin komawa Senegal a wata mai zuwa, ta ce da wannan ƙuduri nata ta nuna cewa ba ta manta da asalinta - kodayake ɗan-uwanta Abdoul, wanda shi ma kamarta aka haife shi a Paris bai ga dalilin wannan ƙaura ba.
Ya ce, shi al'adarsa da iyalinsa suna nan Faransa. Afirka nahiyar kakanninsu ce. Ba lalle tasu ba ce saboda ba a can yake zaune ba.
Kuma yana ganin ba zai samu al'umma da take da cigaba da fasaha ba kamar Faransa take.
When I arrived in Senegal three years ago I was shocked to hear them call me 'Frenchie'"
A Dakar, mun haɗu da Salamata Konte, mai shekara 35, wadda ta bar aikinta na banki a Paris ta koma Senegal, wadda suka kafa kamfanin shirya yawon buɗe idanu da Mista Gomis, inda muka ji daga gareta abin da ke jiran 'yan Faransa asalin Afirka da ke komawa Afirkar.
Ta ce, ''lokacin da na zo Senegal shekara uku da ta wuce na sha mamaki inda na ji suna kirana Bafaranshiya.''
''Da farko wannan ita ce matsalar, can a Faransa an ƙi ka, nan ma kuma Afirka da ka dawo ana ƙinka,''
Nan da nan na tashi tsaye, '' Na ce musu e lalle an haife ni a Faransa, amma ni ma 'yar Senegal ce kamarku.''
Shawararta ita ce, ''idan za ka koma dole ne ka zama mai yakana da kankan da kai da mutunta jama'a, wannan shi ne abin da na yi''
Sai dai kuma a matsayinta na mace 'ayr kasuwa ta ce abin da wuya sosai saboda a cewarta, ''mazan Senegal sun tsani ganin mace a matsayin shugabarsu, tana ba su umarni...''
Duk da haka Mista Gomis na cike da farin ciki yayin da yake zaman jiran samun takardarsa ta ɗan-kasa ta Senegal.










