Kane ya ci uku rigis a wasan da Bayern ta doke Stuttgart

Asalin hoton, Getty Images
Kaftin ɗin tawagar Ingila, Harry Kane ya ci ƙwallo uku rigis a wasan da Bayern ta doke Stuttgart da ci 4-0.
Da farko wasan ya so bai wa wa Munich wahala, lamarin da ya sa har aka shiga zagaye na biyu ba tare da cin ko ƙwallo guda ba.
Sai a minti na 57 ne Kane ya samu damar buɗe ragar Stuttgart, wani mataki da ya buɗe wa Munich ƙofar nasara a fafatawar.
Ɗan wasan gaban ya samu zura ta biyu da ta uku a mintina na 60 da 80, yayin da Kingsley Coman ya ci ta huɗun a minti na 89.
Ya zuwa yanzu Kane ya ci ƙwallo takwas a wasa bakwai na gasar Bundesliga a bana.
Da wannan sakamako Bayern - wadda a baya ta yi canjaras biyu a jere - ta koma mataki na ɗaya a kan teburin gasar Bundesliga da bambancin ƙwallaye tsakaninta da RB Leipzig.







