Mawaƙan Hausa biyar da aka karrama da digirin girmamawa

Asalin hoton, YouTube
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
A daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan batun digirin girmamawa da kai-komo da aka samu kan karramawar da aka yi wa fitaccen mawakin Hausa Dauda Kahutu Rarara, hankali ya fara komawa sama kan shin me ya sa lamarin ya ja hankali?
An dai gudanar da wani taro ne a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda aka ce wata jami'a ta karrama fitaccen mawaƙin da digirin girmamawa, taron da ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da wasu ‘yan siyasar arewacin Najeriya.
Sai dai kuma tun kafin a je ko'ina ne sai murna ta koma ciki, inda aka tsinci wata sanarwa a yanar gizo daga jami'ar European-American, inda a ciki ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan digirin na girmamawa.
Wannan ya sa wasu suke ganin mawaƙin ya cancanci karramawar, yayin da wasu suke ganin da sauran aiki a gabansa kafin samun irin wannan girmamawar.
Shin waɗanne mawaƙan Hausa ne a baya suka taɓa samun irin wannan karramawar?
BBC ta waiwayi tarihi, inda ta zaƙulo mawaƙan, tare da tattaunawa da masani kan ko karramawar na da wani tasiri a harkarsu ta waƙar.
Mamman Shata - Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria

Asalin hoton, BAKANDAMIYA.COM
Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria ce ta karrama fitaccen mawaƙi Alhaji Mamman Shata a shekarar 1991da digirin girmamawa.
Am haifi fitaccen mawaƙin ne a shekarar 1923 a garin Musawa da ke jihar Katsina, kuma ya rasu a shekarar 1999.
Shata ya yi waƙoƙi fitattu da suka yi shuhura, ciki har da 'Bakandamiya' da sauran waƙoƙinsa da har yanzu suke tashe da tasiri.
Mamman Shata ya bayar da gagarumar gudumawa a fagen adabin Hausa ta hanyar wakokinsa wadanda ake yin nazari kansu a jami’o’i da dama.
Ɗan Maraya jos

Asalin hoton, Jaridar Taskar Labarai/Facebook
An haifa Adamu Muhammadu Wayya, wanda aka fi sani da Ɗanmaraya Jos ne a garin Bukuru da ke Jos a jihar Filato amma an ce asalin mahaifinsa mutumin Sokoto ne, kuma ya yi fice da waƙarsa da ake amfani da kutuginsa.
Daga cikin waƙoƙin da ya raira akwai 'Karen mota' da 'Auren Dole' da 'Ɗan'adam' wadda ta fi tashe ta 'Mai Akwai da Babu' da sauran su.
Jami'ar Jos ce ta karrama marigayin da digirin girmamawa.
Akilu Aliyu

Asalin hoton, Jaridar Taskar Labarai/Facebook
An haifa marigayi Alhaji Aliyu Akilu a garin Jega na jihar Kebbi a yanzu ne a shekarar 1918, sannan ya rasu a shekarar 1999.
Sai dai fasihin marubucin waƙoƙin ya yi rayuwa sosai a jihar Kano, sannan ya yi rubutattun waƙoƙi da dama da suka yi shuhura, musamman wajen isar da saƙo cikin hikima.
Daga cikin waƙoƙinsa akwai Waƙar Najeriya da 'Matan Aure' da 'Bahaushe mai ban haushi' da sauran su.
Jami'ar Bayero da ke Kano ce ta karrama marigayin da digirin girmamawa.
Aminu Ala

Asalin hoton, ZURIA FM 88.7
Aminu Ladan, wanda aka fi sani da Aminu Ala, ko Alan waƙa yana cikin mawaƙan da suka yi tashe a wannan zamanin, wajen gwanancewa a isar da saƙo da hikima.
An haife Aminu Ladan Abubakar a shekarar 1973) a jihar Kano, kuma ya yi waƙoƙi fitattu irin su 'Jami'a" da sauran su, sannan marubuci ne da ya rubuta littafai da dama, kamar 'Jirgi daya Ke dauke Da Ni' da 'Ceto Ko Cuta?
Jami'ar HEGT ta Jamhuriyar Benin ce ta karrama shahararren mawaƙin a shekarar 2020.
Nura M. Inuwa

Asalin hoton, Dr. Nura M inuwa/Facebook
Nura Musa Inuwa, wanda aka fi sani da Nura M Inuwa mawaƙi ne na zamani wanda aka haifa a jihar Kano a shekarar 1989.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin matasan mawaƙa da suka ƙware wajen jera magana da aika saƙo a cikin waƙoƙinsa.
Daga cikin fitattun waƙoƙin da ya yi akwai 'Aisha humaira' da 'Rai dai da 'Badi ba rai' da sauran su.
Jami'ar Jagora ta Faransa ce ta karrama mawaƙin a shekarar 2023 kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.
Wane tasiri karramawa ke da shi a kan mawaki?
A game da ko wannan digirin karramawar tana da wani tasiri, masanin waƙoƙin Hausa na dauri da na zamani, Malam Ibrahim Sheme ya ce lallai karramawar ta yi tasiri wajen ƙara tagomashi ga mawaƙan baya.
Ya ce, "Yana tasiri ga mawaƙan da, domin ya ƙara masu martaba a idon duniya. Kamar Shata dai, a lokacin da aka ba shi digirin yana tsakiyar baƙar adawa da yawancin mawaƙan Hausa irin su Ɗankwairo da Ahmadu Doka, amma da aka ba shi digirin sai suka saduda, suka ajiye makaman,"
Sheme ya ƙara da cewa bayan karramawar, sai mawaƙan da suke adawa da shi, suka nemi shiri da shi "saboda sun ga cewa a gwamnatance an tabbatar da shi ne jagoran su."
Masanin kuma ya ce, "Sannan ita karramawa irin wannan tana ƙara ƙaimi ga mawaƙi, ta saka masa shauƙin fifiko a cikin mawaƙa 'yan'uwansa. Daga nan duk waƙar da zai yi sai ya yi ƙoƙarin ƙara zurfafa fiƙira saboda ya san ana masa kallon shi gwani ne."
Wane mawaƙi ne ya cancanci a karrama shi?
A game da ko akwai mawaƙan da suka cancanci karramawar a cikin mawaƙan zamani, Malam Sheme ya ce jami'a ce kaɗai za ta iya tantance wanda ya dace ta bai wa digirin girmamawa.
"Amma akwai tsarin da ake bi, misali akan kafa kwamitin ƙwararru wanda zai yi nazarin mawaƙin da ya dace. Za a samar da dalilan bayar da digirin wanda duk wanda ya ji zai gamsu."
Masanin ya ce digirin girmamawa iri biyu ne, "akwai na mutum mai rai da na mamaci. Misali, a shekarun baya mun taɓa kafa kwamitin nema wa Alhaji Musa Ɗankwairo digirin girmamawa, shekaru sama da ashirin bayan rayuwar sa, amma ba mu yi nasara ba."
A ƙarshe, Sheme ya ce "ba tashen mawaƙi ko dukiyar sa kaɗai ne cancanta ba, sai dai tasirin sa a kan adabin baka da gudunmawar sa ga cigaban al'umma ta hanyar waƙoƙin sa. Saboda haka, duk mawaƙin da za a iya ba digirin girmamawa sai ya cike waɗannan muradun."











