Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa rigingimun duniya ke assasa sha'awar ilimin taurari?
- Marubuci, Lebo Diseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 6
Da yawa cikinmu mun san aƙalla mutum guda da ya taɓa binciken tauraronsa da na buduruwa ko saurayi domin fahimtar dacewa da juna.
Yayin da wasu ke ɗaukar hakan a matsayin wasa ko raha, akwai mutane da dama da suka ɗauki ilimin taurari da matuƙar muhimmanci.
Sun yi imanin cewa tafiyar burujin tauraronsu a lokacin haihuwarsu na da matuƙar tasiri a rayuwarsu, da halayensu da kuma mu'amalarsu.
An kwashe ƙarnuƙa masu yawa ana amfani da wannan ilimi a ƙasashe irin China da Indiya.
A Indiya wasu ƴansiyasa kan tuntuɓi masana ilimin taurari domin duba musu yiwuwar cin zaɓukansu.
To sai dai da alama yanzu wannan tsari ya fara samun karɓuwa a ƙasashen Yamma, inda suke amfani da shi domin hasashen siyasarsu da wasu manyan al'amuran duniya.
A yanzu ƙasashen Turai da Amurka cike suke da yunwar ilimin da kuma amfani da shi.
Dandalin TikTok cike yake da bidiyoyin - mafi yawansu daga Arewacin Amurka - na masana ilimin taurari da ke bayar da bayanin siyasar yankunan duniya ta hanyar amfani da limin.
"Tauraron Donald Trump ya nuna kamamceceniya da na ƙasar Iran, abin da ke nuna cewa za a iya samun dangantaka mai ƙarfi tsaknainsu.'' Kamar yadda wani masanin ilimin taurari ya bayayna cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin TikTok rana guda bayan Amurka ta ƙaddamar da hari kan Iran.
Shi ma wani mutum ya wallafa wani bidiyon a wannan rana, wanda ke hasashen cewa Iran za ta mayar da harin martani ranar 1 ko biyu ga watan Yuli.
Kasancewar hasashe irin wannan ba lallai yake zama gaskiya ba, hakan ba ya nufin za a samu raguwar wallafa irin waɗannan bidiyoyi ko samun raguwar buƙatarsu ba.
Cikin shekara biyar da suka wuce, shafin Google Trends - da ke nuna abubuwan da aka fi neman bayaninsi - ya nuna yadda kalmomin ''ilimin Taurari'' da ''Yaƙi'' suka yi fice cikin abubuwan da ake neman bayanai a kansu.
Musannan a farkon ɓarkewar annobar covid a watan Fabrairun 2020 da farkon yaƙin Rasha da Ukraine a Fabrairaun 2022, da yaƙin Indiya da Pakistan da ya faru cikin watan Mayun 2025 da kuma cikin watan Yunin 2025 lokacin da Amurka ta kai hare-hare cikin Iran.
Wata ƴar ran da ke zaune a London ta shaida wa BBC cewa a lokacin da boma-boman suka faɗa kan Tehran, ta tuntuɓi masanin ilimin taurari, kamar yadda ƴar'uwarta ta yi a Iran suna masu neman tabbacin makomar ƙasarsu.
A lokacin da kalaman ''Ilimin taurari'' da ''yaƙi'' suka fi yawa a google search, ƙasashen Indiya da Arewacin Amurka ne kan gaba cikin masu neman bayanai game da kalaman.
Amma yin amfani da ilimin taurari don gwadawa da fahimtar "babban rikice-rikice na ɓangarorin duniya bai dace ba", in ji Dokta Galen Watts, na Jami'ar Waterloo da ke Kanada wanda ya ƙware a fannin zamantakewar al'adu da addini.
Aliza Kelly, ƙwararriya a fannin ilimin taurari da ke zaune a birnin New ta yi maraba da ƙaruwar nuna sha'awa a fanninta, amma ta ce akwai damuwa game ƙa'idojin ilimin a wasu bidiyoyin da ake wallafawa a shafukan sada zumunta.
"yin hasashen waus abubuwa masu girman gaske kamar harin nukiliya ko yaƙin duniya na uku, a bidiyo na 90 na biyu ba zai yiwa a bi ƙa'idar yaɗa waɗannan bayanai ba,'' in ji ta.
Ta ce irin waɗannan bidiyoyi kan samu karɓuwa saboda ba a yi su bisa ƙa'idar ilimin ba.
"Ab ne mai hatsarin yin hisabi ko duba ta hanyar amfani da sunan da akwai kukure a cikinsa, ko tauraronsa. Wannan ba irin ilimin taurari ba ne da nake so in yi," in ji Kelly.
Ta ce ta fahimci yawan ƙaruwar sha'awar mutane a fannin, waɗanda ke amfani da taurari wajen lissafin siyasar duniya.
Ta fara yin fice a daren zaɓen shekarar 2016, lokacin da Trump ya doke Hillary Clinton ya zama shugabar Amurka. Ta kasance a wurin wani biki, inda baƙi ke manne da talabijin yayin da suka ga sakamakon na tafiya ta wata hanya daban fiye da yadda aka yi hasashe.
"Mutane sun riƙa zsuwa wurina a matsayina na wadda ta san ilimin taurari domin sanin abin da ke faruwa. Me zai faru a yanzu? me taurarin Hilary suka nuna? me na Trump suka nuna?
"Wannan ne karo na farko da na fara ganin hakan, inda mutane ke son a yi amfani da limin taurari domin fahimtar abubuwan siyasa da suaran fannonin duniya,'' in ji Kelly.
Shi ma annobar covid, wannan babban al'amari ne da aka riƙa amfani da ilimin taurari wajen hasashen abubuwa.
A daidai wannan lokaci ne Cassie Leventhal ta fara buƙatr ilimin taurari domin duba manyan ɓarkewar annobar. Duka iyayenta a loacin na da cutar kansa kuma an fara yi musu magani a lokacin.
Shawarar da ta bai wa iyayen nata ya yi daidai da na ma'aikatan lafiya, amma Cissie ta ce ta yi amfani da taurari wajen bai wa iyayen nata shawarar da ya kamata su bi.
Lokacin da na tambayi Cassie cewa ilimin taurari ba shi da tushe na kimiyyance, ta ce tana kallonsa a matsayin "wani abu da za a iya koya, a kuma yi amfani da shi, lokacin da kuke buƙatar ƙara zurfi zuwa [fahimtar ku game da halin da ake ciki".
Cassie ta shaida min cewa ta yi amfani da ilimin taurari wajen fahimtar siyasar Amurka.
Ɗabi'a ko addini?
Dakta Watts ya ce "Akwai lokutan da ake ɗaukar iimin taurari a matsayin wani abu na ibada ko addini.''
"Mutanen da ke tuntuɓar taurari suna zaton cewa akwai wani nau'in tsari na sararin samaniya, wanda a wani bigiren na da muhimmin tasiri ga rayuwarsu," in ji Dr Watts.
Duk da wannan, hanyoyin da ake bi wajen fahimtar ilimin taurari ya bambanta a fadin duniya.
A lal misali a Indiya, ana ɗaukar ilimin taurari da matuƙar muhimmanci, domin akan yi amfani da ilimin wajen gano dacewar masoya idan za su yi aure, ko ɗaukar matakin rabuwar aure.
Sai dai saɓanin haka, Dakta Watts ya ce a ƙasashen Yamma akan yi amfani da ilimin taurari kan ɗaiɗaikun al'amura.
Duk da labarin bunƙasar ilimin taurari a ƙasashen Yamma, bayanai daga Cibiyar Pew sun nuna cewa adadin mutanen da ke amfani da shi a Amurka ba su da yawa.
A cikin 2017 da 2024, kusan kashi 27% na mutane a Amurka sun ce sun yi imani da ilimin taurari.
To amma me ya sa ake cewa akwai ƙaruwar lamarin, bayan kuwa alƙaluma suna nuna wani abu daban?
Dakta Watts ya bayar da hujjar cewa a baya ba a la'akari da addini a batutuwan tattaunawa, musamman ta kafofin watsa labarai. Amma zaɓen Trump a matsayin shugaban Amurka a shekara ta 2016 ya kawo "sauye-sauye masu tsauri a fagen siyasar kasa".