Yaushe jami'an tsaron Najeriya za su daina raka manoma gona?

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da ci wa wasu al'umomin arewacin Najeriya tuwa a ƙwarya, musamman manoma da a wasu lokuta 'yan bindiga ke hana su zuwa gonakinsu domin noma ko girbe amfanin gonarsu, ko ma yanka musu haraji mai tarin yawa kafin su je gonakin nasu.

Manoman a ke waɗannan yankunan sun koka kan yadda suka ce 'yanbidigar na addabarsu a gidaje da kuma gonakin nasu , kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaida wa BBC.

Mazauna yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun ce matsalar ta yi ƙamari ne musamman yadda ɓarayi suka addabe su.

“Ƴan bindigar za su zo ana cikin aikin gona su koma gefe, su kasa su tsare bayan an gama tattara amfanin gona an saka a buhu su ce nasu ne.”

“Sannan kuma su ce a saya a ba su kuɗin bayan tattara amfanin gonar,” kamar yadda wani mazauni yankin Birnin Gwari ya shaida wa BBC.

Ya ce manomi ba zai iya kwashe amfanin gonarsa ba har sai ya kammala biyan harajin da ɓarayin suka aza masa.

“Idan kuma mutum ya gaza biyan kuɗin da suka buƙata, sai dai ya bar amfanin gonar a nan.”

“Wannan matsala ta tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira.” in ji shi.

Lamarin da ya sa a wasu lokutan jami'an tsaro ɗauki matakai daban-daban na taimaka wa manoman ciki har da raka su gonakin nasu dokin gudanar da ayyukansu a wasu lokutan.

Batun raka manoma gona da jami'an tsaro ke yi, ya jima a ƙasar, wani batu da wasu 'yan ƙasar ke aza ayar tambayar cewa yaushe wannan matsala za ta kawo ƙarshe.

Jam'an tsaron Najeriya

Asalin hoton, AFP

Yaushe matsalar ta faro?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazari kan al'amuran tsaro ya ce matsalar ta faro daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, sakamakon matsalar Boko Haram.

''Hakan kuma ya faru ne, musamman saboda yadda 'yan bindigar ke hana manoma zuwa gonakinsu, domin yin noma ko girbe amfanin gona'', in ji shi.

Ya ce daga nan ne jami'an tsaro na rundunar Operation hadin kai da wasu rundunonin tsaro ciki har da Civil Defence suka zauna suka yi yarjejeniya da gwamnatin jihar domin gudanar da wannan aiki ƙarƙashin shirin.

Masanin tsaron ya ce matsalar ta faro ne kusan shekara biyu da suka gabata, ko ma fiye da haka.

Baya ga yankin arewa maso gabas, Dakta Kabiru Adamu ya ce an samu ɓullar wannan matsala a jihohin arewa maso yamma, musamman Zamfara da Katsina, inda ya ce matsalar ta fara a baya-bayan nan.

''Kuma a halin yanzu, jihohin Zamfara da Katsina ne kan gaba inda wannan matsala ta fi ƙamari, sai kuma jihar Kaduna da ke biye musu'', in ji shi.

Ta yaya ake rakiyar?

Dakta Kabiru Adamu ya ce yadda ake rakiyar shi ne manoman ba za su je gonakin nasu ba, har sai manoman sun tabbatar da tsaro a wannan yanki.

''Yadda ake yi shi ne jami'an tsaron ne ke zuwa su yi wa gonakin ko garuruwan da ke kusa da gonakin ƙawanya, sannna sai manoman su shiga gonakinsu domin gudanar da harkokinsu''.

Wa ke ɗaukar nauyin rakiyar?

Jami'an tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Kabiru Adamu ya ce galibi gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomin da ke fuskantar matsalar ne ke ɗaukar nauyin rakiyar.

''Ba wani jami'an tsaron suna yi ne don aikinsu ba, a'a shiryawa ake yi tsakaninsu da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi waɗanda ke ba su abin da suke kira ''kuɗin man mota'', domin gudanar da aikin.

Dakta Kabiru Adamu ya ce ba shi da labarin ko mutanen gari na biyan irin wannan kuɗi, amma kuma ya ce hakan ba zai kore ikirarin cewa suna biyan ba.

Yaushe jami'an tsaro za su daina raka manoma gona?

Masanin tsaron ya ce hanya guda na kauce wa matsalar ita ce samun ingantacciyar gwamnati da za ta jajirce wajen magance matsalar.

''Idan na ce haka, ba ina nufin gwamnatin tarayya kaɗai ba, har ma da gwamnatocin jihohi''.

Data Kabiru Adamu ya ce mafi yawan gwamnonin jihohin arewacin Najeriya ba su shirya wa kawo ƙarshen wannan matsala ba.

''Sakamakon aikin da nake yi yi, na kan ziyarci wasu jihohin, kuma har yau ban ga gwamnan da ya gwamnan da ya naɗa kwamishinan tsaro kuma aka sakar masa komai, ya zama wuƙa da nama a fannin tsaron,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa abin da ya kamata a yi, shi ne gwamnatoci a matai daban-daban su nuna cewa da gaske suke wajen yaƙi da matsalar tsaron.

''Yana da kyau idan za a naɗa jagorin hukummomin tsaro, a riƙa naɗa waɗanda suka san matsalar, don mutum ya taɓa zama soja ko ɗan sanda ba shi ke nuna ya san matsalar tsaro ba, dole ne sai ka karanta wannan tsarin kana kuma da matsaniya kan matsalar'', in ji shi.

Dakta Kabiru Adamu ya ce tanade-tanaden da jihohin Legas da Edo da kuma Enugu suka yi kan tsari, babu wata jiha guda a arewacin kasar da ta kusa kama ƙafar waɗanann jhohi.

''Kuma idan ka duba wannan matsala ta tsaro kusan kashi 80 cikin 100 na matsalar a arewacin Najeriya suke''.

Ya ce abin da ya kamata gwamnati ta saka a ranta shi ne, ta yi amfani da sashen kundin tsarin mulkin ƙasar, da ya yi tanadin cewa dole ne gwamnati ta samar wa mutanenta cikakken tsaro.

''Dole ne su san wannan, su kuma san muhimmancin wannan'', in ji masanin tsaron.