Waɗanne ƙasashen Afirka ne ba sa goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Marina Daras
- Lokacin karatu: Minti 4
Bayan da ƙasashen Birtaniya da Canada da kuma Australia suka shiga jerin waɗanda suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinawa, ana sa rana wasu ƙasashen su ma su bi sahu.
To amma yaya ƙasashen Afirka ke kallon batun kafuwar ƙasar Falasɗinawa?
Akasarin ƙasashen Afirka sun amince da kafuwar ƙasar Falasɗinawa tun a shekarun 1980 bayan da bayan da jagoran Falasɗinawa Yasser Arafat ya ayyana ƴancin kan yankin a birnin Algiers.
Shugabanni irin su Thomas Sankara da Nelson Mandela duk sun alaƙanta fafutukar neman ƴancin Falasɗinawa da fafutikar ƙasashen Afirka na samun ƴanci.
Sai dai, ƙasashe biyu - Kamaru da Eritrea - ba su yi hakan ba.
Mun duba wasu daga cikin dalilansu.
Kamaru

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Kamaru tana da alaƙa sosai da Isra'ila.
Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Ƙasashen Afirka da tsare-tsare a Geneva, David Otto ya ce Isra'ila na kallon Kamaru a matsayin ɗaya daga cikin ƙawayenta na kusa a Afirka.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce "Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alaƙar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra'ila ba."
Ya ce alaƙarsu na da ƙwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro.
"Isra'ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru," in ji shi.
Isra'ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban ƙasar.
"Haka nan kuma kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Kamru da Isra'ila ta sanya Kamru ɗin tana samun goyon baya daga Amurka ta bayan fage."
Haka nan kuma matsayar Kamaru game da yankin Falasɗinawa, akwai yiwuwar yana da alaƙa da artabun da take yi da ƴan aware na yankin da aka fi amfani da harshen Ingilishi a ƙasar.
"Amincewa da ƙasar Falasɗinawa zai iya haifar da ƙarin matsi a cikin ƙasar, wanda hakan zai alamta cewa su ma masu fafutikar ƙwatar ƴancin kai na ƙasar, su ma suna da hujja ke nan. Bayan kuwa Kamaru ta nanata cewa ita ƙasa ɗaya ce wadda ba za ta ɓalle ba," in ji Otto.
A yancin lokaci Kamaru na kame bakinta ne kawai a duk lokacin da ake magana kan amincewa da kafa ƙasar Falasɗinawa.
Ita kuwa Eritrea, tata matsayar na da dalilai da suka sha bamban, waɗanda suka samo asali daga tata fafutikar ta samun ƴanci.
Eritrea

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 1988 lokacin da Yasser Arafat ya ayyana ƴancin ƙasar Falasɗinawa, yana buƙatar goyon bayan ƙasashen Afirka.
Ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashen ita ce Ethiopia.
"Wadda ita ce ke da mazaunin cibiyar Ƙungiyar Hadin kan Ƙasashen Afirka a wancan lokacin, wadda daga baya ta koma Tarayyar Afirka, a birnin Addis Ababa," in ji mai sharhi kan siyasa ɗan ƙasar Ehiopia, Abdurahman Sayed.
"Gwamnatin mulkin soji ta wancan lokacin tana kuma goyon bayan Tarayyar Soviet, saboda haka tana goyon bayan ƴanci da kuma hakkin Falasɗinawa."
To amma a lokacin ita kuma Eritrea tana fafutikar neman ƴancinta daga Habasha.
"A bayyane yake cewa a wancan lokacin Habasha ta mamaye Eritrea. Kuma a lokacin ƴan Eritrea sun ɗauki makamai suna neman ƙwatar ƴancin kansu daga Habasha," in ji Sayed.
"A lokacin idan har Falasɗinawa na son yin kyakkyawar alaƙa da Ethiopia to dole ne su nesanta kansu daga Eritrea, kuma ina ganin abin da Yasser Arafat ya yi ke nan, lamarin nda bai yi wa ƴan Eritrea daɗi ba, ciki har da shugaban Eritrea na yanzu," in ji shi.
Sai dai duk da haka, shugaban ƙasar Eritrea Isaias Afwerki ya nuna tausayawa ga Falasɗinawa, a 2012 ma ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da bai wa yankin Falasɗinawa matsayin "mai sa ido" a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai kuma ya yi watsi da tattaunawar zaman lafiya ta Oslo, wadda ta samar da tsarin zaman lafiya da ya bai wa Falasɗinawa ƙwarya-ƙwaryar ƴancin kai a wani yankin Gaɓar Yamma da Gaza, a matsayin wani mataki na samun ƴancin kai.
"Shugaban Eritrea na daga cikin na farko-farko da suka yi watsi da yarjejeniyar Oslo a 1993, inda ya bayyana ta a matsayin maras amfani wadda ba za ta taimaka wajen warware rikicin da ake fama da shi ba ko kuma hanƙoron yankin na samun ƴancin yankin Falasɗinawa," in ji Abdurahman Sayed.
Shugaba Afwerki ya ce ba ya goyon bayan kafa ƙasa biyu.
To sai dai zai iya fuskantar matsi daga cikin gida kasancewar kashi 55 cikin ɗari na al'ummar ƙasar Musulmai ne.
"Eritrea ta samu nasara a fafutukarta ta samun ƴanci. Saboda haka a ce mutumin da ya jagoranci fafutikar samun ƴanci kuma ba ya goyon bayan wasu su samu ƴanci, za a ga kamar hakan ba abu ne mai kyau ba. Za su fuskanci matsi," in ji Sayed.
BBC nemi jin ta-bakin gwamnatocin ƙasashen biyu, amma ba su bayar da amsa ba.











