Yadda Falasɗinawa ke da shugabannin ƙasa da yawa, duk da ba su da ƙasarsu ta kansu

Shugaban Falasɗinawa na yanzu Mahmoud Abbas tare da tsohon Shugaba Yasser Arafat a 2003

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Falasɗinawa na yanzu Mahmoud Abbas tare da tsohon Shugaba Yasser Arafat a 2003
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da Falasɗinawa ke neman ƙasashen duniya su amince da ƙasarsu ta kansu, akwai shugabannin siyasa da dama da aka yi a yankin tun daga shekarun 1960.

Akwai muƙamin Shugaban Falasɗinawa, da Shugaban Hukumar Falasɗinawa ta Palestinian Authority, da Shugaban Kwamatin Ƙungiyar 'yanta Falasɗinawa ta Palestine Liberation Organization (PLO), waɗanda ke ƙarƙashin Shugaba Mahmoud Abbas.

An kuma ƙirƙiri muƙamin firaminista kusan shekara 20 da suka wuce, inda Abbas ya zama na farko a muƙamin.

Shugaban PLO

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas kenan a hedikwatar Palestine Liberation Organization a 2011 da ke Ramallah a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas kenan a hedikwatar Palestine Liberation Organization a 2011 da ke Ramallah a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye

An kafa ƙungiyar Palestine Liberation Organization (PLO) a 1964 wadda ke ƙunshe da ɓangarori, da jam'iyyun siyasa, da masu faɗa-a-ji, da ƙungiyoyin farar hula.

Ƙungiyoyin Hamas da Islamic Jihad ne kawai ba su cikin ƙungiyar.

PLO ce aka tsara za ta dinga wakiltar Falasɗinawa a hukumance duk inda suke a duniya, ciki har da tattaunawa irin ta siyasa.

Kwamatin zartarwa na PLO daidai yake da majalisar ministoci a sauran ƙasashen duniya.

Tun daga lokacin ne kuma mutum huɗu ke shugabantar kwamatin: Ahmed Shukeiri, Yahya Hamouda, Yasser Arafat, da Mahmoud Abbas, kuma ana yi wa shugaban kwamatin kallon shugaban ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ɗauki matakin kafa gwamnati a 1993 bayan ƙulla Yarjejeniyar Oslo.

Ƙungiyar ce ke wakiltar Falasɗinawa a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da sauran ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Hani al-Masri, shugaban cibiyar nazari kan harkokin Falasɗinawa ta Palestinian Center for Policy Research and Strategic Studies, ya siffanta ƙungiyar a matsayin "gwamnatin da ba ta da ƙasa".

Jagoran ƙasa

Shugaban PLO Yasser Arafat yana nuna alamun nasara lokacin wani taron majalisar Falasɗinawa a birnin Algiers na Aljeriya a 1988

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban PLO Yasser Arafat yana nuna alamun nasara lokacin wani taron majalisar Falasɗinawa a birnin Algiers na Aljeriya a 1988
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar 15 ga watan Nuwamban 1988 ne shugaban PLO Arafat ya ayyana kafa ƙasar Falasɗinu tare da Binrin Ƙudus a matsayin babban birninta yayin wani jawabi a Aljeriya.

'Yan mintuna bayan haka ne kuma Aljeriya ta ayyana amincewa da ƙasar ta Falasɗinu, wadda a yanzu ƙasashe sama da 145 ne suka amince da ita.

A 1989, kwamatin gudanarwa na PLO ya zaɓi Yasser Arafat a matsayin shugaban ƙasar Falasɗinu.

A 2008, kwamatin ya sake zaɓar Mahmoud Abbas a matsayin shugaban ƙasa.

Shugaban cibiyar Arab World Observatory for Democracy and Elections in the Palestinian Territories, Aref Jaffal, ya ce yana ganin an ayyana muƙamin shugaban ƙasa ne kawai saboda an ayyana kafa ƙasar Falasɗinu.

"Babu ƙasa, saboda haka babu ƙarfin iko," in ji shi. "Ya fi kama da shugaban al'umma ba tare da ƙarfin iko ba. Duk da cewa akwai muƙaman shugaban ƙasa uku, akwai hukumomi biyu wato PA da kuma PLO."

A 2025 ne kuma kwamatin zartarwar ya amince da ƙirƙiro muƙamin mataimakin shugaban kwamatin zartarwa na PLO.

Ya zaɓi shugaban jam'iyyar Fatah Hussein al-Sheikh don hawa muƙamin.

"Babu wanin rubutaccen abu game da ƙarfin ikonsa," a cewar Jafal.

Shugaban hukumar Palestinian Authority

Wani allo da aka rubuta "Hukumar Falasɗinawa" da Larabci da Ingilishi rataye a Hebron da ke yankin Gaɓar Yamma da Kogi Jordan wanda Isra'ila ta mamaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani allo da aka rubuta "Hukumar Falasɗinawa" da Larabci da Ingilishi rataye a Hebron da ke yankin Gaɓar Yamma da Kogi Jordan wanda Isra'ila ta mamaye

A 1993, majalisar Falasɗinawan ta yanke cewa shugaban kwamatin zartarwa na ƙungiyar PLO, Yasser Arafat, shi ne zai zama shugaban hukumar Palestinian National Authority Council.

An gudanar da zaɓe a ranar 20 ga watan Janairu na 1996 domin zaɓar shugaban PA da na 'yanmajalisa, kuma Arafat ya yi nasara.

Bayan mutuwar Arafat ranar 11 ga watan Nuwamban 2004, Rawhi Fattouh, wanda shi ne kakakin majalisa a lokacin, ya zama shugaban ƙasa na PA na tsawon kwana 60.

A ranar 9 ga watan 2005, ɗantakarar Fatah Mahmoud Abbas ya lashe zaɓen shugaban ƙasa kuma ya zama shugaban PA.

PA ce ke da alhakin kula da Yammacin Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Firaministan Falasɗinu

Tsohon Firaministan Falasɗinu Ismail Haniyeh kenan ranar 30 ga watan Mayun 2006

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon Firaministan Falasɗinu Ismail Haniyeh kenan ranar 30 ga watan Mayun 2006

Gwamnatin Falasɗinawa na ƙarƙashin ikon hukumar Palestinian Authority (PA).

Ɓangare ne na masu zartar da shirye-shiryen da majalisa ta amince da shi.

SHugaban hukumar ne ke naɗa firaminista bayan amincewar majalisa, kuma yana da ikon korarsa.

Aan ƙirƙiri muƙamin ne a 2003, kuma Mahmoud Abbas ne ya fara riƙe shi.

'Muna buƙatar rage yawan shugabanni'

Wan mutum riƙe da tutar Falasɗinu a birnin Jenin ranar 10 ga watan Disamban 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wan mutum riƙe da tutar Falasɗinu a birnin Jenin ranar 10 ga watan Disamban 2024

Hani al-Masri na cibiyar Palestinian Center for Policy Research and Strategic Studies (Masarat) ya faɗa wa BBC cewa kwamatin zartarwa ne mafi girman muƙami.

A lokacin guda kuma, gwamnatin Masar na neman a mayar da shugaban PA ya zama mafi ƙarfin faɗa-a-ji.

Jafal ya ce PA ce ke iko da harkokin kuɗi masu yawa, ba PLO ba, wadda kuma ke karɓar kuɗi kai-taye daga ma'aikatar kuɗi.

Majdalani wanda ya riƙe muƙamai da yawa a hukumar PA, ya faɗa wa BBC cewa ikon PA ya samu ne daga ƙungiyar PLO bayan ƙulla Yarjejeniyar Oslo.

Ya ce bai ga wani cin karo ba a muƙaman.

Duk da cewa ikon gwamnatin Falasɗinu ɓangare ne na dokokin PA, ana samun cin karo game da ikon shugaban ƙasa da na firaminista, a cewar Jafal, yana mai cewa babu cikakken bayanin aikin kowane ɓangare.

Jafal na ganin babu buƙatar irin waɗannan muƙaman. "Ya kamata mu rage yawan abubuwan nan domin mu daina ruɗar da kanmu."