Abincin gargajiya da yi wa kare aski kare cikin hotunan Afirka

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

A ranar Litinin, wani mutum ya sanya wa jama'a albarka yayin bikin Hindu na shekara-shekara mai suna 'Thaipoosam Kavady' a birnin Durban, Afirka ta Kudu ...

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin, wani mutum ya sanya wa jama'a albarka yayin bikin Hindu na shekara-shekara mai suna 'Thaipoosam Kavady' a birnin Durban, Afirka ta Kudu ...
Mutane suna soka lemun tsami da furanni a jikinsu ta hanyar amfani da allurai masu tsini da ƙugiya domin nuna sadaukarwa da godiya ga Murugan, wani wani bautar hindu

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, Mutane suna soka lemun tsami da furanni a jikinsu ta hanyar amfani da allurai masu tsini da ƙugiya domin nuna sadaukarwa da godiya ga Murugan, wani wani bautar hindu
Masu ibada wani lokaci suna rawa yayin da ba su cikin hayyacinsu.

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, Masu ibada wani lokaci suna rawa yayin da ba su cikin hayyacinsu.
Masu wasa da babura a lokacin zanga-zangar

Asalin hoton, Abubaker Lubowa / Reuters

Bayanan hoto, A ƙasar Uganda a ranar Litinin, magoya bayan Muhoozi Kainerugaba, ɗan shugaban ƙasar Yoweri Museveni, sun nufi majalisar dokokin ƙasar yayin wata zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa.
Wasu matan Masar biyu ke riƙe da tukwane

Asalin hoton, Khaled Desouki / AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wasu mata biyu ƴan ƙasar Masar suna shirya cuku na gargajiya a wata cibiyar al'umma da ke Giza, ƙasar Masar.
Hoton wani mutum lulluɓe da tutar DR Congo

Asalin hoton, Simon Wohlfahrt / AFP

Bayanan hoto, Wani mutum da ke lulluɓe da tutar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ya halarci wata zanga-zanga da aka yi a ƙasar Beljiyam a ranar Asabar don nuna adawa da faɗan da a ke gwabzawa a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.
Limamin coci yayin da yake addu'a

Asalin hoton, Hardy Bope / AFP

Bayanan hoto, Washegari a DR Congo da kanta, Cardinal Fridolin Ambongo ya yi addu'ar samun zaman lafiya cocin Notre Dame du Congo da ke Kinshasa babban birnin ƙasar.
bikin sabuwar shekarar ƴan China a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Christian Velcich / AFP

Bayanan hoto, Al'ummar ƙasar China da ke Afirka ta Kudu, sun gudanar da bikin sabuwar shekara a birnin Johannesburg a ranar Asabar...
wasu yara mata biyu zaune cikin wani ɗaki

Asalin hoton, Christian Velcich / AFP

Bayanan hoto, Yayin da wasu mata biyu sanye da kayan gargajiya ke zaune a cikin wani dakin tausa a yankin Cyryldene, gundumar ƙasar China.
Sarkin Ogale a Landan

Asalin hoton, Isabel Infantes / Reuters

Bayanan hoto, Sarki Godwin Bebe-Okpabi na Ogale ya halarci wata kotu da ke Landan bayan da suka shigar da ƙara kan kamfanin Shell saboda gurbatar muhalli a Najeriya.
Liktan kare

Asalin hoton, Mohamed Messara / EPA

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wata karya ta sha gyara a wani wurin kula da dabbobi na tafi-da-gidanka a Tunis, ƙasar Tunisiya.