Bikin sabuwar shekara da rantsar da shugaban Ghana cikin hotunan Afirka
Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afrika na wannan makon.

Asalin hoton, EPA
Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa birnin Cape Town a ranar Asabar inda ake bikin sabuwar shekara na Tweede Nuwe Jaar, wani biki mai ban sha'awa na shekara-shekara wanda ya samo asali daga zamanin bautar bayi

Asalin hoton, EPA
A wajen bikin mutane sun yi shiga irin ta masu nishaɗantarwa, ɗauke da kayan kiɗa inda suke rera waƙoƙin shekarun 1800.

Asalin hoton, Esa Alexander / Reuters
...Raye-raye na cikin muhimman abubuwan da ake gudanarwa a lokacin bikin

Asalin hoton, Nipah Dennis / AFP
A ranar Talata, John Mahama ya ɗaga takobin gwamnati bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Ghana a Accra babban birnin ƙasar.

Asalin hoton, Khaled Desouki / AFP
Da sanyin safiyar Alhamis, masu yawon buɗe ido a Masar sun shiga balan-balan a birnin Luxor da ke kudancin kasar.

Asalin hoton, Khaled Desouki / AFP
Ranar Laraba a birnin na Luxor, aka fara baje kolin sabbin abubuwan tarihi na zamanin Sarauniya Hatshepsut da aka gano...

Asalin hoton, Ahmad Hasaballah / Getty Images
An gano sama da tubalan dutse1000 wanda aka yi wa ado.

Asalin hoton, Tony Karumba / AFP
Ƴansanda sun kama wani ɗan ƙasar Kenya a lokacin wata zanga-zangar neman sako masu sukar gwamnati da aka kama a ƙasar, da aka yi ranar Litinin a Nairobi.

Asalin hoton, Marco Longari / AFP
A jamhuriyar Benin, wani sabon mabiyin addinin gargajiya na Kokou - an lullube shi da man ja da aka hada da garin masara, yayin da ake kwarara masa barasa a kansa yayin wani bikin shekara shekara na al'adun Vodun a yankin Ouidah...

Asalin hoton, Marco Longari / AFP
Egungun, akan ce ruhin kakanni ne da suka rasu, kuma yana ziyartar al'umma a lokacin bikin na al'adun Vodun na ƙasar.











