Ko Afirka za ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya?

    • Marubuci, Marina Daras
  • Lokacin karatu: Minti 3

Amurka da China da Rasha ba su cika haɗuwa a teburi ɗaya ba, duk da cewa akwai wasu abubuwan da dama suke haɗuwa a kai.

Dukkansu sun amince nahiyar Afirka ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaro. Amma shin me ya sa har yanzu ba a tabbatar ba?

A kwamitin tsaro na MDD, akwai ƙasashe biyar masu kujerar dindindin wato China da Rasha da Faransa da Birtaniya da Amurka, waɗanda ake kira da P5. Su kaɗai ne mambobin da suke da damar hawa kujerar na-ƙi.

Sauran ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya suna samun damar zama a kwamitin tsaron ne lokaci bayan lokaci, amma ba su da ƙarfin ikon hawa kujerar na-ƙi.

'Tabbatar da tsaron Afirka dole ne'

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce akwai buƙatar gyara.

"Ba za a taɓa yi iya samar da tsaro a duniya ba, ba tare da tabbatar da tsaron Afirka ba," in ji shi.

"Bai dace ba a ce kwamitin tsaro na duniya babu wakilcin nahiyar da ke da sama da mutum biliyan 1, wadda kuma mutanenta ke ƙara hayayyafa, kuma yanzu haka nahiyar ce ke da kashi 28 na ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya."

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta buƙaci "aƙalla kujera biyu ta dindindin" da ƙarfin ikon hawa kujerar na-ƙi, da kuma ƙarin kujera biyar da ba na dindindin ba.

Amma duk da cewa yawancin ƙasashen majalisar sun amince akwai buƙatar Afirka ta samu damar, masanin diflomasiyya a majalisar, Richard Gowan ya ce ya ce ba su shirya ba.

Gowan ya ce gwamnatin Amurka a ƙarƙashin Biden ta bayyana goyon bayanta kan yunƙurin Afirka na samun kujera biyu, amma ba tare da ƙarfin kujerar na-ƙi ba. Amma ya ce Trump ya nuna cewa ya fi son kwamitin a yadda yake, kuma ba ya so ƙasashe masu ƙarfin hawa kujerar na-ƙi su yi yawa.

Waɗanne ƙasashe daga Afirka?

Wata babbar matsalar da ke ci wa Afirka tuwo a ƙwarya ita ce shin wace ƙasa ce ta fi cancantar ɗarewa kujerar guda ɗaya ko biyu a kwamitin?

Ƙasashen da ake bayyanawa daga Afirka su ne Afirka ta Kudu da Najeriya da Kenya da Habasha da Algeriya da Masar, amma har yanzu babu ƙasar da ta fi shigewa gaba wajen nema.

Tarayyar Afirka na da mambobi 55, kuma ana tunanin ƙungiyar ta zama wakiliyar nahiyar, amma Gowan ya ce ƙungiyar tana fama da cikas wajen aikin diflomaiyya.

Ya ce ana samun matsaloli da dama wajen ɗaukar mataki a ƙungiyar, "misali kan matsalar da ta shafi Somalia," in ji shi.

"Masana diflomasiyya ƴan Afirka da ke New York suna tunanin ya fi dacewa su riƙa ɗaukar matakai daban da na takwarorinsu na Tarayyar Afirka saboda suna tunanin China da Amurka ba za su goyi bayan abin da ƙungiyar ke so ba."

A yanzu da aka taru a birnin New York domin taron na Majalisar Ɗinkin Duniya, abin jira a gani shi ne shin Afirka za ta samu kujerar ta dindindin ko kuma kawai za a ci gaba da tafka muhawara ne.