Fifa za ta yi nazari kan yadda ake musayar 'yan wasa bayan shari'ar Lassana Diarra

Asalin hoton, Getty Images
Fifa za ta yi tattaunawa da kwararru a duniya kan sauyin da take son kawo wa a harkokin saye da sayerwar 'yan wasa, bayan hukuncin kotu kan musayar da aka yi wadda aka amince ta karya dokokin Tarayyar Turai.
A farkon wannan watan ne kotun Tarayyar Turai ta yi wani hukunci kan ƙarar tsohon ɗan wasan Chelsea da Arsenal Lassana Diarra, kan abin da ya ce batanci da Fifa ta ja masa.
Hukuncin ya ce, lokacin da za a ɗauki ɗan wasan da wa'adin zamansa a ƙungiya ya ƙare ba kuma a sabunta ba, kungiyoyi za su haɗu wajen biyan tsohuwar ƙungiyar ɗan wasan idan soke kwantaraginsa ta yi ba tare da wani dalili ba.
Diarra ya ce dokar ta daƙile masa 'yancinsa na yawace-yawace bayan soke kwantaraginsa da ƙungiyar Lokomotiv Moscow ta Rasha a 2014, wanda hakan ya karya dokar gasanni.
Kotun ta amince cewa Fifa ta hana Diarra shaidar musayar kuniya ta ITC domin komawa ƙungiyar Charleroi dake Belgium a 2015, wanda hakan ya nuna yadda hakan ya daƙilewa ɗanwasan 'yancinsa na tafiye-tafiye da zai ba shi damar samun wata ƙungiya sabuwa".
Fifa ta ce yanzu za ta bude wani zauren tattaunawa na duniya domin baiwa masu ruwa da tsaki damar faɗin albarkacin bakinsa domin amfani da sabuwar dokar.







