Me ya sa ƴan Shi'a ke jimamin ranar Ashura, kuma me suke yi a ranar?

Lokacin karatu: Minti 4

Jimamin ranar Ashura, abu ne mai muhimmanci ga mabiya aƙidar Shi'a a Iraqi da sauran ƙasashen duniya.

A duk shekara sukan taru domin tunawa da shahadar Imam Husseini jikan annabi Muhammad, wanda aka kashe a kusa da Karbala. Me ƴan Shi'ar ke yi a wannan lokaci?

Tarihi ya nuna cewa Husseini Ibn Ali Ibn Abi Talib ya tashi ne tare da tawagarsa daga Kufa a kan hanyarsu ta zuwa Hijaz domin karɓe ragamar halifancin Musulunci.

A wancan lokaci Yazid bin Mu'awiyah shi ne khalifa bayan rasuwar mahaifinsa Mu'awuya Ibn Abu Sufyan.

Sai dai wakilan Yazid a Basra da Kufa sun tura dakarunsu waɗanda suka tursasa wa Husseini da tawagarsa karkata akala zuwa Karbala.

A can ne aka yi musu ƙawanya, aka hana shi tsallaka kogin Alfuraat, sannan aka kashe shi a yaƙin da aka gwabza.

A lokacin yaƙin an kama mata da yara da yawa, ciki har da ƴar'uwarsa Zainab da ɗansa Ali Zayn al-Abidin, wanda ɗaya ne daga cikin imamai huɗu na Shi'a.

Babban lamari

Kisan da aka yi wa Husseini da tawagarsa da kuma kama iyalansa ya kawo sauyi sosai a cikin mabiya Shi'a. Wannan ne ya sanya ake tunawa da lamarin a duk shekara.

Darussan da wannan lamari ya koyar ya shafi sauran abubuwan da suka biyo baya a tarihin Musulunci a ɓnagren imani da kuma a siyasance.

Wannan jimami da akan yi duk shekara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Muharram na faruwa ne ba a Iraqi kaɗai ba har da duk faɗin duniya inda ake da yawan mabiya aƙidar Shi'a.

Haɗuwar al'ada da imani

A kwana 10 na watan Muharram, akan yi taruka da abubuwa daban-daban domin nuna baƙin ciki da jimamin abubuwan da suka faru. Launin baƙi da ake amfani da shi na nufin alhini, kuma ana sanya tufafi mai tambarin Husseini.

Taruka da tattaki da raba abinci ga mabuƙata na daga cikin muhimman abubuwan da mabiya Shi'a kan yi a lokacin.

Sun yi amannar cewa kisan Husseini ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa imaninsu, inda suke tashi tsaye wajen ƙwatar ƴancinsu.

A wasu wuraren akan gudanar da taruka a fili domin kwatanta abubuwan da suka faru a Karbala, kuma dubun dubatar mutane sukan halarta.

Wasu na kallon lamarin a matsayin ɗaya daga cikin manyan laifuka da aka tafka a tarihi, yadda mutane suka ƙi taimaka wa Husseini a Kufa, wasu kuma ba su bai wa lamarin muhimmanci ba.

A Karbala ne aka fi ganin tasirin tarukan tunawa da kisan Husseini. Sai dai duk da haka ana yin waɗannan taruka a yankuna daban-daban na ƙasar Iraqi da kuma sassan duniya.

Haramta bukukuwan tunawa da kisan Husseini

A lokacin mulkin tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussain, hukumomin ƙasar sun ɗauki matakan dakushe al'umma mabiya aƙidar Shi'a, waɗanda su ne masu rinjaye a ƙasar daga gudanar da bukukuwan.

Sai dai wannan ba shi ne na farko ba a tarihi. A baya an sha haramta wa mabiya Shi'ar gudanar da taruka da bukukuwansu.

Masana tarihi sun ce an sha haramta tarukan Ashura a zaman mulkin Mulukiya na Iraqi.

Sai dai daga baya an dawo da tarukan a lokacin daular Ottoman, sa'ilin da daular wadda ke da cibiya a Istanbul na Turkiyya ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Iran bayan gushewar mulkin Mulukiya.

Amma an samu karo uku da aka yi yunƙurin haramta tarukan na Ashura.

Ra'ayi na siyasa na daga cikin manyan dalilan da suka sanya shugabanni ke ɗaukar matakin taƙaita tattakin, a yunƙurin hana yin amfani da su domin adawar siyasa.

An riƙa amfani da tattakin wajen nuna ƙiyayya ko rashin jituwa da ke tsakanin ɓangarori ko yankuna daban-daban.

A shekarar 2003 lokacin da aka kawar da gwamnatin Saddam Hussain sa'ilin da Amurka da ƙawayenta suka mamaye Iraqi, an samu sauyin lamurran siyasa.

Ƴan Shi'a sun samu muƙamai da yawa na gwamnati, wannan ya sanya aka kawar da manufofin da aka yi amfani da su a baya wajen mayar da su gefe, abin da ya bai wa ƴan Sunni ƙarfi.

Bayan zaɓukan majalisar dokokin Iraqi da aka gudanar, jam'iyyun ƴan Shi'a sun mamaye gwamnati, duk da cewa akwai na Sunni da kuma Kurdawa da su ma suka samu kujeru a gwamnatin.

Tun daga lokacin ne aka ci gaba da gudanar da bukukuwa ba tare da takurawa ba, sai dai irin wadannan taruka sun zama tarkon da masu harin ƙunar bakin wake ke amfani da su wajen kai hari a lokacin da dakarun Amurka ke ƙasar da ma bayan ficewarsu a 2011.