Tsada da ƙarancin abinci sun mamaye Maiduguri bayan ambaliya

Maiduguri
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da mutanen Maiduguri ke cigaba da jimamin ambaliyar ruwa da ta ɗaidaita garin, mazauna birnin sun faɗa cikin halin ƙarancin kayan abinci da tsadarsa.

Bayan ambaliyar, an kwashe dubban mutane zuwa sansanonin wucin gadi, inda suke cigaba da rayuwa hannu baka hannu ƙwarya.

Wakilin BBC Imam Saleh wanda ya je Maiduguri, ya ruwaito yadda al'umma ke buƙatar agaji. A cewarsa, ambaliyar ta malale babbar kasuwar Maiduguri wato 'Monday Market'.

"Kusan dama abin da ke kawo tashin farashi ƙarancin kayan ne, kuma kusan kashi 50 cikin 100 na Maiduguri ambaliyar ta shafa. saboda haka dole ya shafi shaguna da wuraren hada-hada," kamar yadda ya bayyana.

Akan kai kayan agaji sansanonin da mutane ke fakewa, amma abin ba shi isa saboda yawansu. Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya shafi mutum kusan miliyan biyu zuwa yanzu.

Sai dai wani lamarin shi ne, waɗanda ba su je sansanonin ba kuma suka zaɓi cigaba da zama a cikin gari, suna fama da ko dai rashin kayayyakin masarufi ko kuma tsadarsa.

Wani ɗanjarida a Maiduguri Adamu Ali Ngulde ya ce lallai ruwa ya fara ja baya sosai, amma wani wajen da gizo ke saƙa shi ne neman kayan abinci.

"Ko da kuɗinka sai da rabonka," in ji shi. "Wuraren da aka yi ambaliya dama babu kayan abinci, a wuraren da ba a yi ba kuma sun yi ƙaranci sosai ko kuma tsada."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ƙara da cewa komai ya ƙara kuɗi, musamman ma biredi wanda a cewarsa shi ne aka fi amfani da shi yanzu, amma waɗanda za su saya da kuɗinsu ne ke fuskantar ƙalubale.

"Kuma biredin ne ake ci a sansanonin gudun hijira. Ƙungiyoyin sa-kai da ɗaiɗaikun mutane masu hannu da shuni duk sun je gidajen biredi sun sa ana yin biredi ana zuwa ana raba wa al’umma a sansanonin.

"Biredin da za ka samu kafin ambaliyar a naira700 zuwa 800, yanzu ya koma 1,100 zuwa 1,200, wanda kuma ake iya samu a 1,200 yanzu ya koma 1,500 zuwa sama."

Ya ce batun ruwan leda ba a cewa komai, domin ba a samun sa sosai "saboda yawanci an riga an biya kuɗi ana kai wa sansanonin wucin gadi."

Game da sauran kayayyakin buƙata, Ngulde ya ce: "Shinkafa da ake samu kan naira 2,000 ko 2,100, yanzu ta koma tsakanin 2,300 zuwa 2,500."

Ita ma Badiyya Usman, wadda take zaune a Maiduguri ta bayyana wa BBC cewa lallai kayayyak sun ƙara tsada.

A cewarta: "Tun daga ranar Litinin kayayyaki suka fara tsada. Yanzu haka na sayo ƙwai naira 5,200. Kafin ambaliyar kuma 4,500 ne zuwa 4,700. Sannan waɗanda muke tare da su sun sayo sauran kayayyakin masarufi da tsada."

Me ya sa kayan masarufi suka yi tsada?

BBC ta tambaye Ngulde dalilin da ya sa abincin ya yi tsada, kasancewar an san ambaliyar ce ta jawo ƙarancinsa.

"Tsadar ma ambaliyar ce ta jawo. Yawancin kayayyakin nan suna nan a shaguna kafin ambaliyar, babu wani sabon abinci da aka shigo da su Maiduguri," kamar yadda ya bayyana.

Ya ƙara da cewa dankalin Hausa ne kawai ya shigo sabo, "shi ma ba a samu shigo da shi Maduguri ba saboda ambaliyar. Sai aka bar shi a titunan Bulunkutu da sauransu. A can aka tsaya ana kasa dankalin ana sayarwa kan N300 ko N500 ko1,000," inji shi.

Ya ƙara da cewa bayan dankalin babu wani sabon kayan abinci da aka shigo da shi, tsofaffi ne kawai suka ƙara farashi.

'Ko da kuɗinka sai da rabonka'

Ɗanjaridar ya ce ƙarancin kayayyakin masarufin ya fi ɗaga hankali saboda ko da kuɗinka da wahala ka samu abin da kake so.

"Idan ma kana da kuɗin, idan ka je shago sai a ce mai shagon ya rufe ya tafi ceton ƴan'uwansa. Gaskiya waɗanda suke zaune a cikin gari su ma sun shiga cikin ƙunci, saboda wasu na da ƴan kuɗaɗe a hannunsu amma samun kayayyakin da suke buƙata yana wahala."

Ngulde ya ƙara da cewa talauci ya kuma ƙara yawa a tsakanin mutanen, saboda "galibi an ta’allaƙa rayuwar ce a kan sai an fita ake samun abin da za a ci, yanzu kuma ba a fita. An rufe kasuwannci".

"Sannan yawancin tattalin arzikin garin a kusan yanki ɗaya yake. Kasuwar Monday, da Kasuwar Custom, da Kasuwar Gamboru, yawancin masu sana’a a ta can suke zuwa nema, kuma an rufe su. Abin da ke hannunka ya ƙare, kuma ba a fita nema. Dole a shiga damuwa."

Wuraren da ƴan gari suka taimaki kansu

Sai dai ya ce a wasu wuraren an samu sauƙi saboda wasu da ambaliyar ta shafa gidajensu da shagunansu kuma akwai abinci.

"Har ma suna suna cewa sun kyautar da kayan idan matasa za su iya shiga ruwa su kwaso su," acewarsa.

Hakan ya sa matasa suka dinga ƙoƙarin shiga suna kwaso biski, da garin laushi ana raba wa mutane.

Sannan ya ƙara da cewa wasu suna sayar da buhun biski a farashi mai rahusa kan naira 5,000, masu kuɗi suna saya suna rabawa.