Ambaliyar Maiduguri: 'Abin ya fara ne da wasa da wasa'

Asalin hoton, Borno State Government
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumomi ba su fayyace haƙiƙanin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a birnin Maiduguri na jihar Borno ba, amma waɗanda matsalar ta shafa sun ce suna cikin mawuyacin hali.
Hukumomi sun ce ɓallewar madatsar ruwa ta Alau ce ta haddasa ambaliyar da ta fi ƙamari a unguwannin Shehuri, da Gambomi, da Budum, da Bulabulin, da Adamkolo, da Millionaires Quarters, da Monday Market, da Galtumare, da Gwange.
Kazalika, ruwan ya malale fadar mai martaba shehun Borno, da wani ɓangare na Jami'ar Maiuduguri, da wani ɓangare na gidan gwamantin jihar.
Bugu da ƙari, akwai fargabar ruwan ya share wasu dabbobi masu haɗari daga gidan ajiyar namun daji na Maiduguri.
Wannan ce ambaliya mafi muni da jihar ta gani cikin shekara 30 bayan faruwar makamanciyarta lokacin da madatsar ta Alau ta ɓalle a watan Satumban shekarar 1994.
A cewar hukumomi, ɗaya daga cikin makwararar kogin ce ta ɓalle sakamakon tumbatsar da ta yi saboda mamakon ruwan sama ranar Litinin da tsakar dare, inda nan take ruwa ya auka wa unguwannin da ke kusa.
Gwamnatin jihar ta buɗe sansanin Bakassi domin tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa tare da haɗin gwiwar hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa National Emergency Management Agency (Nema).

Asalin hoton, Social Media
'Abu kamar wasa'

Asalin hoton, Nema
Tun a ranar Alhamis gwamnatin jihar ta tabbatar wa mazauna Maiduguri cewa babu wata matsala game da madatsar ruwan yayin da take musanta rahotonnin da ke cewa ta ɓalle.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata sanarwa da fadar gwamnatin ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce tawagar bincike da Gwamna Babagana Umara Zulum ya tura ce ta tabbatar da hakan bayan nazarin da ta yi a ranar 5 ga watan Satumba.
"Da yake yi wa sakataren gwamnati bayani, Injiniya Mohammed Zannah ya bayyana cewa duk da ƙaruwar ruwa a kogin lamarin ba wata barazana ba ce ga birnin, yana mai cewa an ɗauki dukkan matakan da suka dace don shawo kan lamarin," a cewar sanarwar.
Sai dai wani mazaunin birnin na Maiduguri ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya fara ne da wasa da wasa.
"Tun ana ganin abin kamar wasa, mutane suna ɗan ɗaukar kayansu kaɗan-kaɗan, daga ƙarshe kowa ya ga ba zai iya ba kuma aka fita," in ji mutumin da bai bayyana sunansa ba.
"Yanzu haka ina tsaye a bakin babban gidan yari na Maiduguri, ga shi nan ruwa iya kallonka kuma sai ƙaruwa yake yi. Motoci duk sun maƙale. Wasu ma da rigunan barcinsu suka fita kan tituna."
Wani mai suna Maina Bukar da ke zaune a Kasuwar Shanu ya ce saman gini aka ɗaɗɗora mata da yara saboda ambaliyar.
"A yankinmu babu wani wuri [ko'ina ya shafe da ruwa] sai shagunan da gwamnati ta gina, sai kuma masallacin Girimami kuma mata da yara ne a ciki," a cewarsa.
"Mafi yawa sun fita daga wurin yanzu bayan mun samu wasu gidajen da ke da dakin, inda mata da yaran suka hahhau, mu kuma maza mun fita. Amma dai babu batun raguwa sai dai kawai Allah ya sawwaƙe mana."
Shi kuma Sayyadi Ibrahim ya ce gidaje sun fara rushewa a yankinsu.
"Ruwan nan ya riga ya cinye mu fiye da yadda muke tunani ta yadda har wasu gidaje sun fara rushewa," a cewarsa.
"Muna buƙatar tallafin abinci da magunguna da gidajen sauro daga gwamnati, sabod idan ka ga dubban mutanen da ke fitowa daga Railway Quaters ba mu da abin cewa sai dai kawai inna lillahi wa inna ilaihi raji'un."
Madatsar ruwan Alau da ta kwararo ruwa

Asalin hoton, Borno State Government
An gina madatsar ruwa ta Alau a yankin ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno da ke da nisan kilomita 36 daga Maiduguri a shekarar 1986.
Kogin na ɗaya daga cikin kogunan da ke kwaranyewa cikin Tafkin Chadi bayan Ngadda da kuma Yedzeram, wanda shi ne mafi girma.
Babbar manufar gina Alau ita ce samar wa manoman rani ruwa, da kuma rage haɗarin ambaliyar ta hanyar tara ruwan da ya kai yawan cubic meter miliyan 112 (lita biliyan 112).
Daga baya kuma, gwamnati kan samar wa mazauna ƙananan hukumomin Maiduguri da Jere ruwan sha daga kogin.
Lokaci na ƙarshe da madatsar ta ɓalle kafin yanzu shi ne a 2012 sakamakon mamakon ruwan sama, amma hakan ta faru a 1992 da 1994.











