'Za a iya rage karfin ambaliyar ruwa ta yadda ba za ta cutar da mutane ba'

Tsawon kwanaki da aka shafe ana ruwan sama ta haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Jigawa da Bauchi da ke Nijeriya

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Ambaliyar ruwa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar lura da al'amuran ruwa ta Nijeriya, NIHSA, ta ce ana iya yin amfani da ambaliyar wajen samar da hasken wutar lantarki da biyan bukatun harkar noma da dai sauransu.

Idan har aka alkinta ruwan da ke malala cikin gonaki da garuruwa yana haddasa ta'adi.

Shugaban hukumar ta NIHSA, Umar Ibrahim Muhammad ya shaidawa BBC cewa a mafi yawan lokuta ruwan sama ne ke janyo ambaliyar ruwa:

‘’Kamar yanzu a cikin sati daya da ya wuce, yawan ruwan saman da aka yi a jihohi irinsu Jigawa da Bauchi da Kano, kwanakin da aka yi ana ruwa shi ya haddasa ambaliyar ruwa sosai’’, in ji shi.

Malam Umar Ibrahim Muhammad ya ce duk da cewa ana kallon ambaliyar ruwa a matsayin jidali amma za a iya sabunta ta:

‘’ Kasashen da suka ci gaba, sun dauko tsari wanda suka iya sabunta yanayin, ta yadda a maimakon cutarsu da su da ta ke yi sai su ka mayar da ita abinda yake amfanar da su''

‘’A nan su e samar da wutar lantarki, su ka bunkasa harkar noman rani, su ka maida wani yanayi wanda mutane za su rika zuwa daga kasashe su na biyan kudi suna Kallon yadda yanayin ruwan yake’’, in ji shi

Masanin ya ce a maimakon ruwan ya zo ya yi ta ta'adi ana kirkiro abinda ake kiransu lockup dams watau dam- dam kuma ko wacce daga ciki ta na da abinda za ta yi

‘’Misali kamar mutane da ke bakin ruwa sai a matsar da su dan ciki kadan sannan kuma ayi wata hanyar ruwa wadda za ta je wurin da jama’a suke watau a tsare ta yadda ba za ta cutar da su ba kuma zai ba su damar noman rani da kamun kifi’’

Ruwan da ke zuwa da ambaliya za a rage karfin shi kafin ya kai wurin da alumma suke ko garuruwa kamar yadda Umar Ibrahim Muhammad ya bayyana:

‘’Idan aka tara ruwa, sai ayi masa magudana wadda za ta rika juya injuna da karfi , ita kuma ke bada wuta’’

Ya kuma ce tsari ne da za a iya amfani da shi a Nijeriya

‘’Shi wannan tsari zai samar da yadda za a magance matsalolin da ambaliyar ruwa ta ke zuwa da su na tsawon lokaci’’, in ji shi.