'Kusan yara miliyan uku ne ke fama da tamowa a Borno da Adamawa da Yobe'

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matsalar ta fi shafar yara 'yan ƙasa da shekara biyar
Lokacin karatu: Minti 3

Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya nuna damuwa kan matsalar rashin abinci mai gina jiki ko tamowa da ta shafi ƙananan yara a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Unicef ya yi kiran ɗaukar matakin gaggawa kan matsalar, tare da jaddada muhimmancin taimaka wa yaran da tamowar ta shafa a waɗannan jihohi.

Asusun ya ce jihohin Borno da Adamawa da Yobe na cikin na gaba-gaba da matsalar tamowa ta fi ƙamari, inda ya ce matsalar ta shafi kimanin yara miliyan 3.8 a yankin.

Aminu Usman Dan Zomo, wani jami’i a Unicef kuma ƙwarare kan abinci mai gina jiki ya shaida wa BBC cewa akwai dalilai da dama da suka haddasa wannan matsala:

"Akwai matsin tattalin arziki a wannan yanayi da mu ke ciki, akwai ƙaruwar rashin samun abinci ga mutane da dama a wannan ƙasa tamu".

''A wannan yanki namu mun fuskanci ƙalubale na faɗa tsakanin gwamnati da mayaƙan Boko Haram, kuma akwai rashin sanin irin abincin da za a haɗa wa yaro da kuma lokacin da ya kamata a haɗa masa,'' in ji shi.

Unicef ya ce akwai wasu hanyoyi da ya kamata a bi domin a inganta shayarwa ga yaro.

"Misali da zarar an haifi yaro ya kamata a ce an sa shi a nono kafin awa guda, ko kuma tsakanin haihuwarsa zuwa awa guda a tabbatar an sa shi a nono domin ya sha ruwan nonon da ake kira Cholestrol mai ruwan ɗorawa".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Asusun ya yi gargaɗin cewa muddin ba a ɗauki ƙwararan matakan da suka dace ba , akwai fargabar yara da mata miliyan 1.1 za su iya kamuwa da tamowa a wannan shekara. Sannan ya ce akwai mata masu shayarwa 206, 779 da ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.

Unicef ya kuma bayyana irin abinci da ya dace a samar wa yaran da suka kamu da tamowar don kauce wa barazanar mutuwa.

"Yara waɗanda suka kamu da tamowa sun fi haɗarin mutuwa kamar da kashi 11 cikin 100 a kan yaran da suke da lafiya".

Asusun na Unicef ya ce akwai buƙatar ganin an ɗauki matakan magance wannan cuta ta tamowa tare da maida hankali wajan gano ko zaƙulo yara daga cikin al'umma masu fama da wannan lalura.

Asusun ya ce ya naɗa cibiyoyin karɓar magani fiye da 700 a jihohin uku, sannan ya yi kira a riƙa bai wa yara abinci mai gina jiki da ya ƙunshi nau'in abinci mai ƙara kuzari, wato Carbohydrate da mai gina jiki, wato protein, kamar wake da nama da kifi da sauransu.

Asusun ya ce matsalar ta fi shafar yara 'yan ƙasa da shekara biyar, amma a cikinsu 'yan wata 6 zuwa 24 ne suka fi kamuwa da lalurar.

Ya ce tun cikin shekara biyu da suka gabata ya fara gargadi game da yiwuwar fuskantar matsalar tamowa a Najerya saboda matsalolin tsaro da talauci da suka haifar da ƙarancin abinci. Ko a watan Mayun da ya gabata Majalisa Dinkin Duniya da gwamnatin Najeriya sun yi kiran buƙatar dala miliyan 306 domin magance matsalar tamowa a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.