Chelsea na son Toney, Lewin na daukar hankalin New Castle da Man U

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ivan Toney
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na son dauko dan wasan Ingila mai taka leda a Brentford Ivan Toney mai shekara 28. Ko da ya ke Blues ba za ta iya gogaggaya da makudan kudaden da kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya ta zuba a tayin dan wasan ba.(Sky Sports)

An yi kiyasin Toney zai dinga daukar albashin fam miliyan 400 a kowanne mako idan ya koma Pro League din Saudiyya. (Mail)

Newcastle da Manchester United na son dan wasan gaba na Ingila Dominic Calvert-Lewin, 27, wanda zai kammala kwantiraginsa da kungiyar Everton a kaka mai zuwa. (Football Insider)

Liverpool na aiki tukuru domin kammala batun sayan dan wasan gaba na Italiya mai taka leda a Juventus Federico Chiesa, mai shekara 26, kafin a rufe kasuwar musayar yan wasa a ranar Juma'a. (Athletic - subscription required)

Ana sa ran dan wasan Lyon kuma na tsakiyar Belgium Orel Mangala, 26, zai yi gwajin lafiya da kungiyar Everton, da ake hasasshen zai koma taka leda kulub din zaman bashi, kafin wa'adin rufe kasuwar musayar 'yan kwallo ya cika. (Sky Sports)

Leicester na gab da kammala yarjejeniyar dauko dan wasan tsakiya na Morocco mai taka leda a Genk Bilal El Khannouss, mai shekara 20, kan kudi kusan fam miliyan 20. (Daily Telegraph - subscription required)

Nottingham Forest na son dan wasan Ajax, kuma na gaban Netherland Brian Brobbey, 22, kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa. (Mirror)

Chelsea na son maye gurbin dan wasan Najeriya mai taka leda a Nepoli Victor Osimhen, da dan wasan gaba na Colombia mai taka leda a Aston Villa John Duran, mai shekara 20, a daidai lokacin da dan wasan Najeriyar mai shekara 25 ke shirin barin kungiyar. (Givemesport)

Roma ta bude kasuwar sayar da dan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, 26, kuma tuni kungiyar West Ham ta fara nuna sha'awa kan dan wasan. (Football Insider)