Mutumin da tsoron Allah ya shige shi bayan yin ido-biyu da mutuwa

    • Marubuci, Vishva Samani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

"Ni magini ne da ke fafutikar neman rufin asiri, kuɗi ya kusa ƙare min kuma ana shirin fitar da ni daga gidan da nake haya."

David Ditchfield mai shekara 46 riƙaƙƙen mashayin giya ne. A shekarar 2006 ya kasance a yana zama a birnin Landan, kuma rayuwarsa ba ta tafi yadda ya kamata ba.

A wannan lokaci, David ya je don zama tare da 'yar uwarsa a yankin Cambridge.

Wata abokiyarsa ce ta kawo ziyara kuma David ya je yi mata rakiya a lokacin da za ta koma, inda ya kai ta tashar jirgin ƙasa.

A lokacin da jirgin zai tashi sai ƙofar jirgi ta maƙalo rigarsa.

Jirgin ya ja shi, inda ya faɗa ƙasan jirgin aka yi ta hajijiya da shi.

A ƙarshe mutumin ya tsira da munanan raunuka, ciki har da wanda ya samu a hannunsa.

A wannan lokaci an garzaya da shi asibiti inda aka yi masa tiyata.

Sai dai kafin a isa asibiti, David ya tsinci kansa cikin wani yanayi na ba-zata wanda bai taɓa samun kansa a cikin irin sa ba.

"Na bar duk wani abu da ke faruwa a asibitin, na bar duk raɗaɗin da nake ji a jikina, inda na tsinci kaina a wani wuri mai cike da nutsuwa," in ji shi.

“Lokacin da na ɗaga ido, sai ga wani haske guda uku masu ƙarfi, hasken ya dangana da jikina, sai na ji a hankali hasken yana tafiya a jikina gaba-ɗaya yana warkar da ni."

David ya kuma ji tamkar wasu mala’iku a tare da shi. "Na ji suna warkar da duk wasu raunukan da ke jikina kuma suna cire duk wani nau'in cutarwa a rayuwata, suna gangarowa cikin ruhina.

“Na ji na zama cikakke a karon farko."

Amma sashe na ƙarshe na abin da David ya fuskanta ne ya fi buɗe masa ido.

Ya kwatanta yadda ya ji shi a sararin subhana cikin tsakiyar taurari, sannan daga nesa ga wani farin rami mai haske.

"Ina jin kowane tsokar halittar jikina tana kaɗawa daga wannan babban rami mai farin haske. Na san a wannan lokaci ina kallon tushen dukkan halitta ne. Wannan wani abu ne da ya fi karfin kowa a cikin siffar wannan babban rami na farin haske.

Na yi farin ciki sosai."

Tasirin wannan hali da David ya shiga ya kasance na nan take da kuma na tsawon lokaci.

Ya ce yana ci gaba da samun gamsuwa a zuciyarsa tare kuma da jin cewa akwai wani abu da yake tasiri a rayuwarsa.

Yanzu ya ci gaba da amfani da hannunsa kuma ba ya tsoron mutuwa.

Duk da cewa ba shi da wani gogewa a baya, a yanzu David ya samu ƙwarewa a fannin tsara waƙa sannan ya iya zana hoton duk irin abubuwan da suka faru da shi.

Sai dai duk da haka, David ba ya ɗaukar wannan lamari da ya faru da shi a matsayin mai alaƙa da wani addini, ya gwammace kawai ya kwatanta kansa a matsayin wanda ya koma ga Allah.

Samun kai

Dakta Steve Taylor kwararre ne a fannin nazarin abin da ke faruwa a cikin zukata da kuma halayyar ɗan'adam, wanda ke nazari kan alaƙar da ke tsakanin tsananin wahalar da ke sa mutum ya koma ga Allah, wanda ba kowa ne ke iya fahimta ba.

Ya ce abin da ya faru ga David lamari ne da ya fara zama ruwan dare, inda a yanzu akan samu mutane da dama waɗanda ke cewa sun zama masu tsoron Allah sanadiyyar hakan.

"Lokacin da mutum ya shiga wani yanayin da ya kusa mutuwa, abu ne mai matukar tasiri, wanda ya sha bamban da irin abubuwan da muka saba gani a zahirin rayuwa, ta yadda zai yi wahala mutum ya koma yadda yake a baya, har zuwa ƙarshen rayuwarsa.”

"Yawanci yakan faru ne ga mutanen da suke shagala a rayuwar duniya, kuma ko da bayan sun tsinci kansu cikin irin wannan hali ba lallai ne su zama masu bin addini ba," in ji Dakta Taylor, babban malami a Jami'ar Leeds Beckett.

Ya ce wasu na fassara irin waɗannan abubuwan ta fannin addini, to amma mafi akasari ba su alaƙanta kansu da wani addini , sai dai su ɗauki wani ra’ayin daban.

Bayanan kimiyya mafiya shahara kan shiga halin yin ido-da-ido da mutuwa sun nuna cewa mutum kan samu kansa a cikin irin wannan yanayi ne a lokacin da aka samu katsewar iska zuwa cikin kwakwalwarsa, lokacin da mutum ke gab da mutuwa.

Sai dai Dakta Taylor ya ce har yanzu ba a kai matsaya ba game da wannan bincike kuma babu wani cikakken bayani a kimiyyance kan lamarin.

Ya kuma bayyana gurguwar fassarar da akan yi kan irin wannan lamari domin sun saɓa wa abin da kimiyya ya sani na zahiri.

Dakta Taylor ya ce “Irin wannan abu na nuna cewa da alama ruhi ba abu ne da ke cikin kwakwalwa ba, kuma akwai yiwuwar ruhin na iya rayuwa ko da gangar jiki ta mutu.”

Gigi Gigi Strehler tauraruwar fim ce a arewacin London, wadda a shekarar 2014 ta kafa ƙungiyar 'waɗanda suka ga mutuwa ƙuru-ƙuru a Birtaniya bayan da ta kusa rasuwa a wani asibiti.

"Na tsinci kaina a wani sarari, maimakon yadda wasu ke cewa sun ga rami mai haske. Don haka sai na kasance a wani wuri da babu komai kuma babu kowa. Babu komai sai natsuwa da kwanciyar hankali.”

"Wancan wurin ya fi kama da zahiri idan ka kwatanta da wannan duniyar tamu wadda take kamar mafarki ce. " in ji Gigi.

Bayan abin da ya faru da ita, ta samu sauye-sauye a rayuwarta, kamar fahimtar ilimin yadda lamurra suka samo asali.

Hakan ya sa ta nemi amsoshi daga manyan addini tsawon shekaru da dama, da kuma wasu rassa na sufi.

Amma babu wanda ya gamsar da ita, kuma Gigi yanzu tana da kwakwanto game da addini.

"Halin da na shiga ya nuna min cewa wanzuwarmu ta zarce duk wani bayani da ɗan’adam ya sani. Amma na yi imani cewa dukkanmu muna da wani abu da ya haɗe mu baki daya."

David Ditchfield yana da irin wannan ra’ayin. Yana da zurfin tunani sannan yana mutunta addinai, amma shi karan kansa ba ya da addini.

Dakta Steve Taylor ya ci gaba da sha'awar bincike kan abubuwan da David da Gigi suka bayyana cewa sun gani, amma duk da haka ya yarda cewa lamarinsu abu ne da zai yi wahalar fahimta ga wasu mutane.

"Muna ganin kanmu a ‘yan’adam waɗanda muke iya yin bayanin kan abubuwan da ke faruwa na zahiri da kuma abubuwan da suka faru da mu. To amma akwai wasu abubuwan ban mamaki waɗanda ba dole ne mu iya fahimtarsu ba".