Man Utd za ta fara tattaunawa kan Neves, Ajax da Juventus na gogayya kan Henderson

Jordan Henderson

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na fatan fara tattaunawa da Benfica nan da ƴan makonni kan cinikin matashin ɗan wasan tsakiya na Portugal Joao Neves. (Mirror)

Ajax na ganin tana dab da cimma yarjejeniyar karɓar aron tsohon ɗan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson daga Al-Ettifaq ta Saudiyya. (Mirror)

Amma kuma Juventus ma na son Henderson kuma ƙungiyar na da ƙwarin gwiwar daukar tsohon kyaftin ɗin na Liverpool tsawon wata shida a farko kafin kuma su saye shi gaba ɗaya nan gaba. (Gazzetto dello Sport)

Kamfanin zuba jari na Amurka na 777 Partners na ganin cewa da wuya ya yi nasarar sayen Everton a cinikin da tuni hukumar gasar Premier ta yarda da shi. (Football Insider)

Har yanzu Sevilla na da ƙwarin gwiwar karɓar aron ɗan wasan tsakiya na Tunisia Hannibal Mejbri kodayake Manchester United za ta fi son matashin mai shekara 20 ya tafi Everton. (Revolo)

Fulham na fuskantar gogayya daga Porto kan sayen ɗan bayan Atletico Madrid Caglar Soyuncu, na Turkiyya. (A Bola daga Sport Witness)

Crystal Palace na fatan kammala cinikin fam miliyan 10 na ɗan bayan Genk Daniel Munoz, na Colombia. (Sun)

Juventus ta bi layin Napoli da Galatasaray a gwagwarmayar neman aron ɗan wasan tsakiya na Nottingham Forest Orel Mangala na Belgium. (Sky)

Sevilla ta cimma yarjejeniyar sayen matashin ɗan gaban Manchester United Mateo Mejia na Colombia. (Fabrizio Romano)

Besiktas ta yi watsi ta bukatar Wolves ta neman sayen matashin ɗan gabanta na Turkiyya Semih Kılıcsoy mai shekara 18. (Haberturk)

Chelsea za ta yi ƙoƙarin sayen matashin ɗan wasan gaba na gefe na Brazil, Estevao Willian mai shekara 17 da ke Palmeiras, a kan yuro miliyan 60.

Fulham da Burnley na sha'awar sayen ɗan wasan bayan Strasbourg Gerzino Nyamsi, ɗan Faransa. (Football Insider)

Jesse Lingard ya kori wakilinsa, yayin da yake fafutukar neman sabuwar ƙungiya bayan barinsa Nottingham Forest. (Sky Sports)