Newcastle za ta ƙyale Guimaraes ya tafi, Ajax na son Henderson

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle a shirye take ta ƙyale ɗan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26, ya koma Barcelona ko Real Madrid kan kasa da fam miliyan 100 a wannan kaka. (Football Transfers)
Manchester United ta kwaɗaitu da ɗan wasan baya a Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, amma ba dole ta biya Nice kusan fam miliyan 52 domin sayensa ba. (Caught Offside)
United da Chelsea na son ɗan wasan Sweden mai shekara 16 da ke taka leda a AIK, Jonah Kusi-Asare. Ita ma Bayern Munich ta nuna zawacinta. (HITC)
United ta soma shirya yada za ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan nan mai shekara 18 daga Belgium Arthur Vermeeren da ke take leda a Royal Antwerp. (Football Insider)
Juventus ta tattauna da ɗan wasan Ingila mai shekara 33, Jordan Henderson, kan dawo wa wurinta zaman aro daga Al-Ettifaq. (Gianluca Di Marzio - in Italian)
Ajax ta matsa kaimi wajen sayen ɗan wasan Henderson da Ingila da ke taka leda a Saudiyya. A karshen wannan makon take shirin tuntubar ƙungiyarsa.(Standard)
Ɗan wasan tsakiya a Chelsea da Ingila mai shekara 21, Cole Palmer, ya tambaye kocin Manchester City, Pep Guardiola ko zai iya tafiya zaman aro. Sai dai an faɗa ma sa cewa ko ya zauna ko a sayar da shi. (Mail)
Chelsea ba za ta yarda ɗan wasanta na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 23, ya bar ƙungiyar ba a wannan watan yayin da Tottenham ke nuna zawarcinta a kansa. (Sun)
Spurs na duba yiwuwar dawo da ɗan wasanta na Faransa da ke zaman aro a Galatasaray, Tanguy Ndombele, mai shekara 27, saboda rashin tabbas da take fuskanta a kan Gallagher. (Football Transfers)
Za a bukaci kuɗaɗe masu yawa kan ɗan wasan Brazil Joao Gomes, mai shekara 22, kafin Wolves ta sake shi a watan Janairu, yayinda ake jita-jitar Tottenham na zawarcinsa. (Mirror)
Napoli ta miƙa tayinta kan ɗan wasan tsakiya a Bournemouth da Ivory Coast Hamed Traore, mai shekara 23. (Fabrizio Romano)
Ana tattaunawa da tsohon kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer kan zama sabon kocin tawagar Sweden. (Fotboll Skanalen - in Swedish)










