Ivory Coast ta fara gasar cin kofin Afirka da ƙafar dama

Asalin hoton, Getty Images
Mai Masukin baki, Ivory Cost ta fara da cin Guinea - Bissau 2-0 a wasan farko a rukunin farko ranar Asabar a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Tun kan fara wasan an fara da bikin bude gasar karo ta 34 karo na biyu da Ivory Coast ke karbar bakuncin babbar gasar tamaula ta Afirka.
Ivory Coast mai rike da kofin Afirka biyu ta yi bikin bude labulen wasannin bana da raye-raye da kada-kade daga baya aka share fili, domin take leda.
Mai masaukin bakin ta fara cin kwallo ta hannun Seko Fofana a minti na hudu da fara wasan, haka suka je hutu Ivory Coast tana da kwallo daya.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Ivory Coast ta kara na biyu ta hannun Jean-Philippe Krasso.
Hakan ya sa mai masaukin baki ta ke mataki na daya a rukunin farko da maki uku da kuma kwallaye biyu a raga.
Ivory Coast tana da kofin nahiyar Afirka karo biyu da ta dauka a 1992 da kuma 2015 ta kuma zo ta biyu 2006 da kuma 2012.
Ranar Lahadi ne Najeriya za ta kara da Equatorial Guinea a wasan farko a rukunin farko.
Wannan shi ne karon farko da Super Eagles za ta kece raini da Equatorial Guinea a gasar cin kofin Afirka.
Super Eagles ta yi rashin wasu fitattun 'yan wasa da suka ji rauni da suka hada da Umar Sadiq da Victor Boniface da kuma Wilfred Ndidi.










