An dakatar da Pogba kan zargin shan abubuwan ƙara kuzari

An dakatar da dan wasan Juventus, Paul Pogba kan zargin karya dokar shan abubuwan kara kuzari ga ƴan wasa.

Hukumar hana shan abubuwan kara kuzarin wasa ta Italiya (Nado) ta ce ta samu wani sinadari fiye da ƙima a jikin Pogba, bayan tashi daga karawar da Juve ta ci Udinese 3-0 ranar 20 ga watan Agusta.

Dan kwallon na tawagar Faransa, mai shekara 30 ya yi zaman benci a karawar, amma aka zabo shi cikin jerin 'yan wasan da aka gwada bayan karawar.

Idan aka samu Pogba da laifi za a iya dakatar da shi shekara biyu zuwa hudu.

Juventus ta fitar da sanarwa cewar ''Rana ta yau 11 ga watan Satumbar 2023, ta samu umarnin dakatar da Pogba daga hukumar kula da hana shan abubuwan kara kuzarin wasa, bayan samun sakamakon gwaji da aka yi masa ranar 20 ga watan Agustan 2023.

An bai wa Pogba nan da kwana uku, domin ya kare kansa kan zargin da ake yi masa.

Juventus ta sake daukar Pogba kan kwantiragin kaka hudu a Yulin 2022, bayan da ya kammala kwantiraginsa da Manchester United.

Sai dai ttun bayan da Pogba ya koma birnin Turin da taka leda yake ta fama da jinya da raunin da ya hana shi zuwa gasar cin kofin duniya a Qatar.

Minti 51 jimilla ya buga wa Juventus a bana, shi ne a fafatawa da Bologna da kuma Empoli.

A bara minti 108 ya yi a karawa shida a Serie A, idan ka hada da gasar Europa League da ya buga da minti 11 a Coppa Italia - ya hada minti 162 jimilla ba tare da cin kwallo ba.