Antony ba zai koma United ba domin zai kalubalanci zargin cin zarafi

Dan wasan Manchester United, Antony ya amince ba zai koma Old Trafford ba, domin ya samu damar kalubalantar zargin cin zarafi da ake yi masa.

Ya kamata dan wasan mai shekara 23 ya koma United ranar Litinin, bayan da Brazil ta ajiye shi a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da ta kara da Bolivia da kuma Peru.

United ta sanar cewar ta bai wa dan kwallon damar tsayawa, domin ya fuskanci zargin da ake masa.

Antony ya musanta dukkan zargin da ake masa..

Tuni 'yan sanda suka fara bincike, bayan da aka shigar da kara kan zargin ya ci zarafin tsohuwar budurwarsa.

Haka kuma zai kara fuskantar wani zargin da wata mata ta yi masa a wata hira da kafar talabijin a Brazil.

Antony ya halarci wata hira a gidan talabijin a Brazil ranar Juma'a, inda ya ce ''Ban taɓa cin zarafi wata mace ba'' ya ƙara da cewar ''gaskiya za ta yi halinta''.

Ya kuma fitar da wata sanarwa ranar Lahadi cewar ''United ta amince min na tsaya na fuskanci dukkan zargin da ake yi min kafin na koma Old Trafford.''

Ana zargin Antony da cin zarafin tsohuwar budurwarsa, Gabriela Cavallin da cewar ya yi mata gware a ka a wani otal a Manchester ranar 15 ga watan Janairu, wadda ta ji raunin da likitoci suka yi mata aiki.

Ta kuma yi zargin ya naushe ta a kirji da ta kai ta ji ciwon da likitoci suka yi mata tiyata.

Ita kuwa Ingrid Lana, mai shekara 33, mai aikin banki ta yi zargin Antony ya tureta da ta kai ta bugi bango a gidansa a Manchester a Oktoban 2022 a wani faifan bidiyo da gidan talabijin a Brazil ya saka.

Dukkan 'yan sandan Greater Manchester Police da na birnin Sao Paulo Police na binciken lamarin..

Antony bai buga wa Brazil wasan da ta buga da Bolivia da Peru ba, bayan da hukumar kwallon kafar ta ce ta ajiye shi, bayan da ake zarginsa da cin zarafi.