Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pogba zai yi ritaya bayan an ci amanarsa
Paul Pogba ya ce yana duba yiwuwar yin ritaya daga taka leda, bayan ya zargi ɗan'uwansa, Mathias da haɗa baki da gugun 'yan ta'adda, inda suka dinga yi masa barazana da karɓar kuɗaɗensa.
Ɗan ƙwallon Juventus, mai shekara 30 ya shigar da ƙorafi ga masu shigar da ƙara a birnin Turin cikin watan Yulin 2022, inda ya ce an buƙaci ya biya sama da fam miliyan 11.
An tsare ɗan'uwan Pogba, Mathias Pogba a watan Satumban 2022 daga baya aka sake shi a watan Disamba.
Mai shekara 33, ya musanta zargin da ake yi masa.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa a Al Jazeera, kan yadda batun ya shafi rayuwarsa, Pogba ya ce ''Duk abin da ya haɗa da kuɗi to ka yi taka-tsantsan. Kuɗi na sauya mutane. Zai iya tarwatsa 'yan gida ɗaya, zai iya haɗa yaƙi.
''Wani lokaci nakan yi tunani, ba na son na ƙara samun kuɗi. Kawai zan ji ba na son ci gaba da taka leda, kawai ina jin na koma mutum kamar kowa, yadda za a kaunace ni, ko ni wane ne ba don fice ko kuɗin da nake da shi.
Masu shigar da ƙara a Faransa sun fara ɗaukar mataki na shari'a a watan Satumba, wata biyu tsakani bayan Gasar cin Kofin Duniya a 2018, lokacin da Pogba ya shigar da ƙorafi.
Mai shigar da ƙara a birnin Paris, Laure Beccauau ta ce cikin binciken da suke yi, akwai batun cin amana da yaudara da haɗa kai da gungun 'yan ta'adda da sace mutum don biyan kuɗin fansa da haɗa baki don aikata laifi.
Bayan tsare Mathias a watan Satumba, lauyansa Yassine Bouzrou ya ce ɗan'uwan Pogba bai aikata laifin komai ba.
Pogba ya koma Juventus, bayan ƙarewar yarjejeniyarsa a Manchester United ƙarshen kakar 2022.
Mathias shi ma, ƙwararren ɗan ƙwallo ne, wanda ya buga wa tawagar Guinea da wasu ƙungiyoyi a Turai da suka haɗar da Crewe da Wrexham da Crawley da kuma Partick Thistle a Burtaniya.