Tinubu ya bayar da wa'adin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ba wa hukumomin tsaron kasar wa'adin kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta nan da ƙarshen shekarar nan ta 2025.

Ministan Tsaron kasar, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya shaida wa BBC hakan ya ce, hukuomi sun dukufa sosai domin tabbatar da hakan.

Ya ce: "Ya bada umarni kan cewa duk abin da ake ciki na matsalar tsaro a Najeriya baki ɗaya ta ƙare zuwa ƙarshen wannan shekarar (2025)".

Najeriya na fama da matsalolin tsaro ta fannoni da dama - Boko Haram ta shafe sama da shekara 10 tana kashe-kashe a arewa maso gabashin ƙasar; Matsalar ƴan fashin daji ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a arewa maso yammacin ƙasar, sai kuma rikicin manoma da makiyaya da ya yi katutu a arewa ta tsakiya.

A baya-bayan nan wasu munanan hare-hare da aka kai a jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiya ya yi sanadin rayukan kimanin mutum 100.

Haka nan a baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram sun tsananta kai hare-hare kan sojoji da kuma fararen hula, lamarin da ya kai ga cewa gwamnan jihar Borno - cibiyar rikicin Boko Haram - Babagana Zulum ya yi iƙirarin cewa mayaƙan na ƙwace yankuna a jihar.

Gwamnatin ƙasar na iƙirarin cewa tana bakin ƙoƙarinta a kan lamarin, sai dai har yanzu kashe-kashen ba su kau ba.

A tattaunawar tasa da BBC, Badaru Abubakar ya ce hukumomin tsaron ƙasar sun fara shirye-shiryen ganin sun aiwatar da umarnin shugaban ƙasar.

''Ana tsare-tsare da yawa, kusan an gaggano matsalolin, kuma ana aiki a kansu, kuma da yardar Ubangaji za a samu sauki in shaa Allahu,'' in ji Badaru.

...
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ministan ya ce daga cikin irin kokarin da suke yi na tabbatar da inganta tsaron kasar ya ce idan aka yi la'akari da yadda girman matsalar tsaron yake a baya za a ga sauyi sosai a bangarori da dama na kasar wadanda a baya suke cikin mawuyacin hali.

Ya yi nuni da hakan ne ganin yadda a baya hukumomin kasar kan bayyana irin kwarin gwiwarsu game da matakan da suke cewa suna dauka na shawo kan matsalar a lokuta da dama inda kuma suyke cewa suna samun nasara a yakin da suke yi da matsalar tsaron.

''Duk wanda zai mana adalci a dan tsakanin nan wata shida zuwa yanzu ya san cewa abubuwa sun canja kwarai-kawai da gaske.

''Yanzu Birnin Gwari zuwa Kaduna 12 nadare za a bi, Abuja zuwa Kaduna 12 na dare za a bi, Zaria zuwa Funtua zuwa Gusau 12 na dare za a bi ba a tare mutane. Kusan titunan da a da ba sa biyuwa yanzu duka ana bi.'' In ji Ministan.

Dangane da rikicin jihar Filato na kwanan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ministan tsaron ya ce sun gano matsalolin da ke janyo matsalar kuma suna fatan za su hada hannu da gwamnan jihar da sarakunan gargajiya na jihar domin su tabbatar da cewa an samu sauki da fuskantar juna da kuma fahimtar juna.

Game da matsalar jihar Borno kuwa wadda a kwanan nan gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce wasu yankunan jihar sun koma karkashin ikon kungiyar Boko Haram, Ministan ya ce wannan ma matsala ce da za su shawo kanta cikin wani dan lokaci.

''Idan aka duba kusan duka kananan hukumomin jihar in banda cikin Borno ba sa hannun gwamnati a baya aka zo aka yi ta yi har aka gama, to don 'yan tsirarun wurare a yanzu an ce suna hannun wadannan mutanen za a karbo su,'' a cewar ministan.

Badaru ya ce babbar matsalar da suke fama da ita ta danganci rashin wadatar jami'an tsaro ta yadda idan sun yi maganin matsalar a wani waje, ya kamata a ce suna da isassun jami'ai da za su bari a wajen bayan sojoji sun fita, to amma rashin wadatar jami'an ke sa yankunan da a baya aka magance matsalar kan koma ruwa.

Ya ce a yanzu haka suna tsare-tsare ta yadda idan sojoji sun je sun kwato waje, sun kawar da duk wata barazanar tsaro, za a samu mutanen da za a bari a wajen su ci gaba da kula da tsaron wajen ta yadda bai sake komawa hannun miyagu ba.

Ya tabbatar da cewa shugaban kasar ya bayar da umarnin daukar karin jami'an tsaro, iya wadanda za a iya dauka aiki ta yadda ita kanta wannan matsalar karancin za ta ragu, wadda a karshe za ta taimaka wajen inganta tsaron kasar baki daya.

A halin da ake ciki dai kusan dukkanin yankunan kasar ta Najeriya na fama da matsalolin tsaro iri-iri har ana ganin sun yi wa kasar yawan da ba za ta iya yakarsu ba a lokaci daya.

A yankin arewa maso gabas musamman jihar Borno ana fama da matsalar Boko Haram, yayin da yankin arewa maso tsakiya ke fama da matsalar barayin daji da satar mutane domin karbar kudin fansa, da kuma rikicin manoma da makiyaya.

Can kuwa a yankin kudu maso gabashi kasar na fama da matsalar 'yan-a-ware na Biafra na haramatacciyar kungiyar IPOB.

A kudu maso kudanci kuwa matsala ce ta masu satar albarkatun mai da kasar ta fi samun arzikinta daga shi, galibi ta yi katutu a can.

Baya ga daidaikun matsaloli na tsaro da kusan kowa ne bangare na kasar ke fama irin tashi matsalar akwai wasu matsalolin galibi na tsaro da suka dangani zamantakewa da bambancin kabila da kuma addini da sauran matsaloli daban-daban da kasar ke fama da su.