Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man U da Arsenal na fafatawa kan Pulisic, Real Madrid na tunanin rabuwa da Endrick
Dan wasan baya na Nottingham Forest Murillo zai bar kungiyar a wannan bazarar inda Chelsea ke nuna sha'awarsa sosai, ita ma Liverpool na tunanin neman dan wasan na Brazil mai shekaru 23. (Teamtalk)
Napoli ta fara tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay, mai shekaru 29, game da tsawaita zamansa a Italiya zuwa 2030. (Corriere dello Sport)
An shaida wa Manchester City cewa za su biya fam miliyan 60-70 don daukar dan wasan tsakiya na Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekaru 26, daga Nottingham Forest a lokacin bazara. (Football Insider)
Chelsea da Tottenham suna sha'awar sayen dan wasan baya na Bayern Munich Kim Min-jae, mai shekaru 29. (CFBayernInsider)
Dan wasan gefe na RB Leipzig na Ivory Coast, Yan Diomande, mai shekaru 19, wanda aka alakanta da komawa Liverpool, ya ce kungiyar ta Anfield ita ce kungiyar da mahaifinsa ya fi so. (Bild via Goal)
Amma kocin Bayern Munich Vincent Kompany yana son shugabannin Bundesliga su doke abokan hamayyarsu na Premier League wajen daukar dan wasan. (Fabrizio Romano)
Everton na shirin sake neman dan wasan gefe na Wales Harry Wilson, mai shekaru 28, a lokacin bazara bayan Fulham ta ki amincewa da tayin a watan Janairu. (Football Insider)
Manchester United da Arsenal suna sha'awar dawo da dan wasan gaba na AC Milan da Amurka Christian Pulisic, mai shekaru 27, zuwa gasar Premier, ko da yake ita ma Tottenham na son dan wasan. Farashin tsohon dan wasan na Chelsea zai kai Yuro miliyan 70 zuwa 80 (£61-£70m). (Cough Offside)
Real Madrid na tunanin sayar da dan wasan gaban Brazil Endrick, mai shekaru 19, idan ya dawo daga zaman aronsa daga Lyon, yayin da tuni wasu kungiyoyin Premier suka fara nemansa. (Fichajes)
Juventus na son dan wasan tsakiya na Amurka Weston McKennie, mai shekaru 27, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya, amma tattaunawar ta tsaya cak saboda yana son a ninka masa albashinsa, inda a halin yanzu yake karbar Yuro miliyan 2.5-3 (£2.18m-£2.6m) a kowace kakar wasa. (Gazzetta dello Sport)
Dan wasan tsakiya Sandro Tonali, mai shekaru 25, ya sake tabbatar da kudirinsa na ci gaba da zama a Newcastle United bayan jita-jitar da ake ta faman yadawa, ta danganta shi da Arsenal. Dan kasar Italiyan ya ce ya tsinke da mugun gudu don dakile Eddie Howe bayan ya zura kwallo a gasar cin kofin FA da Aston Villa ranar Asabar saboda ya sake nunawa duniya cewa da gaske fa yana tare da kungiyar ta sa. (ChronicleLive)