Me ya sa Trump ya gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa fadarsa?

Donald Trump ,in a white USA cap and wearing a blue jacket with a US flag badge pinned to it, lift up one of his hands outside in the White House garden - 6 July 2025.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump na son tattauna kasuwaci a nahiyar Afirka kuma ba shi da niyyar bada tallafi
    • Marubuci, Abdou Aziz Diédhiou & Yūsuf Akínpẹ̀lú
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Dakar & Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald ya fara wata tattaunawa ta kwana uku a birnin Washington DC tare da shugabannin ƙasashen Afirka biyar, wani abu da Donald Trump ke yi wa kallon damar kasuwanci mai "ɗan karen kyau."

Mutanen da Trump ya gayyata sun haɗa da shugaban Gabon da Guinea-Bissau da Laberiya da Mauritaniya da Senegal - cikin su babu wanda ya ke waƙiltar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka.

Taron ganawar da za su yi ta kwanaki uku zai mayar da hankali kan batun kasuwancin Trump ba tsarin taimako ba, kuma dukkaninsu na fuskantar harajin kashi 10 cikin 100 da aka kakaba musu na kayayyakin da suke shigarwa Amurka, ana fatan su tattauna da cimma yarjejeniya a kan hakan.

Abubuwan da za a tattauna sun haɗa da batun albarkatun ƙasa da tsaron teku da 'yan ci-rani da waɗanda ake shirin tasa ƙeyarsu gida.

Ban da ƙasar Gabon, kowannesu ana amfani da hanyoyinsu wajen kwararan baƙin haure da kuma batun fataucin kwayoyi daga yankin Latin Amurka.

Wasu daga cikin waɗannan ƙasashe na fuskantar matsaloli ko barazanar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da makwaftansu ke fama - don haka ana ganin za a tattaunawa kan haɗin-kai domin ɗakile wannan barazana.

A farkon wannan shekarar Janar Micheal Langley, da ke shugabantar US Africa Command (Africom), ya gargaɗi cewa ɗaya daga cikin manufofin mayaƙan jihadi shi ne samun samar kutsawa da karfi a yankin yammacin Afirka - abin da muke zai haifar da barazana ga Amurka.

Tsohon jakadan Senegal a Washington, Babacar Diagne, ya ce gayyatar da aka yi wa shugabannin na Afirka na nuna idan Amurka ta karkata ta fuskar alaƙa da nahiyar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan hawa mulki a watan Janairu a wa'adi na biyu, Trump ya katse tallafin da Amurka ke bai wa nahiyar, yana mai cewa ana asarar kuɗi da hakan bai yi daidai da manufar fifita Amurkawa ba.

Yayinda Trump da jam'iyyarsa ta Republican ke cikin kan ganiyarsu, ana nuna shaku kan anya Amurka za ta mutunta ko sabunta yarjejeniyar karfafa alaƙa da cigaban Afirka wanda ya bada damar soke haraje-haraje kan wasu kayayyakin Afirka.

A cewar wani tsohon jami'in diflomasiya, matsayin gwamnatin Trump zai karkata ne kan yadda take tafiyar da harkokin yaƙin da Ukraine ke yi da shugabanta Volodymyr Zelensky.

A watan da ya gabata, an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Washington tsakanin Rwanda da Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo - wani diflomasiyar kasuwancin da ake ganin Amurka za ta ƙaru sosai ta hanyar samun damar cin moriyar albarkatun ƙasarsu.

Nicaise Mouloubi, wanda ke shugabantar wani kamfanin mai zaman kansa da ke harkan mai a Gabon, ya ce gwamnatin Trump na mayar da hankali a Afirka ne gudun kada abokan hamayyarta irinsu - China da Rasha - su yi musu fintinkau.

Gabon ke da kashi 1 cikin 4 na albarkatun mangenese a duniya - kuma ita ke bai wa China kashi 22 cikin 100 na albarkatun, da ake amfani da shi wajen kirkirar batiri da stainless steel.

Flames seen flaring on a offshore oil platform Gabon's Port Gentil

Asalin hoton, Gamma-Rapho/Getty Images

Bayanan hoto, Gabon mai arzikin man fetur na son mayar da hankali a kasuwancin teku da cigabanta a gaba

Mista Mouloumbi ya kara da cewa Amurka za ta fi nuna matsuwa wajen kulla alaƙa da Gabon saboda tana da albarkatun ƙasa da ba kasaifa ake samu ba, irin su manganese da uranium, da kuma ɗanyen man fetur, sannan ta kasance a yankin da ke da teku.

Ta na iya bai wa sojojin Amurka damar kafa sansani wanda dama ta jima tana son cimma hakan, a cewar Mista Mouloumbi.

Mista Diagne ya kuma yi irin wannan maganar kan batun 'yan fashin teku, yana mai cewa masu aikata ta'adanci a teku a mashigin Guinea sun kasance wani abin damuwa da ke bukatar Amurka ta bai wa muhimmanci.

Tankoki da dama da ke ɗaukan mai da gas na bi ta hanyar mashigan Guinea, wanda kuma yayi fice ko ke fuskantar matsalolin 'yandaban teku a tsawon shekaru.

Ga Mauritania da Senegal, batun ci-rani za a fi mayar da hankali, a cewar Ousmane Sene, shugaban cibiyar bincike na yammacin Afirka. (WARC)

"Ya ce kada mu manta cewa tsakain 2023 zuwa 2025, matasa dubu 20 daga Mauritania sun yi hijira zuwa Amurka ta Nicaragua, tare da daruruwan matasa 'yan Senegal," kamar yada masu sharhi suka shaida wa BBC.

Mauritania ita ce ƙasa guda cikin ƙasashen biyar da ba ta da alakar diflomasiya da kawar Amurka, Isra'ila - a 2009 ta yanke alaka da ita saboda Gaza - kuma majiyoyi sun shaida Semafor cewa, dawo da alakar na nufin cimma yarjejeniya mai gamsuwa da White House.

Sannan batun wucin wa'adin kwanakin da biza ke ɗauke da shi musamman ga Gabon da Liberia, wanda duk sun zarce Burundi, sun kasance abubuwan da suka sa Amurka ta tsawwala mutane haramci da takaita bada bizar ziyara.

A group of women with their babies wait to receive routine vaccinations at Redemption Hospital in Monrovia, Liberia. On the turquoise-painted wall in red are painted the words 'Vaccinate Your Child' and underneath there is a mural of a doctor vaccinating a child sitting on their mother's lap.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ..

Liberia na kuma iya amincewa da tayin Amurka na karban mutanen da za a ke tusa keyarsu gida, ciki harda masu laifi. Ƙasar, da tarihin alaƙarta da Amurka ya gushe, na cikin ƙasashen da rahotanni ke cewa an tuntuba.

Ƙasar, da yaƙin basasar shekara 14 ya ɗaiɗaita da kuma annobar Ebola shekaru 10 da suka gabata, a yanzu na cikin matsanancin bukatar kuɗi saboda zabtare tallafin Amurka ya shafeta matuƙa.

Sannan tasirin ya nuna ƙarara har a fannin lafiyarta, da ya dogara kan tallafin Amurka da kashi 48 cikin 100 na kasafinsa.

Guinea-Bissau, da ta sha fama da jeren juyin-muki da yunkurin kifar da gwamnati a tsawon shekaru, yanzu ta nuna matsuwarta na ganin Amurka ta sake bude ofishin jakadancina a birnin, Bissau, wanda tun 1998 yake rufe.

Shugaba Umaro Cissoko Embaló ya fito ƙarara ya yi murnar gayyatar da suka samu daga Amurka, wanda a tsawon shekaru ana yiwa ƙasarsu kallon wacce ta yi fice a harkar ƙwaya. Daga ƙasar ake fasarar hodar iblis zuwa ƙasashen Latin Amurka da Turai da Arewacin Amurka.

Shi da takwarsnsa - Brice Clotaire Oligui Nguema na Gabon, Joseph Boakai na Liberia da Mohamed Ould Ghazouani na Mauritania da kuma Bassirou Diomaye Faye of Senegal - na fatan nasara wajen cimma yarjejeniya da Trump.

Kuma ba sa su so tarihi ya maimaita kansa ba na abin da aka gani cikin watan Mayu, lokacin haduwar shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da Trump, wanda bai yi wani tasiri ba.

Ana iya cewa ziyara ta sake sukurkuta komai ganin a wannan mako ƙasar mai karfin tattalin arziki a Afirka ta fahimce cewa daga wata mai zuwa Amurka ta lafta mata harajin kashi 30 cikin 100 na kayayyakin da take kaiwa ƙasar.

Map