Rasha ta kama ɗan jaridan Amurka kan zargin leƙen asiri

Asalin hoton, AFP
An kama wani ɗan jaridan Amurka da ke aiki da jaridar Wall Street Journal a Rasha inda aka zarge shi da ayyukan leƙen asiri.
Evan Gershkovich, wani gogaggen mai aika rahotanni ne a Rasha, kuma yana aiki a birnin Yekaterinburg lokacin da aka kama shi aka tsare.
Jaridar The Wall Street Journal ta ce tana cikin "matsananciyar damuwa" game da tsaron lafiyarsa kuma da kakkausar murya ta musanta zarge-zargen da aka yi masa.
Fadar Kremlin ta shugaban Rasha ta yi iƙirarin cewa an kama ɗan rahoton ne "dumu-dumu da laifi".
Hukumar ayyukan leƙen asirin Rasha ta FSB ta ce ta "dakatar da haramtattun ayyukan" ɗan jaridan wanda ta ce ya riƙa "aiki bisa umarnin Amurka" kuma ya "tattara sirrukan ƙasar".
Sa’o’i bayan nan, jami’an tsaro suka ɗauke shi, inda suka kai shi kotu a lardin Lefortovo da ke birnin Moscow don samun ikon kama shi bisa ƙa’ida.
Daga bisani, an ga lokacin da aka yiwo masa rakiya daga cikin kotun kafin a wuce da shi a cikin mota.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax.
Lauyansa ya ce ba a ba shi damar shiga kotun ba, kuma kamar yadda kamfanin dillancin labaran Tass ya ruwaito, ɗan jaridar ya musanta zargin da aka yi masa.
Kotun tun da farko ta umarci ma’aikata da masu ziyara su fice daga cikin zaurenta saboda barazanar tashin bam, in ji kamfanin dillancin labaran Ria na Rasha.
Hukumar leƙen asirin FSB ta tabbatar a cikin sanarwarta cewa ma’aikatar harkokin waje ce ta tantance Evan Gershkovich lokacin da yake aiki a Yekaterinburg, birnin da ke da nisan kilomita 1,800 gabas daga Moscow.
Rahotonsa na ƙarshe da ya aika wa jaridar the Wall Street Journal a wannan mako ya ba da labarin cewa tattalin arziƙin Rasha yana durƙushewa, da kuma yadda fadar Kremlin take tunkarar "maƙudan kuɗaɗen da take ƙara kashewa a harkokin soja" a daidai lokacin da take ririta abin da take kashewa kan harkokin al’umma.

Asalin hoton, Reuters
Sai dai, hukumar leƙen asiri ta FSB ta yi iƙirarin cewa an tsare ɗan jaridar ne saboda ya riƙa "aiki bisa umarnin Amurka" kuma ya yi ta "tattara bayanan da za su iya zama sirrukan ƙasar game da harkokin wani kamfanin tsaron Rasha".
Ta ƙara da cewa wani sashen hukumar tuni ya ƙaddamar da bincike kan batun mummunan laifin leƙen asiri da aka aikata.
Sai dai a cikin wata sanarwa, jaridar Wall Street Journal ta ce tana goyon bayan ɗan jaridar da kuma iyalinsa: "Cikin kakkausar murya, jaridar the Wall Street Journal ta musanta zarge-zargen da hukumar leƙen asiri ta FSB ta yi, kuma tana neman a gaggauta sakin jajirtacce kuma amintaccen ɗan jaridar namu, Evan Gershkovich."
Fadar Kremlin ita ma ta yi bayani a kan batun tsare ɗan jaridar na Amurka. "Wannan haƙƙi ne na hukumar FSB, kuma tuni suka fitar da sanarwa," in ji mai magana da yawun fadar Dmitry Peskov. "Abu ɗaya kawai da zan ƙara shi ne, a iyakar saninmu, an kama shi ne dumu-dumu."
Laifin satar bayanan sirri a Rasha na ɗaukar hukunci mafi tsanani na tsawon shekara 20 a gidan yari.
Tun ma kafin fara mamayen ƙasar Yukren a watan Fabrairun 2022, ɗauko rahoto daga Rasha ya ƙara zama jan aiki ga manema labarai.
Ana yi wa 'yan jarida masu zaman kansu laƙabin "'yan aiken ƙasashen waje" har ma an kori 'yar jaridar BBC a Rasha Sarah Rainsford daga cikin ƙasar.
Lokacin da aka fara yaƙin Yukren, Rasha ta ɓullo da wata doka da ke kallon aika “rahotannin jabu” ko “shafa wa sojoji kashin kaji” a matsayin aikata babban laifi a ƙarƙashin haka kuma an hukunta gomman Rashawa saboda sun soki lamirin mamayen Yukren a shafukan sada zumunta.
An rufe bakin kusan duk kafofin labarai masu zaman kansu, ko kuma an rufe su kwata-kwata, ko an toshe su, a ciki har da manyan gidajen talbijin kamar TV Rain da Radio Echo ta Moscow da jaridar Novaya Gazeta. Da yawan kafofin yaɗa labaran Ƙasashen Yamma sun fice sun bar Rasha.
Wata ƙwararriyar mai sharhi kan harkokin siyasa a Rasha Tatyana Stanovaya ta ce kama Mista Gershkovich ya zo da matuƙar ban mamaki.







