Hare-hare ta sama a Khartoum bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wuta

Faɗa na ci gaba da rincaɓewa a Khartoum babban birnin ƙasar Sudan bayan yin watsi da yarjajeniyar tsagaita wuta domin bai wa fararen damar ficewa daga birnin.

A ranar Lahadi sojojin ƙasar sun ce suna kai wa birnin hare-hare ta kowanne ɓangare ta sama da manyan makaman atilare, domin fatattakar abokan faɗansu dakarun RSF.

Da tsakar daren yau Lahadi ne yarjejeniyar tsagaita wutar ke ƙarewa, yayin da har yanzu miliyoyin mutane ke maƙale a birnin wanda ke fama da ƙarancin abinci.

Tuni dai jirgin farko ɗauke da kayan agaji da magunguna ya isa ƙasar.

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce jirgin ya sauka a tashar jiragen ruwan Sudan ɗauke da tan takwas na kayan agaji da suka haɗar da magunguna.

Fiye da kashi 70 na cibiyoyin lafiyar ƙasar aka tilasta wa rufe ayyukansu sakamakon rikicin da ya ɓarke tun ranar 15 ga watan Afrilu.

Fiye da mutum 500 ne suka mutu, yayin da ake sa ran adadin zai ƙaru.

Kwamandan dakarun sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban rundunar RSF Janar Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da Hemedti, na faɗa da juna, sakamakon rashin shigar da dakarun RSF cikin rundunar sojin ƙasar.

Ƙasashen duniya na ci gaba da kwashe al’ummarsu sakamakon rikicin.

A faɗaɗa yarjejeniyar da aka cimma ranar Alhamis da daddare bayan tattaunawar diplomasiyya tsakanin ƙasashe makwabta tare da haɗin gwiwwar Amurka da Birntaniya da Majalisar Dinkin Duniya, to sai dai ɓangarorin da ke faɗa da junan sun ƙi martaba ƙarin wa’adin.

Da maraicen ranar Asabar ne aka ci gaba faɗa a birnin Khartoum, inda dakarun sojin ke cewa sun ƙaddamar da sabbin hare-haren ne domin fatattakar dakarun RSF.

Wani shaidar gani da ido ya faɗa wa kamfanin dillancin labari na Reuters cewa ya ga jirgin yaƙin soji maras matuƙi na kai hari a kusa da inda dakarun RSF suke a kusa da babbar matatar man fetur ta ƙasar.

A ranar Asabar gwamnatin Birtaniya ta ce ta kammala ɗaukar ‘yan ƙasarta, kusan 1,900.

Ita ma tawagar Amurka ta isa tashar jiragen ruwan Sudan domin kwashe Amurkawan da ke Sudan a jirgin ruwa zuwa birnin Jedda na ƙasar Saudiyya.

Daruruwan Amurkawa ne suka fice daga ƙasar cikin har da jami’an diplomasiyyar ƙasar da ke Sudan cikin makon da ya gabata.

A ranar Asabar tsohon firaministan Sudan Abdalla Hamdokya yi gargaɗin cewar rikicin ƙasar ka iya munana fiye da na Siriya da Libiya, ƙasashen da yaƙi ya ɗaiɗaita fararen hula da dama tare da hasarar rayuka masu yawa da kuma raba dubbai da muhallansu