Argentina ta tsallaka zagaye na biyu a Copa America

Argentina

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Argentina ta kai zagayen ne bayan cin wasa biyu cikin uku a rukuni

Argentina ta zama ƙasa ta farko da ta samu gurbin buga zagaye na biyu a gasar Copa America ta 2024 da ke gudana a Amurka.

Tawagar ta samu nasarar kaiwa zagayen kwata fayinal ne sakamakon doke Chile 0-1 a wasan da suka buga da tsakar daren da ya gabata, bayan Lautaro Martinez ya ci ƙwallo a mintunan ƙarshe.

Argentina mai riƙe da kofin ta mamaye baki ɗayan wasan da aka buga a filin wasa na MetLife Stdaium da ke birnin New Jersey, inda ta buga shot har 22.

Ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, da na tsakiyar Fiorentina Nicolas Gonzalez ne suka fara kai wa golan Chile Claudio Bravo hari tun da farkon wasan.

Messi ne ya fara samun dama mafi kyau tun kafin tafiya hutun rabin lokaci amma sai ta bigi tirke.

Har sai a minti na 72 Chile ta kai harin farko bayan Rodrigo Echeverria ya ɗaɗa wa gola Martinez ƙwallon da shi kuma ya fitar da ita bugun kwana.

An ci gaba da fafatawa inda har sai da aka kai saura minti biyu lokaci ya cika sannan Lautaro Martinez ya sauya wasan bayan ya shigo daga baya.

Argentina ce ta ɗaya a Rukunin A da maki shida wanda hakan ya sa ta samu gurbin zagaye na gaba tun kafin ta buga wasan ƙarshe da Peru ranar Lahadi.

Canada tana matsayi na biyu bayan ta samu nasara kan Peru da ci 1-0 a wasan da suka buga ranar Talata.