Everton na son riƙe Grealish, Liverpool da Man United na rubibin Mokio

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jack Grealish
Lokacin karatu: Minti 2

Everton na fatan siyan Jack Grealish na Manchester City a kan kasa da fam miliyan 50, Manchester United, Liverpool da Chelsea na zawarcin Adam Wharton na Crystal Palace, yayin da Fulham ke tunanin makomar Harry Wilson.

Everton na fatan za ta iya siyan dan wasan Ingila Jack Grealish daga Manchester City kan kudi kasa da fan miliyan 50 bayan ɗanwasan ya kammala buga mata a matsayin aro. (Telegraph)

Manchester United na daya daga cikin kungiyoyin da ke duba yiwuwar siyan dan wasan tsakiyar Crystal Palace Adam Wharton a watan Janairu, inda Liverpool da Chelsea ke zawarcin dan wasan na Ingila mai shekara 21. (Caughtoffside)

Chelsea ta yi kokarin sayen dan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 25, kafin ya koma Tottenham a bazara, amma ta kasa shawo kan West Ham ta amince ta ba ta wani dan wasanta sannan ta kara mata da kudi. (Fabrizio Romano)

Zai wajaba a kan Nottingham Forest ta dauki dan wasan tsakiya na Juventus a matsayin aro Douglas Luiz, mai shekara 27, kan Yuro miliyan 25 (£21.6m) idan dan wasan na Brazil ya buga minti 45 cikin wasanni 15 na gasar Premier a wannan kakar. (La Gazzetta dello Sport)

Liverpool da Manchester United suna cikin kungiyoyi da dama da ke zawarcin matashin dan wasan Ajax Jorthy Mokio mai shekaru 17, wanda tuni Belgium ta sanya shi cikin tawagarta, kuma zai iya buga baya ko tsakiya. (Teamtalk)

Borussia Dortmund na iya kokarin siyan dan wasan bayan Argentina Aaron Anselmino, mai shekara 20, na dindindin idan ya taka rawar gani a Chelsea, inda ya je aro. (Bild German)

Dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Sam Mather, mai shekara 21, yana tattaunawa domin ya koma kungiyar Kayserispor ta Turkiyya. (Manchester Evening News)

Chelsea, da Everton da Brighton duk sun yi bincike a bazara kan dan wasan Barcelona kuma na tsakiyar Spain Marc Bernal mai shekaru 18. (Mundo Deportivo)

Chelsea na sha'awar sayen dan wasan Juventus da Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, amma za ta biya £86m (€100m). (Fichajes Spanish)

Fulham za ta nemi kudi don siyan dan wasan tsakiya Harry Wilson a watan Janairu don gujewa rasa dan wasan Wales mai shekara 28 kyauta a bazara. (Football Insider)

Babban jami'in kwallon kafa na Nottingham Forest Ross Wilson zai bar aikinsa a City Ground don zama darektan wasanni na uku a Newcastle cikin shekaru uku. (paper I)