Ta yaya faɗuwar farashin ɗanyen mai zai shafi tattalin arziƙin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Farashin danyen mai ya fadi inda ya fadi da kashi 12 cikin 100 wato ya koma dala 65.50 kan kowacce ganga, bayan da shugaba Donald Trump ya kakabawa kasashe da dama haraji.
Kafin sanar harajin, ana sayar da gangar mai a kan fiye da dala 70.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya sanya hannu a kan kasafin 2025 in da ya kayyade farashin kowacce ganganr danyen mai a kan dala 75.
Hakan na nuna cewa gwamnatin Najeriya sai ta lalubo hanyar da zata cike gibin dala 10 tun da farashin danyen mai ya fado zuwa dala 65 kan kowacce gangan.
'Yan Najeriya da dama na mamakin yadda rashin mai ke tashi ya sauka a kodayaushe wanda hakan na matukar shafar tattalin arzikin kasar da ma rayuwarsu.
Ya wannan matsala za ta shafi 'yan Najeriya da ma tattalin arzikin kasar?
Dangane da wannan dambarwa, sashen BBC Pidgin, ya tattauna da daya daga cikin masana, Farfesa Kabiru Isa Dandago, wanda malami ne a sashen kula da kudi na jami'ar Bayero da ke Kano.
Farfesa Dandago, ya ce ko shakka babu faduwar farashin danyen man dai zai shafi tattalin arziki Najeriya da ma 'yan kasar, a don haka sai ;yan kasar su shirya dandana kudarsu.
Ya kara da cewa,"Yanzu akwai bukatar 'yan Najeriya su shirya jurewa duk wani kalubale da gwamnatin kasar za ta fusaknta.Saboda kudaden shigar kasar za su ragu, sannan idan suka ragu gwamnatin ba za ta aiwatar da duk wasu abubuwa da ya kamata ta yi da kudaden shigar ba."
A don haka idan gwamnatin na son tabbatar da tattalin arzikinta bai jijjiga ba, to hakan na nufin sai gwamnati ta ciyo bashi domin cike gibi.
Ya ce, "Yawancin ayyukan da gwamnati ta ce za ta yi ba za ta iya yinsu ba, don akwai bukatar kasar ta ciyo bashi don cike gibin kudaden da ta yi niyyar kashewa wajen gudanar da ayyukan a kasa."
Ya kuma ce, kasashen da shugaban Amurka Donald Trump ya kakabawa haraji, za su nemo hanyoyin da za su rika fitar da kayayyakinsu.
Mecece mafita ga Najeriya?
Farfesa Dandago, ya ce ya kamata gwamnatin nNajeriya ta nemo hanyar da zata rika sayar da danyen manta a maimaikon dogara a kan kasuwar Amurka kadai, ya kamata Najeriya ta mayar hankali wajen kai wa kasashen da ke bukatar danyen mai danyen manta.
Ya kamata Najeriya ta nemo hanyar da zata rika sayar da kayayyakinta kamar albarkatun kasa da kuma kayan amfanin gona.
Farfesa Dandago ya ce," Idan har Najeriya ta kasa samun kudi daga bangaren mai, sai ta koma neman kudi daga kayayyakin albakatun kasar da ta ke fitarwa da na noma da makamantansu."
Daga karshe, malamin jami'ar, ya bayar da shawarar cewa ya kamata Najeriya ta daina dogara kacokan a kan danyen mai, tun da kasar na da abubuwa da dama da zasu iya kawo mata kudi kamar albarkatun kasa da kuma fasahar kirkirar da matasan kasar ke da ita.














