Euro 2024: Jorginho da Vicario suna cikin ƴan Italiya na ƙwarya-ƙwarya

Ɗan wasan Arsenal, Jorginho da mai tsaron ragar Tottenham Guglielmo Vicario suna cikin ƴan ƙwallo 30 da Italiya ta bayyana na ƙwarya-ƙwarya domin Euro 2024.

Sai dai ba a gayyaci ɗan wasan Lazio, Ciro Immobile da Marco Verratti, wanda ya koma ƙungiyar Qatar, Al-Arabi daga Paris St-Germain cikin Satumba ba.

Rabonda kociyan tawagar Italiya, Luciano Spalletti ya kira Verratti tun bayan da ya maye gurbin Roberto Mancini cikin Agustan 2023.

Italiya mai rike da kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Ingila a Wembley karkashin Mancini, ta kasa shiga gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Haka kuma Spalletti ya gayyaci Nicolo Fagioli na Juventus a karon farko tun bayan wata bakwai da aka dakatar da shi, bayan samunsa da laifin karya dokar yin caca.

Haka kuma Italiya ta kira Gianluca Scamacca, wanda bai buga wa kasar wasan sada zumunta cikin watan Maris da Venezuela da Ecuador ba.

Ɗan wasan yana cikin wadanda suka bayar da gudunmuwar da Atalanta ta lashe Europa League ranar Laraba a Dublin, bayan doke Bayern Leverkusen 3-0.

Italiya za ta tantance ƴan wasa 26 daga 30, kafin 7 ga watan Yuni a gasar da Jamus za ta karbi bakunci cikin Yuni zuwa Yuli.

Tawagar za ta buga wasan sada zumunta da Turkiya da kuma Bosnia-Herzegovina kafin ta fara karawar farko a Euro 2024 da Albania ranar 15 da watan Yuni a rukunin da ya hada da Sifaniya da kuma Croatia.

Ƴan wasan tawagar Italiya na ƙwarya-ƙwarya:

Masu tsare raga: Gianluigi Donnarumma (Paris Saint-Germain), Alex Meret (Napoli), Ivan Provedel (Lazio), Guglielmo Vicario (Tottenham)

Masu tsare baya: Francesco Acerbi (Inter Milan), Alessandro Bastoni (Inter Milan), Raoul Bellanova (Torino), Alessandro Buongiorno (Torino), Riccardo Calafiori (Bologna), Andrea Cambiaso (Juventus), Matteo Darmian (Inter Milan), Giovanni di Lorenzo (Napoli), Federico Dimarco (Inter Milan), Gianluca Mancini (Roma), Giorgio Scalvini (Atalanta)

Masu buga tsakiya: Nicolo Barella (Inter Milan), Bryan Cristante (Roma), Nicolo Fagioli (Juventus), Michael Folorunsho (Verona), Davide Frattesi (Inter Milan), Jorginho (Arsenal), Lorenzo Pellegrini (Roma), Samuele Ricci (Torino)

Masu cin kwallaye: Federico Chiesa (Juventus), Stephan El Shaarawy (Roma), Riccardo Orsolini (Bologna), Giacomo Raspadori (Napoli), Mateo Retegui (Genoa), Gianluca Scamacca (Atalanta), Mattia Zaccagni (Lazio)