Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda shan miyagun ƙwayoyi ya zama jiki ga 'yan matan Somaliya
Gano gawar wata matashiya - mai shekara 22 a gafen titi a Mogadishu babban birnin Somaliya a shekarar da ta gabata - ne ya fito da matsalar yadda matasan 'yan matan ƙasar suka shaƙu da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar. Likitoci sun ce ta mutu sakamakon shan ƙwayoyi fiye da ƙima.
Abokananta da masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce ta ɗauki lokaci mai tsawo tana yin allurar da ke sa maye. Sun ce sai ta yi mankas kafin ta fara naɗar bidiyoyin da take wallafawa a shafinta na TikTok.
'Yan sanda sun ce an samu ƙaruwar masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a birnin Mogadishu da sauran sassan ƙasar, ciki har da mata. Sun ce a yanzu mutane sun koma amfani da sabbin nau'in ƙwayoyi.
Inda suke cin wani nau'in ganye da ake kira Khat a ƙasar - wanda ba haramtacce ba ne - sannan sai su sha giya, ko su zuƙi sufa gilu ko su sha tabar wiwi, sannu a hankali mutane na amfani da allura mai ɗauke da sinadarin opioids inda suke yinta a jikin jijiyoyinsu.
A farko watan Disamba, 'yan sanda suka kama wata tarin ƙwaya yawanci mai ɗauke da sinadarin bugarwa a filin jirgin saman Mogadishu, tare da kama mutanen da ake zargi su ne shigo da ita.
''Miyagun Ƙwayoyi na nau'in allurai da ƙwaya sun zaman ruwan dare musamman kan matasan 'yan mata da ƙananan 'yan mata'' a cewar wani likita a birnin Mogadishu, wanda ya buƙaci a sakaya sunansasaboda girman matsalar.
''Mafi yawan waɗanda suke amfani da ƙwayoyin sun zame musu jiki, ta yadda suke sayensu a shagunan sayar da magani a ko'ina cikin birnin, ba tare da amincewar likita ba''.
'Na fara kwana a tasha da gefen titi'
Wani fitaccen ƙwaya da matasan matan ke amfanin da shi shi ne taunar ganyen tobacco da aka fi sani da 'tabbuu', wanda ke janyo cutar sankarar baki da ta maƙogoro.
Amino Abdi, wata matashiya ce mai shekara 23 kuma ta kwashe kusan shekarar biyar tana ta'ammali da miyagun ƙwayoyi. Duk da cewa abin kunya ne shan miyagun ƙwayoyi ga mata a ƙasar Somaliya, ta shaida wa BBC cewa ta yanke shawarar yin magana ne game da batun cike da fatan samun raguwar matsalar.
"Na fara taunar ganyen tabbuu tare da 'yan matan da nake zaune da su," in ji ta.
''Sun kasance ɓata-garin ƙawaye a gareni. Bayan da taunar ganyen tabacco ya zama jiki a gareni, sai na fara shan miyagun ƙwayoyi, har ta kai ga ina yin allurar tramadol da ta pethidine''.
Misis Abdi ta ce takan sha ƙwayoyin a duk lokacin da ta samu saɓani da mijinta, lamarin da yake sa ta shafa wa fuskarta shuni tare da yi wa mijin nata tatas. Daga ƙarshe dai mijin ya sake ta bayan da ta haifi 'ya mace.
"Tsohon mijina ne sadanin sabawata da ƙwaya. Ta bi jikina ta yadda bana sanin inda hankalina yake. Daga ƙarshe na fara kwana cikin tasha da gefen tituna".
Misis Abdi na ƙoƙarin yadda za ta daina shan ƙwaya, to amma ta ce yin hakan abu ne mai wahala saboda babu cibiyoyin sauya ɗabi'a a Somaliya da za su taimaka mata wajen barin ɗabi'ar shan ƙwayar.
Ta ce ba zai yiyu ta daina amfani da ƙwayoyin a lokaci guda ba. To amma ta samu nasarar rage yawan alluran da take yi, sai dai har yanzu tana taunar ganyen tobacco tare da shan shisha.
Iyaye musamman uwaye na ci gaba da bayyana fargabarsu game da ƙaruwar shaye-shye tsakankanin 'yay'yansu mata, waɗanda wasunsu har yanzu na makaranta.
Khadijo Adan ta ce ta fahimci 'yarta maishekara 14 na yin wasu abubuwa da suka saɓa wa hankali.
"Tana yawan yin bacci a kowanne lokaci, tare da yin wasu abubuwa da ban saba gani ba," in ji mahaifiyar tata.
"Wata rana sai na samu ƙwayar tramadol da ganyen tobacco a cikin jakarta, da na tuntuɓeta sai ta shaida min cewa ta fara shan ƙwaya ne daga wajen ƙwayenta''.
Daga nan ne sai Misis Adan ta tura 'yar tata wata makarantar kwana da wasu malaman addinin musulunci ke gudanarwa. A yanzu ta daina shan ƙwaya saboda ba ta iya ganin ƙwayoyin a makarantar.
Many parents send their "problem" children to such institutions, especially those with mental illnesses, those involved in crime or drugs and those suspected of being gay.
Iyaye da yawa kan tura 'ya'yansu da ke da matsaloli zuwa makarantun kwana, musamman waɗanda ke da taɓin hankali, da masu ta'ammali da ƙwaya da waɗanda ake zargi da neman jinsi.
Yaran da ke gararamba kan tituna na cikin hatsari
A yayin da ƙasar ke fama da matsanancin fari cikin shekara 40, tare da yaƙi na kusan shekara sama da 30, sauran albarkatun ƙasar ba za su iya biya wa al'umar ƙasar buƙatunsu ba, sai kuma ga shi yanzu matsalar shan miyagun ƙwayoyi na neman bulla a ƙasar.
Wasu ƙungiyoyi 'yan ƙalilan sun fara kiraye-kirayen wayar da kan jama'a game da illar shan miyagun kwayoyin.
Wata ƙungiya mai suna The Green Crescent Society kan ziyarci makarantu da jami'o'i tare da gargaɗin dalibai game da illar sabawa da shan miyagun ƙwayoyi, da shaha, da sauran nau'ikan laifuka.
Sirad Mohamed Nur shi ne ke gudanar da gidauniyar Mama Ugaaso, wadda ke mayar da hankali wajen matsalar shan miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa ciki har da 'yan mata.
"Muna baƙin ƙoƙarinmu wajen ganin matasa sun daina shaye-shaye ta hanyar shirya tarukan wayar da kan jama'a game da illar da ƙwayar ke yi wa lafiyarsu''.
"Muna kuma yin kira ga gwamnati da ta shigo ciki tare da yin wani abu domin kawar da wannan matsala. Amma wannan kaɗai ba zai isa ba, muna buƙatar ɗaukar matakai wajen ganin ƙwayoyin ba su kai ga hannun matasanum ba, musamman yaran da ke tallace-tallace a kan tituna''.
Wasu alƙaluma da hukumar kula da mata da 'yancin ɗan adam suka fitar sun ce kashi 40 cikin 100 na yaran da ke tallace-tallace a kan titunan na shan miyagun ƙwayoyi.
Kusan kashi 50 cikin 100 na yaran da ke tallace-tallace a kan titunan ƙasar mata ne, kuma kashi 10 cikinsu 'yan kasa da shekara shida ne, wasu ma ba su fi shekara uku ba.
Duk da cewa ganyen khat, da zuƙar sufa gilu da taunar ganyen tobacco su ne shaye-shayen da suka zama ruwan dare a ƙasar tsakanin yaran da ke gararamba a gefen titi, wani bincike da hukumar ta gudanar ya gano cewa kusan kashi 10 cikin 100 na yaran na amfani da manyan ƙwayoyin da ke ɗauke da sinadarin opioids, kuma kashi 17 cikin 100 na amfani da ƙwayoyin da ke sa bacci.
Ƙaruwar shaye-shaye tsakanin matasa ya ƙara samun yawaitar aikata laifukan da suka haɗar da cin zarafin mata da 'yan mata a ƙasar.