Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne matsayin azumin mai zalunci a Ramadan?
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Azumin Ramadana lokaci ne na kamewa da kuma yawan aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da tarin lada tare da ƙaurace wa yin duk wani abin ƙi don kauce wa samun zunubi.
Addinin musulunci ya shimfiɗa hanyoyin zaman lafiya da tafiyar da rayuwa kuma cikin manya-manyan dokokin ubangiji, akwai haramta cuta da kuma wajabta adalci.
A wannan maƙala, za mu duba batun zalunci wanda wani nau'i ne na cuta ga mai azumi a watan Ramadana.
Mun tuntuɓi Dakta Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu, wanda shi ne babban limamin masallacin Dutse ya ce azumi ibada ce da Allah ya wajabta a kan duk musulmi kuma "ko da yana da wasu laifuka, ba a cewa saboda shi mai laifi ne an sauke masa wajibi."
Ya ce mai zalunci - kamar yadda kowane musulmi - ko salihin bawa ko mai kirki ya wajaba a kansa ya yi sallah ya kuma fitar da zakkah sannan ya sauke farali idan yana da hali.
A cewar malamin, akwai ƙa'ida ta hukuncin mutum yana wani laifi sannan kuma ya yi wani aikin kirki, "in dai ba wani abu aka samu na cewa abu kaza ya na rusa aikin mutum ba, aikinsa daban, zaluncinsa daban."
Ya bayyana cewa a duk lokacin da wani ya yi zalunci, to ana rubuta masa cewa "ya zalunci wani".
"Idan ya samu ya mayar da haƙƙoƙin zaluncin nan a rayuwarsa, to ya tsira, idan kuwa har ya bar duniya bai mayar da wannan zaluncin ga waɗanda ya zalunta ba, to ranar ƙiyama, ayyukan da ya aikata na lada su za a ɗauka a bai wa waɗancan da ya zalunta." in ji malamin.
Ya ce hakan yana nuna ana karɓar aikin mai yin zalunci don da ba a karɓa, ladansa ba zai taru har a kwasa daga ciki a bai wa mutanen da ya zalunta ba.
Ya yi ƙarin haske da cewa matuƙar mai zalunci ya cika sharuɗɗa, za a karɓi azuminsa sannan zaluncin da ya yi yana nan an rubuta shi.
Dakta Abubakar ya ce ba a haɗa laifin mutum da kuma azuminsa saboda "mutum ba zai zama mala'ika ba sannan aikinsa ya karɓu, idan aka ce sai ba ka zunubi sannan za a karɓi ayyukanka na alkhairi, shari'ah ba haka ta ce ba." in ji shi.
Ya kuma bayar da misali da masu tsawwala farashin kaya a lokacin azumi inda ya ce waɗanda ke ƙara farashi don zaluntar mutane, duk mai yin zalunci Allah Ya haramta zalunci amma hakan a cewarsa, ba ya nufin azumin mai zalunci bai karɓu ba.