Yadda ake amfani da labaran bogi wajen kambama shugaban Burkina Faso

    • Marubuci, Chiagozie Nwonwu, Mungai Ngige, and Olaronke Alo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
  • Lokacin karatu: Minti 5

A wani bidiyo da aka nuna wani gida turnuƙe da hayaƙi, sannan ga mawaƙiya Beyonce sanye da kakin soja tana tuƙa tankar yaƙi, da kuma shugaban mulkin soji na Burkina Faso Ibrahim Traore yana harba bindiga. Sai kuma waƙar da a ciki aka ji wani mawaƙi yana cewa, "Allah ya kare Ibrahim Traore a ƙoƙarin da yake yi na kare muradun ƴanƙasarsa."

Amma a gaskiya ba Beyonce da Traore ba ne, bidiyo ne na bogi irin wanda ake haɗawa da ƙirƙirarriyar basira.

Akwai ɗaruruwan bidiyoyin ƙirƙirarriyar basira da ke nuna Traore a matsayin mai fafutikar kare muradun Afirka, amma yawanci suna ƙunshe da labaran bogi, duk da sun karaɗe shafukan sada zumunta musamman a yankin Sahel tun daga watan Afrilu.

Bidiyoyin suna tashe matuƙa musamman a kafofin sadarwa irin su X da Facebook da Instagram da TikTok da WhatsApp da YouTube a ƙasashe kamar Najeriya da Ghana da Kenya kuma a ciki duk ana nuna Traore da sauran shugabannin ƙasashen Afirka.

Labaran bogi da na ƙarya

Shugaban mulkin na soji mai shekara 37, wanda ya ƙwace mulki a ƙasar ta Afirka ta Yamma a shekarar 2022 yana bayyana kansa a matsayin wanda yake fafutikar kare muradun Afirka, da suka ga abubuwan da yake kira da kutsen ƙasashen yamma, musamman ma Faransa da Afirka, sannan yake nuna Rasha a matsayin ƙawar arziki.

A ƙarƙashin mulkin Traore, Burkina Faso na fuskantar koma-baya a dimokuraɗiyya, inda ake samun rahotannin kama ƴanjarida da masu sukar gwamnati, sannan a tursasa musu zama sojoji.

A wani rahoto da Human Rights Watch ta fitar, an zargi gwamnatin ƙasar da kashe aƙalla fararen hula guda 100 a wani hari a watan Maris.

Amma a yawancin lokuta, Traore na bayyana kan shi a matsayin shugaba "mai sauƙin kai", kuma ya samu nasarar nuna kansa a haka a idon duniya, wanda hakan ya janyo masa masoya a birnin Ouagadougou. Wasu ma sun fara bayyana shi da sabon Thomas Sankara, wanda fitaccen shugaban ƙasar da ake kashe a shekarar 1987.

Masu sharhi suna cewa matasan Afirka sun fara gajiya ne yadda ake tafiyar da mulki a nahiyar, wanda hakan suke amsa saƙonnin Traore musamman na adawa da ƙasashen yamma. Ya iya jera magana cikin azanci, wanda hakan ya wasu suke masa kallon jagora nagari da ya kamata a yi koyi da shi.

Duk da cewa Traore na da masoya da dama a Afirka, "ƙaruwar bidiyoyin ƙirƙirarriyar basira da ake yaɗawa na nuna akwai cewa akwai lauje cikin naɗi," in ji Eliud Akwei, babban ɗanjarida mai binciken ƙwaƙwaf a cibiyar Code for Africa mai bincike tare da ƙaryata labaran ƙarya.

Akwai wani bidiyon da ke cewa an ba dogaran Traore dala miliyan 5 domin su kashe shi, wanda sama da mutum miliyan ɗaya suka kalla. Duk da cewa an samu labaran yunƙurin juyin mulki a ƙasar, babu wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirarin.

Akwai bidiyo kuma da aka kalla sau miliyan 4.5, wanda aka ƙirƙira da ke nuna yadda Traore ya yi shigar burtu ya shiga wani jirgi, amma sai ma'aikaciyar jirgin ta buƙaci ya sauya kujera saboda ɗan Faransa zai zauna a kujerar. Duk da cewa an bayyana bidiyon a matsayin na "ƙirƙira" tashoshin YouTube da dama sun yaɗa bidiyon.

Dr Lassane Ouedraogo mai koyarwa a tsangayar sadarwa a Jami'ar Ohio ne, amma ɗan asalin ƙasar Burkina Faso, ya ce, "wasu abubuwan da ake yaɗawa abubuwa ne kawai da ake fata, wasu abubuwa ne da suke wakana, amma ake ƙara gishiri a miyar."

Bayan haka akwai bidiyoyin waƙa da ake yaɗawa kamar wanda ke nuna Traore da Selena Gomez da Rihanna suna masa waƙ. An saka irin waɗannan bidiyon aƙalla guda 40 a cikin mako ɗaya kawai.

Tarin gwal

An fara yaɗa abubuwan da suka shafi Traore ne bayan zuwansa taron ƙasashen Afirka da Rasha ta shirya a watan Yunin 2023. An yaɗa hotonsa da Shugaban Rasha Vladmir Putin da jawabinsa a wajen taron sosai, wanda hakan ya ƙara ɗaga darajarsa a nahiyar.

A wani taron bahasi na majalisar dattawa ta Amurka, shugaban Africom, Janar Michael Langley ya zargi Traore da amfani da arzikin gwal na ƙasar domin kare muradun ƙasar. Wannan ya sa aka fara yaɗa batun cewa Amurka na yunƙurin cire shi daga mulki.

A ranar 22 ga watan Afrilu, wani shafi mai mabiya miliyan 1 a X ya rubuta cewa Langley ya faɗa wa majalisar dattawar Amurka cewa, "Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore barazana ce da mutanen ƙasarsa."

Amma asalin abin da Langley ya faɗa, kamar yadda BBC ta gani shi ne arzikin da Burkina Faso ke da shi na gwal ne suke amfani da shi "a matsayin domin kare mulkin sojin ƙasar."

Haka kuma wani bayani daga Code for Africa ya nuna cewa bayan jawabin na Mr Langley, wasu gungun masu amfani da Facebook da suka kai 165 sun yi amfani da irin saƙon wajen cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tura wa Traore dakaru na musamman domin kare shi daga Amurka, kuma bidiyon da aka ƙirƙira an kalle shi sama da miliyan 10.9 a cikin kwana 10 kacal.

Amma a gaskiya tun asali akwai sojojin Rasha a Burkina Faso tun kafin wannan lokacin, inda suke taimakon ƙasar wajen yaƙi da ta'addanci, kuma zamansu ba shi da alaƙa da jawabin da aka yi a Amurka.

A shafin X, wani ya wallafa bidiyon mutane, sannan ya rubuta cewa, "kalla ɗimbin mutane ne da suke gangamin nuna goya bayansu ga Ibrahim Traore da ƴancin ƙasar a Faransa."

Da aka gudanar da binciken ƙwaƙaf kan bidiyon, ya nuna cewa ɗaya daga cikin gidajen da ke cikin bidiyoyin Cocin Orthodox na St. Mark ne da ke Belgrade a ƙasar Serbia, kuma taron gangamin adawa da gwamnati ne da aka yi a Belgrade a watan Maris na 2025.

Mai amfani da kafofin sadarwa na Ghana, Sulemana Mohammed ya wallafa bidiyon a Facebook, inda ya ce gangamin masoya Traore ne da aka yi a Afirka ta Kudu. Duk da cewa BBC ta faɗa masa cewa ba haka ba ne, Mohammed ya cigaba da dogewa kan ra'ayinsa.

"Abin ban dariya ne yadda mutane suke kallon abin da muke faɗa game da shugabanninmu ba gaskiya ba ne," in ji shi.