'Yadda muka samu baƙuncin Osama ba zato ba tsammani'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, ایم الیاس خان
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی بی سی
- Lokacin karatu: Minti 4
Ya za ka ji idan baƙon da aka ce zai zo gidanka don cin abincin dare ya kasance shi ne wanda duniya ke nema ruwa a jallo?
Shi ne shugaban ƙungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden, kuma gidan da ya je baƙunci domin cin abincin dare yana a yankin Waziristan, da ke cikin ƙasar Pakistan.
Shekara ɗaya bayan wannan ziyara da ya kai, sojojin Amurka suka kashe Osama bin Laden a yankin Abbottabad, ranar 2 ga watan Mayun 2011.
Shekara ɗaya bayan mutuwarsa, a 2012, BBC ta wallafa labarin wasu mutum biyu daga Waziristan da suka bayar da labarin lokacin da Osama bin Laden ya ziyarci gidansu, amma ba su san ko wane ne shi ba.
A cewar labarin da aka bai wa Ilyas Khan, aƙalla mutum shida ne a Waziristan suka zauna jiran baƙo wanda aka faɗa musu tun makonni kafin haka, da cewa wani muhimmin baƙo zai zo.
Ba a faɗa musu sunan baƙon ba. Da misalin ƙarfe 11:00 na dare, lokacin da mutanen yankin ke barci sai mutanen gidan suka ji ƙarar motoci na isowa.
Ɗaya daga cikinsu, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce: "Kusan motoci 12 ne danƙara-danƙara suka shigo gidanmu daga ɓangarori daban-daban."
Ɗaya daga cikinsu ta tsaya a gaban barandar gidan, sai wani dogon mutum siriri sanye da rawani da doguwar riga ya fito daga kujerar baya.

Asalin hoton, Getty Images
Cikin dare mutanen nan suka shiga mamaki saboda mutumin da suke gani ba gama-gari ba ne - shi ne mutumin da aka fi nema ruwa a jallo a duniya.
Amurka ta sanar da tayin ladar dala miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama shi.
"Mun sha mamaki. Ba mu tsammaci Osama ne baƙon da zai zo gidanmu ba," a cewar mazaunin Waziristan.
Osam ya gaisa da kowa a wurin. A cewar mutumin wanda shugaba ne a unguwar, ya riƙe hannun Osama, ya sumbace shi.
Osama ya ɗora hannunsa kan kafaɗar ɗaya daga cikin mutanensa kuma suka ƙarasa ɗakin da aka tanada domin zaman. Iyalin ba su bi su ciki ba, sai mutum biyun da ke tare da Osama ne kawai suka shiga.
Lokacin da labarin kashe Osama ya ɓulla kilomita 300 kacal daga ƙauyen nasu, mutumin bai faɗa wa kowa labarin haɗuwarsu da shi ba sai ƴan ƙalilan. Ya yarda ya yi magana da BBC ne kawai bisa sharaɗin za a ɓoye sunansa da kuma na ƙauyen nasu.

Asalin hoton, Getty Images
A cewarsu, Osama ya shafe kusan awa uku tare da su, inda suka yi addu'o'i kuma suka ci suka sha.
A lokacin, ba a yarda mutanen gidan su fita ba, kuma babu wanda zai shigo saboda akwai masu gadi a saman rufin gidan da duka ginin.
Ɗaya daga cikin mutanen ya nemi a ƙyale mahaifinsa mai shekara 85 ya gana da Osama saboda babban burinsa kenan, masu gadin ba su amince ba. Sai da aka faɗa wa Osama kuma ya amince kafin a bari ya shiga gidan.
Masu gadi huɗu ne suka raka mutumin domin taho da mahaifin nasa, kuma ba a faɗa masa wanda zai gani ba har sai da ya shiga gidan.
Tsohon ya yi kamar minti 10 tare da Osama, lokacin da aka ce ya yi amfani da shi wajen yi wa Osama addu'a da kuma ba shi shawara. Ba lallai ne Osama ya fahimci addu'ar ba saboda harshen Pashto da tsohon ke magana da shi, amma sun ce ya yi ta murmushi da masu gadinsa.
Osama da masu gadinsa sun tafi cikin salon da suka shiga gidan. Suna fita kuma motocin waɗanda irin su ɗaya kowacce ta kama hanyarta daban. Su kansu ba su san wacce ya shiga daga ciki ba, kuma wace hanya ta kama.
Mutanen sun ƙi yarda su faɗi wanda ya nemi a shirya wa Osama tarɓar, sannan sun yi ɗari-ɗarin yin magana kan masu gadinsa ma.
Bayan kashe shi, jami'ai a Pakistan da na Amurka sun ce Osama na zaune ne shi kaɗai a garin Abbottabad shekara biyar kuma bai taɓa fita daga gidan ba a lokacin.
Amma wannan labarin ya nuna cewa iƙirarin nasu ba gaskiya ba ne. Sai dai kuma har yanzu akwai tambayoyin da ke buƙatar amsa.

Asalin hoton, AFP
Wurin da Osaman ya je a wannan daren ƙauyen da sojojin Pakistan suka sha fafatawa da dakarun ƙungiyar Al-Qaeda ne. Amma ta yaya Osama ya suɓuce wa wuraren duba ababen hawa a wannan wuri?
Jami'an Pakistan sun sha musanta cewa suna sane da zaman Osama a yankin, kuma sun ce babu wani taimako da gwamnati ta ba shi.
Wata tambayar ita ce: wane ne babban mutumin da ya shirya masa wannan ziyarar? Mene ne dalili? Kuma sau nawa ya yi irin wannan tafiyar zuwa wuraren da ba a san shi ba?










