Smalling ya kusan komawa Al-Fayha ta Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila da Manchester United, Chris Smalling na daf da komawa buga gasar Saudi Arabia a ƙungiyar Al-Fayha.
Mai shekara 34 zai je Al-Fayha a auna koshin lafiyarsa daga nan ya rattaba hannu kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo ta Pro League a tsakar daren Litinin.
Hakan zai kawo karshen kaka biyar da Smalling ya yi a Roma, wanda ya koma Italiya da taka leda a wasannin aro daga Manchester United a 2019.
Ya buga wa ƙungiyar da ke gasar Serie A karawa 150, amma a bara wasa 12 ya yi sakamakon jinya, wanda bai yi karawa koda ɗaya ba a bana.
Yana cikin ƴan wasan da suka lashe Europa Conference League, bayan cin Feyenoord ya kuma kai wasan karshe da Sevilla ta doke Roma a Europa Conference League a 2023.
Smalling ya lashe Premier League biyu a Old Trafford karkashin Sir Alex Ferguson, ya kuma buga wa Ingila wasa 31 na karshe da ya yi mata shi ne a 2017.







