Abin da muka sani game da taron mahaddata Al-Qur'ani a Abuja

Qur'ani

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Taron mahaddata Al'qur'ani da ake shirin gudanarwa a birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya kankane kafafen watsa labarai da na zumunta, inda wasu ke yabo wasu kuma ke kushe shi.

Alƙaluma daga mutane da ƙungiyoyin addini da dama sun nuna cewa Najeriya ce ƙasa mafi yawan mahaddatan al-qur'ani a duniya, inda ƙasar take da miliyoyin mahaddata - maza da mata, yara da ƙanana.

To sai dai batun taron na mahaddatan da ake shirin yi ya janyo muhawara, inda wasu ke sukar kalmar da aka yi amfani da ita ta "festival" da ke nufin "biki", sannan wasu ke dangantaka al'amarin da siyasa.

Wannan ne ya sa BBC yin bincike domin yi wa masu bibiyarta bayani dangane da abin da ta sani kan taron kamar haka:

Mece ce manufar taron?

Qur'ani

Asalin hoton, Getty Images

Bisa bayanan da aka wallafa a shafin intanet na musamman na wannan taro, za a dai a yi taron ne a ranar Asabar ta 22 ga watan Fabrairun 2025, a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.

Dangane da manufar taron, shafin ya ce an shirya taron ne bisa la'akari da irin jajircewar da mahaddata al-qur'ani suka yi shekara aru-aru.

"Al'ummar Najeriya daga sassa da ƙabila daban-daban na ƙasar sun sadaukar da rayuwarsu wajen haddace Qur'ani a ɗaruruwan shekaru"

Saboda haka wannan taron zai zama wani dandamali na karrama makaranta da marubuta al-qur'ani mai girma. Sannan wata mahaɗa ce da ke nuna yadda al'adu da ƙabilun Najeriya daban-daban ke karanta da mu'amala da Qur'ani da irin karin harshensu sannan bisa al'adunsu." In ji shafin.

Shafin ya kuma lissafa ƙarin wasu muhimman abubuwan da za a yi a lokacin taron kamar haka:

  • Karrama mahaddata Al-Qur'ani: Taron zai fito da irin jajircewa da ƙoƙarin mutanen da suka haddace da kuma waɗanda suke iya rubuta al-qur'ani baki ɗaya.
  • Haɗin Kai: Taron zai tattara al'umma daga sassa da ƙabila daban-daban na Najeriya da ke mu'amila da littafi mai tsarki.
  • Zaburar da Ƴanbaya: Wata manufar ta wannan taro ita ce sanya wa yara sha'awar haddace al-qur'ani tunda ƙuruciyarsu, ta hanyar tallata irin nasarar da mahaddatan suka yi domin ganin al'adar haddace Qur'ani ta ɗore.
  • Fito da basirar Mahaddata: A lokacin taron, za a fito da irin basira da kaifin hadda da kuma jajricewar da mahaddata ke da ita.

Ta yaya mahaddata za su halarci taron?

Makaranta Al-Qur'ani

Asalin hoton, Getty Images

Filin da za a yi wannan taro dai da ke Abuja na cin mutum 61,000, to amma bisa tanadin da aka yi a shafin intanet na taron, mutum 30,000 ne za su yi rijista.

"Mun yi hakan ne domin gudun ka da filin ya yi kaɗan tun akwai waɗanda za mu gayyata daga ciki da wajen ƙasa kamar Kamaru, Chadi da Nijar. Gabaɗaya dai mahalarta taron ba za su wuce mutum 61,000 ba kamar yadda adadin filin wasan yake." In ji wani ɗan kwamitin taron.

Shafin intanet na taron dai ya nuna cewa duk mahaddacin da ke sha'awar zuwa taron to zai yi rijista ne domin bayar da bayanai a kansa da suka haɗa da abubuwa kamar:

  • Suna:
  • Gari:
  • Jiha:
  • Ƙasa:
  • Makaranci ne?
  • Marubuci ne?
  • Wace ƙira'a kake yi?
Batutuwa uku da ke tayar da ƙura

1) Kalmar "Festival"

Taron na ci gaba da samun masu suka daga ɓangarori daban-daban dangane da batutuwa guda uku kamar haka:

Kalmar "Festival": Yin amfani da kalmar "festival" a taron da aka kira da "Qur'aninc Festival" ya janyo kace-nace a tsakanin al'umma, inda wasu da dama suka ce amfani da kalmar da ke nufin biki tamkar raina Al-Qur'ani ne.

To sai dai daga bisani bayan da suka ya yi yawa kwamitin shirya taron ya karɓi ƙorafi inda ya sauya taken taron da "Nigeria Qur'anic Convention" inda aka sauya kalmar "Festival" da ta "Convention".

"Wasu ɓangaren na duniya kamar Pakistan da Indonesia suna amfani da kalmar ta "festival" ko kuma "Maharaja" da harshen Hindu da ke nufin biki. Wannan ne ya sa muka sauya kalmar ta "festival" zuwa "convention" da ke nufin taron da za a gabatar da muƙaloli da locci da karatu." In ji wani ɗan kwamiti.

2) Siyasantar da addini

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai masu sukar taron na mahaddata bisa zargin cewa taron na siyasa ne da wasu ƴan siyasa ke son amfani da taron wajen cimma burinsu na siyasa.

Sai dai kwamitin ya musanta wannan zargi inda ya ce ba shi da tushe.

"Me ya sa za a yi siyasa da makarantan Al-Qur'ani? Waɗanda suka tsara wannan taro sun yi ne da manufar fito da irin yadda Al-Qur'ani ya haɗe kan Musulman Najeriya ba tare da banbanci ƙabila ko ɓangare ba.

A wurin wannan taro za a ji karatun Yarabawa da Igbo da Kanuri da Hausawa da Fulani. Ka ga wannan zai nuna wa abokan zamanmu cewa Musulunci ba na wata ƙabila guda ba ne." In ji ɗankwamitin.

BBC ta fahimci cewa shugaban kamfanin mai na NNPCL ne ya yi tunanin taron inda kuma ya tattauna da malamai kuma suka yi na'am da tunanin nasa.

A baya-bayan nan dai shugaban na NNPCL, Mele Kyari ya bayyana wa duniya cewa ya yi almajirci.

"Ina godiya da ƙasata da ta ba ni damar jagorantar kamfanin makamashin da ya fi kowanne girma a Afirka (NNPCL), a matsayina na wanda ya taso almajiri." In ji Mele Kyari.

3) Jagororin taron

Akwai waɗanda suka rinƙa zarge-zargen cewa ba a san masu jagorantar taron ba inda wasu kuma ke kallon cewa ƴan wata fahimtar addini ne da ta saɓa tasu ke jagorancin taron a saboda haka ya zama abin zargi.

To sai dai binciken BBC da ta yi ya nuna cewa wani kwamiti ne da ke da wakilcin sassa da ɓangarorin Musulmin Najeriya ke tafiyar da al'amuran taron bisa jagorancin Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III.